Illustration shows Meta and Threads app logos / Hoto: Reuters

Jim kadan bayan saukar sabuwar manhajar Threads da zafinta, 'yan Nijeriya sun kasance a gaba-gaba wajen yin maraba da wannan dandali.

A ranar Alhamis ne kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram da WhatsApp ya kaddamar da Thread, wata manhaja da ta kasance tamkar kishiya ga Twitter saboda kamanceceniyarsu.

Kafin awa 24 da kaddamarwar sai da fiye da mutum miliyan 30 suka sauke ta a wayoyinsu - amma an dan samu tsaikon sakinta a nahiyar Turai saboda damuwar da aka nuna kan batun tsare bayanai.

Dubban 'yan Nijeriya na daga cikin sahun farko na bin wannan manhaja, inda mutane cikin zakuwa suka yi ta tururuwar shiga suna bude shafuka, musamman da yake kamfanin Meta ya saukaka lamarin ta wajen hade shi da bayanan mutum na Instagram.

A shafin Twitter da ake ganin shi ne kishiyar sabuwar manhajar, Threads ta kasance ita ce ta daya a maudu'an da suka fi tashe. Sannan a Facebook ma duk zancen daya ne.

Cikin 'yan Nijeriya da suka yi tururuwar bude shafin a zubin farko har da shugaban kasar Bola Tinubu da 'yan jarida da fitattun 'yan fim da mawaka da matasa masu fada a ji a soshiyal midiya da 'yan kasuwa da ma kafafen yada labarai.

Abin mamakin shi ne ganin yadda har wadanda ba su faye hawa Twitter ba a da amma yanzu sai ga su a Threads. Hakan na nuna cewa lallai an zaku da samun wannan sabon tsari.

Aisha Falke, wata fitacciya a shafukan sada zumunta a Nijeriya mai shafin Northern Hibiscus a Instagram da Facebook, cikin farin ciki take shaida wa TRT Afrika cewa tana cikin dibar fari na hawa dandalin.

"Daga lokacin da ya fito na ji ana ta hayya-hayya, ko da na zo hawa sai na ga ni ce ta wajen miliyan 20 da doriya, abin ba a cewa komai," in ji Falke.

Malamar Aji, kamar yadda ake yawan kiranta da shi, ta ci gaba da cewa "Ni ina ga kamfanin Meta ya yi nazari ne ya ga akwai mutane da dama da suke Instagram amma ba sa Twitter, saboda yadda ake ganin kamar Twitter na tsorata mutane, ana ganin waje ne na masu kokari kar ka je ka yi kuskure daya ka sha zagi.

"Ina gani da wannan suka yi la'akari suka bude Threads saboda sun san matasa masu IG za su koma can.

"Ni kaina ba na son Twitter saboda daga ka yi abu sai mutane su dirar maka, wannan kuwa da na shiga sai na ji kamar gida ne amma ka yi masa kwaskwarima."

Ga dai sakonnin farko da wasu suka fara wallafawa a shafin na Thread.

Fitaccen dan jaridar nan Jaafar Jaafar ya wallafa:

Jaafar Jaafar ya ce marabanku da zuwa shafin Threads. Ku zo mu baje kolin a nan. Hoto: Screengrab
Gen Sunusi
Sakon Hauwa Farouk Ibrahim

Mutane da dama sun yi ta yada adireshin sabon shafin nasu don samun mabiya. Hakan na nuna cewa ba sa so a bar su a baya wajen zama na farko-farko a cin gajiyar wannan sabuwar manhaja.

Kuma kamar yadda aka sani a halayyar 'yan Nijeriya ta son yawan raha kan duk wani maudu'i da ke tashe, haka suka shafe yini suna kirkiro labaran ban dariya suna danganta su da dandalin na Threads.

Aisha Falke ta ce a yanzu za su zuba ido nan da 'yan watanni don ganin yadda abin zai kasance da irin tasirin da zai yi.

"Amma ni babban abin da ya ba ni mamaki shi ne da hawana ba wahala sai na ga har na samu mabiya 3,000. Sannan ina ga a kan Threads za a dan ajiye wannan jin kan na cewa ba kowa za a bi ba sai fitattun mutane irin yadda ake yi a IG da Twitter.

"Bari dai mu gani, watakila ya zama mai sauki kawance kamar Tiktok. Allah Ya ba mu tsawon rai don ganin yadda za a wanye," in ji malamar.

Ga dai wasu bayanai a takaice a kan Threads:

  • Threads manhaja ce mallakin Meta mai manhajojin Facebook da Instagram da ma WhatsApp.
  • Shafin ya yi kama da Twitter sosai - inda mutum zai iya wallafa sako da tsawonsa bai wuce harufa 500 ba.
  • Kamar dai Twitter, shi ma Threads yana iya daukar hotuna ko gifs ko kuma bidiyon da bai wuce minti biyar ba.
  • Haka kuma kuna iya sake yada abin da wani ya wallafa repost, ko kuma ku ‘so’ shi wato ‘like’.
  • Wani abu kuma shi ne kuna iya shiga shafin Threads, wato ku yi log in ta hanyar amfani da shafinku na Instagram, sannan za ku iya yin amfani da Threads don bibiya wato following dukkan shafukan da kuke bi a Instagram.
  • Sannan kuna iya sirrinta account dinku na Threads, ku mayar da shi private kenan.
  • Kamfanin Meta ya ce ya zuwa wannan lokaci babu settings na aminai ko ‘close friends’, amma idan b aka son hulda da jama’a da yawa sai kawai ka mayar da shi private.
  • Kawo yanzu dai, ba a iya yin DM a manhajar Threads.

TRT Afrika