Daga Sylvia Chebet
Tattaunawa kan sauyin yanayi na faduwa kasa warwas a ko yaushe, inda wasu daga cikin kasashen da suka fi gurbata muhalli suke ta kokarin kawo gyara, a lokacin da sauran kasashen duniya ke nuna bacin rai kan gaz abiyan kudaden da ba sa isa a yi maganin rikicin da ke addabar duniya.
A yayin da taron COP29 da aka gudanar a tsakanin 11 da 22 ga Nuwamba a Baku, Azerbaijan ya tattauna kan matsalolin da ake fuskanta, hankali ya koma ga taron G20 a birnin Rio de Janero na kasar Brazil don ganin an samu wasu alamomi masu kyau dn samun karfin gwiwar yaki da matsalar da ake yi.
Ga Afirka, nahiyar na bukatar dala tiriliyan 1.3 cikin gaggawa don daukar nauyin ayyukan yaki da matsalar sauyin yanayi da ke ci gaba da ta'azzara.
"Yana da muhimmanci cewa G20 su yarda da matsalar bai daya ta sauyin yanayi da kuma cigaba mai dore wa saboda hakan na illata rayuwa da rayukan jama'a.
Tare da ta'azzarar rikicin, lokaci na kure wa," in ji Samson Mbewe, jagoran bincike na wata kungiya da ke Afirka ta Kudu a lokacin da yake tattauna wa da TRT Afirka.
Samar da isassun kudade don yaki da sauyin yanayi, daya ne daga fifikon da Afirka ke da shi a fagen kasa da kasa.
Daga neman sauyi ta fuskar cin bashi da yaki da bambancin samun arziki zuwa ga yaki da tasirin mulkin mallaka da sace dukiyoyinta, nahiyar na yaki da matsaloli da dama a lokaci guda.
Bayan shekaru bakwai na roko da lallami, a karshe Afirka ta samu wakilci a G20, kungiyar da kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki - da suke juya kashi 85 na tattalin arzikin duniya - suke yanke hukunci da smaar da manufofi ga duniya.
Afirka ta Kudu, da ke wakiltar Tarayyar Afirka, ita ma ta samu darajar karbar bakunci da shugabantar taron G20 da za a nan gaba.
A yayin da taron Rio ya baiwa Afirka dama, abubuwan da aka amfana a taron na da damarmaki ga nahiyar.
Hada kai don yaki da yunwa
A yayin fara tattaunawar taron G20, kasashen duniya 82 sun bayyana kudirin na hada kai da duniya don yaki da yunwa da talauci, inda suke isar da nasarar wuri-wuri ga mai karbar bakuncin taron Shugaba Luiz Inacio Da Silva na Brazil.
Kawancen na da manufar hade kokarin kasa da kasa waje guda na samar da kudade don ayyukan yaki da yunwa da maimaita shirye-shiryen d asuka yi nasara a wasu kasashe.
Manufar ita ce a isa ga mutane miliyan dari biyar nan da karshen shekaru gman da aka ware, rage abinda Lula da ya girma cikin talauci yake kira da magance "matsalar da ke kunyata dan adam".
Amma masu nazari na tunatar da cewa Yarjejeniyar Rio de Janero ba ta doshi warware matsalar bashi ba.
Masanan tattalin arziki na nuni da cewa kasashen Afirka ashirin da uku na kashe kudaden bashi da yawa a bangaren kula da lafiya ko ilimi. Suna fatan samun karin cigaba karkashin Shugabancin Afirka ta Kudu.
Jason Rosario Braganza, daraktan Kungiyar Afirka da Kula da Bashi da Cigaba ta Afirka, na kallon ikirarin Tarayyar Afirka ga taron G20 da "babban mataki na kara matsin lamba don tabbatar da samun makoma don sauya fasalin basussuka".
Ya yi muhawara da cewa Tsarin Bai Daya na G20, tsarin bashi da wanda ya bayar da kudaden ke kafa sharuddansa na bayar da fifiko wajen biyan sa kudaden.
"Ministocin kudi na kasashen Tarayyar Afirka sun sha nanata cewa wannan tsari na bai daya ba zai yi aiki ba ga Afirka saboda tasirin ukuba," in ji Braganza, yana mai jaddada bukatar maye gurbin wannan tsari.
"Domin kalubalantar wannan matsala, zama mamban Tarayyar Afirka a G20 na da muhimmanci, za a kare matsayin nahiyar kan wannan matsala."
Karbar haraji daga masu kudi
Taron G20 ya amince da shwarar hada kai don tabbatar da an karbi manyan kudaden haraji daga masu hannu da shini.
Wannan hadin kai zai zama "da cikakken girmama wa ga karbar haraji" da kuma kalubalantar kaucewa biya.
Masanin tattalin arziki Gabriel Zucman, wanda ya kware a wannan bangare kuma shugabancin G20 na Brazil ya nemi da ya rubuta rahoto kan batun. Ya yabi shirin da kiran sa da "mataki na tarihi".
"Muna maraba da Sanarwar Karshe ta Taron Shugabannin G20, musamman yarda da cewa akwai rashin adalci a tsakanin kasashe wanda na daga manyan matsalolin duniya - daga rashin kudade zuwa rikici, sauyin yanayi, yunwa, talauci da rashin lafiya," in ji Aggrey Aluso, darakta, Yankin Afirka, a kungiyar PAN.
Ya ce "Amma a yayin da shugabannin G20 suka hada kai kan dukkan irin matsalolin da muke fuskanta, mataki da zuba jari da ake dauka da yi don magance matsalar ba sa kan daidai. Mun kauce hanya sosai wadda za ta kai mu ga cimma Manufofin Cigaba Mai Dorewa."
Kwararru sun yi amanna cewa mayar da hankalin 'yan siyasa ga bayar da kudade dole ne don daga martabar kasashen, musamman a Kudancin Duniya, don kawar da kalubalen - da ya hada da barazanar annoba, sauyin yanayi, da yake-yake.
Kamar yadda Aluso a bayyana, "Dole ne mu bar magana da baki mu koma ga aiki da cika wa".
Babu wani cigaba a yaki da sauyin yanayi
Akwai fata sosai cewa taron ne shugabannin G20 a Rio zai sake zaburar da tattaunawar MDD game da sauyin yanayi.
A sanarwar bayan taro ta karshe da suka fitar, ta bayyana "kawai suna bukatar samo kudaden yaki da matsalar daga bangarori daban-daban."
Amma kuma, har yanzu ba su bayyana waye zai bayar da kudaden na tiriliyoyin dala ba.
"Ba su kai ga magance kalubalen ba," in ji Mick Sheldrick, daya daga cikin wadanda suka samar da kungiyar Global Citizen.
Mbewe na kungiyar 'SouthSouthNorth' na da ra'ayin cewa "Dole ne shugabannin G20 su matsa daga maganganu d abaki kawai zuwa aiki a aikace da zai kawo mafita" don cim ma manufofin Yarjejeniyar Paris.
Magalie Masamba, babbar jami'a a Kungiyar Rundunar Adalci ga Bashi ta Afirka, ta lura da cewa kasashen Afirka na fama da bukatun cigaba da tasirin sauyin yanayi a lokaci guda.
Ta ce "Kasashenmu na bukatar isassun kudade don samar da kayan more rayuwa masu kyau, saba wa da sauyin yanayi, rage dimbin bashi, da barin wasu hanyoyi ba tare da jefa kawunansu cikin matsalar tattalin arziki ba."
Za a yabi taron Baku da bayyana shi a matsayin mai nasara idan har ya kawo kudaden da ake bukata na sauyin yanayi na sama da dala tiriliyan daya, wadanda za a raba ta hannun hukumomi da kungiyoyi.
Duba ga nazarin kimiyya, kasashe masu taso wa a yanzu na bukatar a kalla dala biliyan 400 don saba wa da halin da ake ciki, asara da magance matsaloli, da kuma wata dala tiriliyan 1.9 don zuba jari a fannin makamashi.
"Wannan ba ga yankinmu kawai yake da muhimmanci ba, har ma ga habakar duniya," in ji Masamba.
Haka kuma shugabannin G20 a Rio ba su jaddada abubuwan da aka yi a wajen COP28 ba a Dubai a shekarar da ta gabata na "fitar da iskar carbon bisa adalci, a nutse da daidaito, da kuma barin fitar da ita".
"A matsayin kasashen da ke da iko da kashi 85 na tattalin arzikin duniya kuma suke da alhakin itar da gurbatacciyar iska da kashi uku cikin hudu, G20 na da muhimmanci wajen matakin da duniya za ta dauka don yakar sauyin yanayi." in ji Mbewe.
A yayin da kasashen duniya 20 suke gurbata muhalli a duniya da kashi 77, kuma suke rike da kashi 85 na tattalin arzikin duniya, suna taka rawa a yunkurin da duniya ke yi na Cim ma Manufofin Yarjejeniyar Paris da ke da manufar rage dumin duniya da digiri 1.5 a ma'aunin celcius tare da bayar da kudade.
Kwararru sun kuma tunatar da cewa Taron Rio na samar da damarmaki a kan lokaci ga G20 kan su dauki alhakin bai daya da fadada burin samar da kudade, rage yawan fitar da gurbatacciyar iska, da kokarin sabo a COP29.
Duk da G20 na da matukar muhimmanci, masu nazari na tunatar da cewa kungiyar na da "iyaka", kkuma watakila lokaci ya yi da za a kalli tsarin aiwatar da dukkan matakan da aka dauka daga kowacce kasa.