Yayin da wasu suka yarda su koma gida a cikin bakin hauren, wasu sun ce ba za su koma ba /PHOTO: Anadolu

An mayar da ‘yan Kamaru 75 wadanda matsalar bakin haure ta kasar Tunisiya ta shafa gida daga kasar.

An mayar da mutanen kasarsu ne bayan sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Kamaru ta fitar kan lamarin.

Gidan talabijin na kasar CRTV ne ya tabbatar da cewar 'yan kasar da aka mayar Kamaru sun sauka a filin jiragen sama na Nsimalen da ke Yaounde, babban birnin kasar a safiyar ranar Alhamis.

Wata sanarwar da ma’aikatar hakokin wajen kasar ta fitar ta ce mutum 75 din ne suka yarda a mayar da su gida cikin ‘yan kasar 181 da aka gano cewar rikicin ya rutsa da su a Tunisiya.

Sanarwa ta ce gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin kasar a Tunisiya sun taimaka wa ‘yan kasar da ke cikin mawuyacin hali a kasar saboda muhimmancin da suka bai wa lamarin.

Ta kara da cewar ma’aikatar da ofishin jakadancin suna ganawa da hukumomin Tunisiya domin kare ‘yan Kamaru da ke kasar ta Tunisiya.

Tun lokacin da Shugaban kasar Tunisiya, Kais Saied, ya ce karuwar bakin haure bakaken fata da ke shigowa Tunisiya wata dabara ce ta sauya mutanen kasar ne ‘yan Afrika Kudu da Sahara da ke kasar suka shiga wani mawuyacin hali.

‘Yan jam’iyyun hamayya a kasar da ma Tarayyar Afrika sun yi zargin cewa shugaban Tunisiya ya yi kalaman ne da nufin nuna wariyar launin fata, amma ya musanta hakan.

Kwanan na mutum 34 cikin bakin hauren suka bace a tekun Tunisiya bayan jirgin ruwan da ya dauke su ya kife/ PHOTO: Anadolu