Daga Pauline Odhiambo
Abu ne mai wahala kasancewa matashi - mai fama da nakasa a wani ɓangaren jiki, da abubuwa masu sosa zuciya, da dangantaka da kuma duk matsin lambar da ke tattare da rayuwar sauyawa daga ƙuruciya mai daɗi.
Ƴar Afrika ta Kudu Lunathi Nokele tana ɗauke da ƙarin matsala da za ta rayu da ita tsawon shekarun ƴan'matantakarta, wacce ta jefa ta cikin yanayin bi-ta-ƙulli da kuma jin mutum bai da wata kima.
Luthani, ƴar shekaru 26 da haihuwa,ta yi fama da fimfus na tsawon shekaru, abin da yake haifar da manyan jajayen ƙuraje masu zafi, da ke fitowa daga ƙasan fata.
Saɓanin fimfus da aka saba gani, su waɗannan manyan ƙurajen za su iya haifar da tabo kuma suna da wuyar sha'ani wajen warkewa.
Wannan mummunan nau'in ƙurajen na samuwa ne lokacin da mai, da ƙwayar cutar bakteriya da matacciyar ƙwayar halittar fata suka maƙale a ƴar ƙofar, abin da galibi yake haifar da kumburi sosai.
"Fatata ta lalace; bana iya kallon kaina a madubi,"Lunathi ta faɗa wa TRT Afrika. "Mutanen da ban sani ba suna tsayar da ni a titi su tambayi mane ne ya faru da ni.
Wasu na damuwa da yadda nake kuma suna son su taimake ni." Lunathi tana gwada magunguna daban daban da aka ba ta shawara ta jarraba amma babu ɗaya daga cikinsu da ya yi aiki.
Abu mafi muni shi ne ko da kyakkyawar shawara daga makusantanta tana sakawa ta ji babu daɗi. Yawan saka mata ido da aka yi yana tunatar da Lunathi cewa ta sha bamban da sauran yara matan.
"Na yi ƙoƙarin ɓatar da su da kwalliya, amma na fahimci cewa sai dai kawai ta sauya wa wajen baƙi baƙin launi. Kwalliya ba ta iya ɓatar da ƙurajen fimfus.
"Na ma yi amfani da man ƙarawa fata haske (bilicin) domin na kawar da baƙi baƙin. Na yi amfani da magungunan gargajiya ta yin amfani da lemon da zuma da tsamiya, babu ɗaya da ya yi aiki.
Karyayyen karsashi
A wajen masu fama da Ƙurajen fuska, musamman lokacin tashen balaga, babban kalubale ga mai fama da matsalar shi ne rashin yin kataɓus.
"Ina jin karsashina ya yi ragu sosai, lokacin da ƙurajen suka addabe ni, yayin da nake jami'a, zamanin da akwai ƙawazucin sai mutum ya yi ado don ya fito tsaftsaf. Ban iya yin hakan ba," matashiyar ta tunano.
"Ba na iya fita da ƙawayena. Ina zama ne kawai a ɗakina saboda ba ni da wani shauƙin fuskantar duniya. A wannan lokacin ne na yanke shawarar na ga likitan fata."
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), cutar Ƙurajen fuska tana daga cikin cututtuka na gaba gaba guda biyar da suke da kaso 80% wajen haddasa cututtukan fata.
Tana iya bayyana a kowanne ɓangaren jiki, da suka haɗa da fuska, da kafaɗa da gadon baya da hannaye, kuma suna iya kasancewa masu wuyan sha'ani.
Ƙurajen fimfus suna buƙatar yin magani akai akai kuma zai iya kasancewa da tsada, gwargwadon munin cutar.
Na ziyarci likitocin fata guda biyu, na farko a shekarar 2018 a asibitin gwamnati. Ta rubuta min magani sannan ta ce na dinga shafa wa fatata mai akai akai.
Har wa yau, ta shawarce ni da na wanke fuskata ta hanyar amfani da sabulu mara ƙarfi.
Likitan fata na biyu da ta ziyarta mai zaman kansa ne, wanda ke karɓar kimanin rand 800 ($45) a matsayin kuɗin duba mutum da kuma wasu rand 900 ($45) na magani, na tsawon kusan ƴan makwanni kawai.
Amma masana lafiyar fata sun ce, ba dole sai kuɗin jinyar da ya yi tsada ne zai yi aiki ba.
"Farashin magunguna sun bambanta, kuma masu araha suma suna karɓar wasu mutanen kamar masu tsadar," a cewar Dr Lerato Mesemola, wata ƙwararriya kan gyaran jiki wanda ta ce a yi amfani da retinoids wajen maganin ƙurajen fimfus.
Retinoids, nau'in magunguna masu ƙara lafiya ɗauke da sinadarin Bitamin A, ana samun su a shagunan magani, amma masu ƙarfi sosai suna da nasu illolin kuma kar a yi amfani da su sai da izinin likita.
"Illolin sun haɗa da rashin ƙwarin fata da bushewarta har ma da batun lafiyar ƙwaƙwalwa kamar tsanani damuwa, abin da ya sa a galibin lokaci ba da retinoids ake fara tunkarar shi ba," a cewar Dr Masemola.
Daidaita sinadarin hormones
Ƙwararriya kan magungunan gyaran jikin ta ce a yi amfani da kwayoyin maganin antibiotics tare da ɗaukar muhimman matakan kula da tsaftar fata gwargwadon irin cutar da aka gani.
"Ginshiƙin kula da fata shi ne wankewa kullum da zai taimaka ƙurgin ya dena daskarewa.
Sayan sabulun wanka da ba ya bari fata ta bushe yana da muhimmanci," ta bayyana.
Ban da wankewa akai akai, wasu ƙwararru sun bayar da shawarar yin amfani da magunguna masu nasaba da sinadarin hormones kamar masu bayar da kariya, waɗanda a galibin lokaci suke da tasiri wajen warkar da fimfus, da ƙurajen fuska.
Amma fa, wasu mutanen ba su natsu da daidaita ƙwayoyin hormones tare da magungunan bayar da kariyaba saboda tsoron zai iya haifar da wasu illoli kamar zaƙuwa da ƙiba.
Muhimmanci abinci mai gina jiki
A wajen Lunathi da wasu masu fama da cutar ƙurajen fimfus kwatankwacinta, cin abinci mai gina jiki da kuma kauce wa wasu nau'ikan abinci na taimaka wa fata ta yi wasai.
"Na san dangin madara na haddasa cutar kan mutane da dama, saboda haka ina ƙoƙarin kauce wa amfani da su tare da wasu nau'ikan abinci masu maiƙo da kuma lemon kwalba, ta sheda wa TRT Afrika.
A shekaru biyu da suka wuce, Lunathi ta lura fatarta na washewa. Baƙi baƙin ya washe shi ma. Yanzu kwalliya na zama sosai a fatata saboda yanzu ba ni da waɗannan manyan ƙurajen a fuskata.," ta faɗa, cikin annashuwa.
Dr Masemola ta bayar da shawara ga duk wani mai fama da cutar ƙurajen fimfus ko wani abu makamancin hakan da ya nemi magani ba tare da ɓata lokaci ba.
"Yana da muhimmanci ka nemi magani don warkar da ƙurajen fimfus, musamman idan magungunan gargajiya ba su karɓi mutum ba.
"Akwai kasadar yi wa fatar ƙarin lahani idan ka ɗauki tsawon lokaci ba ka nemi magani ba."