Ana sa ran rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump a ranar 20 ga Janairun 2025 a harabar Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington. / Hoto: Others

Daga Sylvia Chebet

Jawabin da Mataimakiyar Shugabar Amurka Kamala Harris ta yi ya nuna alamun kawo ƙarshen zaman fargabar da ake ciki na zaɓe a Amurka.

Tun da farko zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya yi jawabi, inda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓe bayan ya samu ƙuri'u mafi yawa da kuma mafi ƙarancin ƙuri'un wakilan zaɓe bayan da muhimman wuraren da ake zaɓe a ƙasar suka samu goyon bayansa.

Duk da cewa a halin yanzu ta tabbata cewa Trump na hanyarsa ta komawa Fadar White House, ba za a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙasar ba har sai wakilan masu zaɓe sun jefa ƙuri'a a ranar 17 ga watan Disamba.

Wakilan masu zaɓe sun ƙunshi masu zaɓe waɗanda ke wakiltar ra'ayoyin jama'a daga jihohi.

"Masu zaɓen za su haɗu a jihohinsu da kuma zaɓen shugaban ƙasa da mataimaki ta hanyar ƙuri'a," kamar yadda kundin tsarin mulkin Amurka ya nuna.

Daga nan ne masu zaɓen za su aika da takardar shaidar zaɓensu ga mataimakin shigaban Amurka mai ci (shugaban majalisar dattawa), jami'an ƙasar da kuma kotun tarayyar ƙasar da kuma hukumar adana bayanai ta Nijeriya.

Kamar yadda doka ta nuna, dole ne a kai takardar shaidar zaɓen birnin Washington zuwa 25 ga watan Disambar 2024.

Ayyana wanda ya ci zaɓe

Kundin tsarin mulki ya nuna cewa akwai buƙatar a tara 'yan majalisa baki ɗaya da kuma ƙirga ƙuri'u da kuma ayyana wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Za a gudanar da gamayyar taron 'yan majalisar a ranar 6 ga watan Janairun 2025 da misalin ƙarfe 1 na rana.

"Shugaban majalisar dattijai a gaban 'yan majalisar dattijai da wakilai za su buɗe duka takardun shaidar zaɓe inda za a ƙirga duka ƙuri'un da aka kaɗa," kamar yadda doka ta tanada.

A matsayinta na shugabar majalisar dattawa, mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris za ta bude takardar shaidar kada kuri’a sannan ta miƙa su ga ‘yan majalisar wakilai guda biyu da ‘yan majalisar dattawa biyu, wadanda za su kirga kuri’un.

Idan aka samu wanda ya samu rinjaye da ƙuri'u aƙalla 270 kuma ba a samu ƙorafi ba daga mambobin majalisa; za a tabbatar da zaɓen shugaban ƙasar a kuma kammala shi.

Idan ba a samu wanda ya samu rinjaye ba, za a tura sakamakon zaɓen a gaban majalisa domin yanke hukunci. Majalisar wakilai ce za ta yanke hukunci kan wane ne shugaban ƙasa; inda majalisar dattawa ta tantance wanda zai zama mataimaki.

Kamar yadda kundin tsarin mulki ya nuna, "wa'adin shugaban ƙasa da mataimakinsa zai ƙare da misalin sha biyu na rana a ranar 20 ga Janairu...inda a lokacin ne waɗanda za su gaji su zai soma."

Za a gudanar da rantsuwar ne a harabar Majalisar Tarayyar Amurka da ke birnin Washington.

TRT Afrika