Hukumar Hisbah a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta yi wa ƴan Tiktok alkawari da busharar cewa za a yi musu auren gata da ba su sana’o’i da tura su ƙaro karatu, idan har suka sauya halayensu da kuma daina yaɗa abubuwan da ba su dace ba a shafukansu.
Kwamandan rundunar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da mataimakansa biyu ne suka sanar da hakan a wata ganawa ta musamman da suka yi da ƴan Tiktok ɗin a oifshin hukumar da ke birnin Kano a ranar Litinin da marece.
An yi wannan taro ne kwanaki kadan bayan wani gagarumin samame da Hisbah ta dinga yi a wasu wuraren taruwar jama’a a birnin Kano, inda ta kama matasa maza da mata da dama, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.
An ga fitattun ƴan Tiktok irin su Murja Ibrahim Kunya a wurin.
“Daga cikin ayyukan Hisbah har da gyaran tarbiyya don mu dinga bai wa matasa shawarar yadda za su tafiyar da rayuwarsu cikin kamala ba tare da lalata samartakar su ba ta yadda za su yi nadama a nan gaba,” a cewar Sheikh Daurawa.
Ya ƙara da cewa ganin yadda mutane suke amfani da shafin Tiktok barkatai ya sa hukumar ta ga bai kamata ta bar abubuwa na taɓarɓarewa ba.
“Mun gayyace ku a matsayinku na matasa don bai wa Hisbah gudunmawa kan yadda za a daƙile irin ayyuka marasa kyau da ɓata tarbiyya ba.
“Mun lura wasu kan yi kasuwanci ko fadakarwa ko koyar da karatun Kur’ani ko na zamani ko koyar da zaman aure da ma sana’o’i. Wasu kuma abin da suke yi bai dace ba. Akwai takaici a ce kun ɓata rayuwar ƙuruciyarku a kan hakan,” Malam ya shaida wa 'yan Tiktok ɗin.
Sheikh Daurawa ya ba da misali da yadda duk abin da aka dora a intanet ba ya taɓa gogewa inda nan da wasu shekaru za su iya zame wa mutum aikin nadama.
Ya nanata muhimmancin ƴan Tiktok din da irin gudunmawar da haɗin kai tsakaninsu da Hisbah za ta kawo gyaran tarbiyya.
“Ba za mu iya gyaran nan ba sai da hannunku, idan kuka yi fada ku yi ta zage-zage a junanku marasa dadin ji, abin ba ya mana dadi.
“Tiktok ta zama alheri ya wani waje, ta wani wajen kuma ya zama sharri. Ko Amurka da China mun san yadda a yanzu al’amarin Tiktok ya sha musu kai,” in ji Malam.
Malam ya jaddada buƙatar Hisbah ta neman gudunmawar ƴan Tiktok don tsarkake al’umma a aikin da take yi mai take “Operation Kawar da Badala.”
Shirin da gwamnati da Hisbah ke yi wa ‘yan Tiktok
Mataimakin kwamandan Hisbah Dr Mujahid Aminuddin Abubakar wanda a ƙarƙashinsa shirin Operation Kawar da Badala yake, shi ne ya yi wa ƴan Tiktok albashirin shirye-shirye uku da aka tanadar musu.
“Za mu yi mene ne matsalolinku da yadda za a magance muku su, daga masu son karatu da aure da sana’a da wadanda za a inganta musu sana’o’inku,” ya faɗa.
Ya kuma musu albishir cewa duk wadanda suka halarci zaman ba za su tafi hannu rabbana ba, kowa za a masa wani ihsani.
Abu hudu da za a musu sun haɗa da:
Na farko: Za a bincika a ji masu son ci gaba da karatu a cikinsu, kuma idan har sun cika sharuɗɗan gwamnati to har wasu ƙasashen ma za a iya kai su yin karatu.
Na biyu: Za a saka su rubuta tsarin kasuwanci ko sana’a har shafi uku, idan an gamsu da tsarin da suka gabatar din za a ba su kuɗaɗen da za su yi kasuwancin.
Na uku: Masu aure daga cikinsu kuma za a ba su duk ƙarfin gwiwar da suke buƙata do inganta zamansu.
Na hudu: Masu son aure a cikinsu za a shirya musu nasu auren gata na ‘yan Tiktok idan har sun zabi mazaje da matayensu. A daidai lokacin da aka sanar da hakan ne sai wajen taron ya ruɗe da shewa da kabarbari, alamun lamarin ya yi musu daɗi.
Sai dai bayan kammala lissafa wadannan albishir, sai Dr Khadijah Sagir Sulaiman mataimakiyar Kwamdandan Hisbah ɓangaren mata ta yi togaciya cewa ba za a aiwatar da waɗannan alkawaru ba sai in har an ga sauyin halayya a irin mu’amalar da suke yi a Tiktok ɗin.
“Za mu ba da tazara don mu ga yadda halayyarku ta sauya kafin ku amfana da abin da ake so a ba ku.
“Za mu gane kun sauya ne tun daga sauyawar yanayin suturarku da irin ayyuka na gari da za ku dinga saka wa a shafukanku,” ta ce.
Martanin ƴan Tiktok
Ƴan Tiktok ɗin sun bayyana jin dadinsu da kuma amincewar hadin gwiwa da hukumar Hisbah don kawo gyara, inda har suka ba da shawarar kafa ƙungiyar haɗaka mai rajista.
Sannan sun yi maraba da shirye-shiryen da aka tanadar musu musamman ma na yi musu auren gata da na samar musu da sana'oi da kuma ci gaba da karatu.
A ƙarshe an ba su naira 2,000 kowannensu don yi kudin motar komawa gida.
Ina labarin Murja Kunya da Idris Mai wushirya?
Abin da kowa ya zura ido ya gani a wajen taron shi ne halartar Murja Ibrahim Kunya da Idris Mai wushirya, wasu fitattun ƴan Tiktok biyu da suka shahara a Jihar Kanon.
Sai dai dama tun bayan sanarwar kiran taron a ka ga Mai Wushirya a wani bidiyo yana cewa shi ba zai halarta ba ko da yana Nijeriya a lokacin.
Idris wanda ya ce yana Saudiyya don gudanar da Umara, ya ce "ni dai da ƙafata ba zan je Hisbah aba haka kawai a kama ni"
Dama kuma a wajen taron Sheikh Daurawa ya yi togaciya a kan wadanda suka ƙi zuwa don tsoron kar a kama su, inda ya ce ba don a kama su aka kira taron ba.
Ita kuwa Murja ba ta samu zuwa ba sai bayan an kammala da sauran ƴan Tiktok ɗin.
An ganta a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta cikin shiga ta kamala har da niƙabi, tana tsugune a gaban shugabannin rundunar suna mata nasiha.
Sheikh Daurawa ya ce "mun ba wa Murja shawarwari da nasihohi da aniyar gwamna na taimakon rayuwarta da nuna mata kura-kuranta da kuma kira gare ta da ta sauya halayyarta."
Sai dai a bidiyon mai tsawon sakan 56 ba a ji Murja ta ce komai ba.