Bayanin almubazzaranci ya fito fili a wannan watan ne bayan wani bincike na cikin gida da aka gudanar. Hoto / Reuters

Daga Firmain Eric Mbadinga

Masu damfara sun sayar da wutar lantarki ta miliyoyin daloli ga mutane a kasar Gabon, bayan da suka kafa tsarin biyan kudin wutar lantarkin na sayarwa a kamfanin samar da wutar lantarki na gwamnati, kamar yadda bincike da hukumomi suka gudanar ya nuna.

Har yanzu ana kan tantance girman asarar da kamfanin Société d'énergie et d'eau du Gabon (SEEG) ya yi, amma wadanda ake zargin sun yi nasarar samar da tikitin wutar lantarki ba tare da bai wa kamfanin ko kwabo ba.

Bayanin almubazzaranci ya fito fili a wannan watan ne bayan wani bincike na cikin gida da aka gudanar, kamar yadda jami'an kamfanin sun ce.

Bincike ya nuna cewa a cikin gida aka kitsa wannan shirin, wanda ya kai ga kama wasu ma'aikatan kamfanin da tun daga lokacin hukumar Direction Générale des Recherches (DGR) ta tuhume su.

Matsalolin kuɗaɗe

Babban Manajan SEEG, Joël Lehman Sandoungout, ya tabbatar da satar kudaden, wanda ya ce ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar matsalar kudi.

"Ana ci gaba da bincike. Muna da wakilai (ma'aikata) da ake yi wa tambayoyi a DGR," in ji Sandoungout a hirarsa da TRT Afrika.

Lauyan da ke wakiltar kamfanin ya ce asarar kudin da aka yi "gagaruma ce".

"Wadanda suka ci gajiyar wannan zamba, wadanda ke ɓuya a bayan wasu, sun fara fitowa fili, wanda hakan ya sa aikin ya kara daukar hankali," Anges Kevin Nzighou, mai ba da shawara kan harkokin shari'a na SEEG, ya shaida wa TRT Afrika.

Tsawon lokacin da aka ɗauka ana almundahanar

Har yanzu dai ba a san tsawon lokacin da aka ɗauka ana wannan aika-aika ba, amma akwai zargin cewa yana iya kasancewa tsawon shekaru. Da yawa a kasar suna kamanta hakan da wata shahararriyar karin magana ta Gabon da ke cewa: "Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya.

Masu amfani da wutar lantarki a kasar dole ne su sayi katin wuta daga kamfanonin da ke samar da ita don samun lambobin da za su loda a mitotinsu da kuma tabbatar da haɗa musu wutar lantarkin.

Wutar lantarki da za a ba wa mutane ya danganta da yawan abin da suka saya a katin.

Wadanda ake zargin sun yi nasarar sayar da katin wutar lantarki ba tare da miƙa kudaden zuwa ga SEEG ba, kamar yadda bincike ya nuna.

Zamba

Binciken cikin gida ya haifar da zargin damfarar ta intanet wanda ya kai ga ci gaba da bincike daga kamfanin.

Wadanda ake zargi da aikata laifin su ne shugabannin sashen biyu da manajan IT.

Hukumomin ƙasar sun gudanar da bincike a harabar babban ofishin kamfanin wato Sigma Technologie, inda a can ne aka ce an kafa tsarin fasahar kamfanin.

Sigma Technologie bai wa mutane bayani kan binciken da ake yi ba.

"A ranar 09 ga Agustan 2024, SEEG ta shigar da kararraki biyu na sata da almubazzaranci. Binciken da ake ci gaba da yi na bayyana sabbin abubuwa a kowace rana, tare da fallasa girman wannan gagarumar zamba," in ji mai samar da wutar lantarki.

Inganta tsaro

SEEG ta riga ta sanar da cewa za ta inganta tsarin tsaro na IT don ƙarfafa sa ido da gano duk wani yunƙuri na sarrafa tsarinta da bayananta.

Har ila yau, za a gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan tsarin sarrafa tikitin sayar da wutar lantarkin na kamfanin, in ji ta. A halin yanzu, tare da matakin shari'a, kamfanin ya fara nazarin kwangila tare da abokan hulɗa na waje don ƙarfafa tsaro na aiki.

TRT Afrika