A Ayyukan haka da aka gudanar a Cankiri, arewa ta tsakiyar Turkiyya, an gano wasu kasusuwan giwa da ta rayu shekaru miliyan 9 da suka gabata.
Wajen hakar da aka fi sani da "Filin Binciken Ƙasusuwan Dabbobi Masu Ƙashin Baya" da ke kan babbar hanyar Cankiri-Yaprakli ya kasance wajen da aka mayar da hankali a kai tsawon shekaru 27.
Masu aikin binciken da Farfesa Ayla Sevim Erol daga Tsangayar Harsuna, Tarihi da Taswira ta Jami'ar Ankara ta jagoranta, sun hako kusan kausuwa 4,320 nau'ikan halittun dabbobi 42, ciki har da na dawaki, giwaye, rakumin dawa, manyan magunan dawa, da sauran su.
An kuma samu wani adadi na irin wadannan kasusuwa a wasu wuraren daban.
A farkon watan Yulin wannan shekarar, tawagar hakar sun gano kashin wata giwa da ta rayu shekaru miliyan 9 da suka shude, sannan an samu karin wasu kayayyaki a wajen.
Erol ta yi bayanin cewar Corakyerler waje ne mai dabbobi maus kashin baya da dama, yana dauke da kasusuwan manya da kananan dabbobi.
Ta yi tsokaci da cewa a baya an gano kasusuwan na nau'ikan halittu 43 a wajen.
"A yanzu haka, muna binciken neman kasusuwan kafada da kafar wata giwa. An gano kashin kafadar sama. A wannan shekarar, mun gano kaussuwan giwaye da dama."
Ta ce "Akwai nau'ikan giwaye a Corakyerler: daya shi ne nau'in manyan giwaye da ake kira 'Konobeledon,' da kananan nau'ikan halitta na dangin 'Choerolophoden.' Kashin kafadar da muka gano dangin manyan giwaye ne."
A yayin ake gaf da kammala ayukan hakar, Erol ta yi tsokaci da cewa gwajin farko ya yi nuni da wajen ya kai shekaru miliyan 8. Har yanzu, wabbin nau'ikan halitta da ake gano wa na nuni da sun wanzu shekru miluyan 9 da suka wuce.
A shekara mai zuwa, wani kwararren bincike daga Spaniya zai gudanar da bincike kan sinadaran yuraniyom da kanwa a wajen.