Daga Susan Mwongeli
Tsawon shekaru, al'ummar Afirka ta Yamma suna tafka muhawara game da wa ya fi iya dafa jollof, wato shinkafa dafa-duka. Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambia duka suna iƙirarin su suka fi iya girka shinkafar.
Haka ma mutanen Saliyo, da Togo, da Ivory Coast, da Laberiya, da ma Mali.
A shekarar 2023, Hukumar Ilimi Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNESCO ta ayyana ƙasar Senegal a matsayin yankin da shinkafa dafa-duka samfurin jalof ta samo asali.
An yi imanin cewa shinkafa jalof ta samu ne daga al'ummar ƙabilar Wolof da ke Senegal.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, nau'in jollof na Senegal girki ne da ya zamo gadon tarihi abin girmamawa daga al'ummar Senegal.
Sai dai duk da wannan iƙirari, sauran ƙasashe a Yammacin Afirka, musamman Nijeriya da Ghana, sun ci gaba da saɓani kan wa ya fi su iya shinkafa dafa-duka da ta fi daɗi.
Mece ce jollof?
Jollof girki ne da ake yi a tukunya ɗaya, inda ake dafa shinkafa haɗe da mai, da tumaturi, da albasa, da sauran kayan miya.
Waɗannan su ne kayan dafa jollof mafi ƙaranci, amma akwai ƙarin kayayyakin girki da ake amfani da su, ya danganta da al'adun mutane.
To, me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan shinkafa jollof? A zahiri dai, wannan abinci yana da muhimmanci ga masu ƙaunar sa.
Shinkafa dafa-duka tana da muhimmanci tamkar na tarihi ga al'umma, da farin cikinsu da gwanintarsu a girki. Ana cin shinkafa dafa-duka a wuraren bikin aure da na ranar suna da sauran shagulgula.
Abincin yana da kima ta yadda bayar da shi ga mutane yake nuna kusanci, ya kuma nuna zumunta da soyayyar juna tsakanin iyalai da dangi.
Muhawara kan ƙasar da jollof ɗinta ta fi kowacce batu ne da ke yawan ɗaukar hankali a shafukan sada zumunta inda aka kasa warware musun. Musun ya fi zafi tsakanin 'yan Nijeriya da Ghana.
Hafiz Tijani daga Ghana ya faɗa wa TRT Afrika cewa yana ganin ƙasarsa ce ta fi iya girka shinkafa dafa-duka, ''Jollof ɗin Ghana ita ta fi kowacce a Afirka. Muna saka mata kayan ƙamshi da niƙaƙƙen tumaturi da kifin Salmon''.
Ya ƙara da cewa, ''Ƙamshin shinkafa dafa-dukan kaɗai tun kafin ka ci zai ƙayatar da kai kuma ba za ka manta da shi ba. Cin Jollof 'yar Ghana ba wai maganin yunwa yake ba, zai birge ka''.
Sai dai kuma wata gwanar girki, Chef Racheal daga Nijeriya ta musanta wannan ra'ayi na Tijani.
Ta ce ''Dahuwar jollof 'yar Nijeriya ita ce ke sanya tamu jollof ɗin ta yi fice. Babu wata ƙasar Afirka da ke iya dafa jollof yadda muke yi. Sakamakon cewa salon girkinmu ya bambanta da na sauran mutane, mu muke da jollof ɗin da ta fi kowacce.''
Sai dai tarihi ya nuna cewa an samo shinkafa dafa-duka ne daga al'ummar ƙabilar Wolof da ke Senegal da Gambia.
Wolof su ne ƙabilar da suka fi yawa a Senegal, kuma sun fi yawa a arewacin ƙasar kusa da kogin Senegal River da kuma Gambia River.
A zamanin farkon mulkin mallaka, Turawan Yamma sun fara shigo da shinkafa karyayyiya a matsayin abincinsu na yau da kullum.
An gani a rubuce cewa mutanen Senegal sun fi son karyayyiyar shinkafa maimako wadda ba ta karye ba. Wannan ya sa a yankin ake da sanannen abincin nan mai suna Ceebu jën a ƙasar.
Daga baya farin jinin jollof ya yaɗu zuwa sauran ƙasashe a Afirka ta Yamma.
Cinikayya da ci-rani da auratayya da musayar al'adu, sun taka rawa muhimmiya wajen yaɗuwar shinkafa dafa-duka. Sannan abincin da a yau muke kira shinkafa jollof ya zamo abin alfahari kuma al'adar Yammacin Afirka.
Ana bayar da jollof ga baƙi a matsayin mutuntawa da kyautatawa. Al'ummar Ghana suna girka jollof ɗinsu da shinkafa nau'in basmati, kuma suna yawan saka kayan da ke da sinadarin protein, kamar kaza ko naman saniya.
Su kuwa 'yan Nijeriya, sun fi son amfani da nau'in shinkafa mai doguwar tsaba, sannan sun fi amfani da manja, kifi ko naman saniya. A wurinsu, shinkafar ta fi daɗi idan ba ta yi ruwa ba.
Mutanen Kamaru kuma suna amfani da naman saniya a girkin dafa-duka, yayin da a Senegal aka saka mata manja. Kamar yawancin 'yan Afirka ta Yamma, mutanen Liberia su ma suna saka yaji a dafa-dukansu.
Muhawara kan jalof ba ta da matsaya guda, don haka za ta ci gaba da wanzuwa tsakanin mutane masu tantamar: wa ya fi iya dafa jalof?