Daga Abdulwasiu Hassan
Wani abu game da filayen tashi da saukar jiragen sama da ke kai komo a zukata shi ne ganin cunkoso da kai komon mutane a koyaushe.
Manyan gine-gine, kai komon ma'aimakatan jiragen sama, ganin sabbin fuskoki na shiga da fita da tattaka malale mai kyalli, da karar tashi da saukar jirage da ake jiyo wa daga nesa duk na daga abubuwan da suke na musamman ne ga sufurin jiragen sama.
A Nijeriya, filayen tashi da saukar jiragen sama na lalacewa a jihohi, wanda manufar da gwamnatocin da suka samar da su ke son cimmawa ita ce bunkasar tattalin arziki da zamantakewa, inda a wasu bangarorin kuma ake yi wa irin wadannan ayyuka kallon matsayin wadanda ba su da amfani ko ba za a iya kula da su ba.
Jiha ta baya-bayan nan da ta yi niyyar samar da filin tashi da saukar jiragen sama a arewa maso-yammacin Nijeriya ita ce Zamfara.
"Filin tashi da saukar jiragen sama na Gusau na da muhimmanci sosai ga tattalin arziki da amfanar da jama'a.
"Da zarar an kammala aikin, za ta saukaka gudanar da kasuwanci da al'amuran sufuri a jihar," in ji gwamna Dauda Lawal na Jiar Zamfara a yayin kaddamar da aikin.
"Filin tashi da saukar jiragen saman zai bayar da dama ta kai tsaye ta zuwa jiharmu, sannan za su kawar da wahalhalu da 'yan kasuwarmu ke fuskanta wajen fitarwa da shigo da kayayyaki."
Ana sa ran kammala gina filin tashi da saukar jiragen saman a cikin watanni 30.
Filayen tashi da saukar jiragen sama da ba a iya kula da su
Jihohi da dama, ciki har da Ekiti, Akwa-Ibom da Ebonyi da ke kudancin kasar da Yobe da ke arewa maso-gabas, sun gina filayen tashi da saukar jiragen sama a 'yan shekarun nan.
A yayin da jihohi suke gina filayen tashi da saukar jiragen sama, sai kuma su mika wa Hukumar Kula da Filayen Tashi da Saukar Jiragen Sama ta Tarayya filayen, su dora musu nauyin kula da su.
Wannan ya sanya masu suka ke samun sararin sukar ayyukan da cewa ba ma su dore wa ba ne.
Suna nuni da cewar wasu jihohin da suke da filayen tashi da saukar jiragen sama sun kira kamfanoni don su zo daga wurare masu nisa, inda suke yin alkawarin biyan duk kujerar da ba a hau ba.
Wannan na nufin aikin asara, saboda filayen da aka gina da kudaden jama'a don su samar da kudin shiga, sai ya zama su ake kashe wa karin kudade.
A yanzu haka, FAAN na kula da filayen tashi da suakar jiragen sama 22, ciki har da wadanda gwamnatocin yankuna suka samar. Olubunmi Kuku, manajan daraktan hukumar, a baya-bayan nan ya sanar da cewa, ana bayar da tallafi ga tashi da suakar jiragen sama a filaye 19 saboda babu fasinjoji.
Bukatar daidaito
Zamfara na daga cikin jihohin arewa maso-yammacin Nijeriya d ake fama da hare-haren 'yan bindiga, garkuwa d amutane da neman fansa a kan tituna.
Mahukunta na ganin cewar tuntuni ya kamata a ce an samar da hanyar sama don zuwa jihar, a matsayin wani zabi ga matafiya da ke son kauce wa wadannan hadurra na kan hanyar mota.
Ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya, Festus Keyamo, na kallon filin tashi da suakar jiragen saman na Zamfara a matsayin aikin da ba wai farar daya aka kirkire shi ba.
"Ina son na dawo nan a shekara mai zuwa don kaddamar da fara jigilar mutane a filin. Alhazan jihar Zamfara na shan sawala tsawon shekaru, kamar na sauran jihohi, saboda ba su da hanyoyin sufuri na sama.
"Suna bukatar su dinga hawa jirgi kai tsaye zuwa kasa mai tsarki daga Zamfara." in ji Keyamo a wajen wani taro da aka yi a jihar a kwanan nan.
Mai nazari Alhaji Muhammad Tukur na cewar gina manyan gine-gine na harkokin sufurin jiragen sama ba ya nufin za akashe kudade 'yan kadan.
Tukur ya ce jihohi makota irin su Bauch da Gombe a arewa maso-gabashin Nijeriya, wadda kowace tana da filin tashi da suakar jiragen sama, da za su iya hada hannu su samar da guda daya na hadin gwiwa a wani waje da yake kusa da kowa, don yin tsimin kudade.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Wannan tsari ba kashe kudade kadai zai taimaka wa ba, har ma da gine-gine da rage kudaden da ake kashe wa wajen gudanarwa."
To ta yaya Nijeriya za ta yi amfani da filayen tashi da suakar jiragen sama na sufurin cikin gida a gwamnatoci suka samar tun 1999?
Ra'ayin da kwararru suka yarda da shi shi ne a hade su su zama na kasa d akasa, sannan a baiwa kamfanoni masu zaman kansu su dinga kula da su, ta yadda za a dinga samun riba.
Tukur ya ce "Filayen tashi da suakar jiragen sama na jihohi da ke samun fasinjoji na iya hade wa da wasu na tarayya, dukkan biyun za su dinga aiki don samar da riba a karkashin kamfani mai zaman kansa."
"A filin tashi da saukar jiragen saman Legas, za ka iya samar da layin dogo da zai hade bangaren sufurin cikin giuda da na kasashen waje, kamar yadda yake a wasu kasashen duniya.
"Wannan ne abinda ya kamata gwamnati ta yi ta hanyar kwangilolin gina-kula da shi-ka dawo wa da gwamnati."
Maslahar da Turkur ya kawo na kan falsafar "gwamnati ba ta da ruwa da tsaki a cikin kasuwanci".
Mafi yawan manazarta sun amince kan cewar ya kamata a yi duba na tsanaki ta yadda za a kawar da yanayin da za a ce jihohi sun samar da filayen tashi da saukar jiragen sama amma kuma sun ksa kula da su, suna mika wa gwamnatin tarayya su.