Daga Emmanuel Onyango
Jami'an gwmanatin Afirka ta Kudu nasu ci gaba da kare dalilan da suka sanya ake kwaskwarima ga yanayin mallakar kasa da filaye, bayan Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa za a daina bai wa kasar duk wasu kudaden tallafi saboda an ji labarin za a yi wata doka da za ta kai ga kwace filaye.
Afirka ta kudu ta nace kan cewar dokar da Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanya hannu a kai a watan da ya gabata ba "ta kwace filaye ba ce" sai dai wata madogarar "tabbatar da jama'a sun mallaki kasa da filaye".
Har yanzu mallakar kasa da filaye a Afirka ta Kudu na bayyana tsarin rashin daidaiton da aka gani a karkasin gwamnatocin fararen fata 'yan tsiraru da ya sanya mafi yawan gonakin da ba na gwamnati ba suke mallakin farar fata - sama da shekaru 30 bayan kawo karshen mulkin tsiraru farar fata.
A ranar Lahadi Trump ya fada wa 'yan jaridu amma ba tare a kawo shaida ba cewar, "shugabancin Afirka ta Kudu na yin wasu munanan ayyuka, ayyuka kazamai", kuma ana gudanar da bincike.
"Muna saka idanu da bincike har zuwa lokacin da za mu gano me Afirka ta Kudu ke kullawa - za su kwace kasa da filaye, suna kwace filaye, watakila ma suna yin abubuwan da suka fi haka muni," in ji shi.

Ta yaya muka kai ga haka?
Gwamnatocin da suka biyo baya a Afirka ta Kudu sun kasance karkashin matsin lambar su magance wasu kura-kurai na nuna wariya da aka yi a zamanin mulkin fararen hula da suka tilastawa bakaken fata barin kasarsu ta asali - daga baya aka kora su kauyuka da birane.
Bayan shekaru 30 da kawo karshen mulkin farar fata 'yan tsiraru, mallakar kasa ya karkata sosai ga farar fatar.
Wani rahoton tantance yawan gonaki da aka fitar a 2017 ya bayyana cewa kashi 72 na gonaki da filayen da ba na gwamnati ba mallakin farar fata ne, inda bakaken fata kuma suka mallaki kashi 5.
Manufar rahoton ita ce a samar da bayanai kan yawan kasa da mutane suka mallaka duba ga launin fata, kasa da jinsin halittarsu.
Rahoton ya bayar da shawarar samar da dokar da za ta "tabbatar da kasa da gonaki fa filaye sun zama mallaki dukkan jama'ar Afirka t Kudu baki daya".
Kara da dama da aka shigar kan rikicin filaye da gonaki, sun ga yadda kotuna ke bayyana dokokin mallakin filaye a zamanin mulkin farar fata a matsayin wanda uka saba wa kundin tsarin mulki.
Me dokar ta tanada?
Dokar da aka amince da ita a baya-bayan nan ya ba wa gwamnati ta kayyade girman gona "don amfanar jama'a". Shugaba Ramaphosa ya tabatar cewa manufar ita ce a tabbatar da adalci a mallakin kasa.
Afirka ta Kudu "tana ta fuskantar rashin daidaiton mallaka da amfani da gonaki, tare da bayar da kariya ga hakkokin mamallaka," in ji shi.
Ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar "da samun gonaki bisa adali da daidaito kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada".

Meye martanin da aka mayarwa barazanar Trump?
Biloniya abokin Trump, Elon Musk, wanda aka haifa a Afirka ta Kudu, na daga cikin mutanen da ke sukar dokar kwaskwarima kan malkakin kasa a Afirka ta Kudu ina yake goyon bayan matakin da Washington ke shirin dauka kan Pretoria.
Sai dai kuma, wasu kwararru na cewa idan har muzuran Trump da barazanar katse tallafi da gaske a kan barun mallakar gonaki da filaye ne, to martanin nasa ya zama riga malam masallaci, kuma yana bukatar ya fahimci dokar ta Afirka ta Kudu tukunna.
"Donald Trumo bai samu bayanai masu kyau ba" game da dokar daidato ta Afirka ta Kudu, in ji Ongama Mtimka, malamin Jami'a a Afirka ta Kudu kuma masanin siyasa, a tattaunawar da ya yi da TRT Afrika.
Mtimka says. "Duk wadannan kasashe na da nasu dokokin don cim-ma wata manufa. Wannan ne abin da Afirka ta Kudu ke yi," in ji Mtimka.
"Shigar da batun babu biyan diyya na da iyaka kuma ba zai zama abinda Trump da masu tsaurin ra'ayi irin sa ke tunanin gwamnati na kokarin yi da wannan doka ba," ya kara fada.
"Afirka ta Kudu kasa ce da ke d dimokuradiyya mai aiki da kundin tsarin mulki, adalci da daidaito. Gwamnatin Afirka ta Kudu ba ta kwace wata gona ko fili ba," Shugaba Ramaphosa ya bayyana wa a shafinsa na X, yana mai watsi da ikirarin Trump kn batun kwace gonaki a Afirka ta Kudu.
‘Mu ba mabarata ba ne’
Abokin hadakar Ramaphosa, shugaban jam'iyyar DA, John Steenhuisen, ya shigo cikin muhawarar inda ya ce ga "bayani filla-filla" game da sabuwar dokar.
"Ba gaskiya ba ne cewa Dokar na bayar da dama a kwace gonaki ta ci barkatai ba, kuma ta tanadi biyan diyya ga duk wanda yake da halascin mallakin gonarsa," in ji a sanarwar.
"Abin takaici ne cewa daidaikun mutane na neman bayyana wannan gyaran Doka ga Sashe na 25 na Kundin Tsarin Mulki don bayar da dama ga karbe gonaki ba tare da biyan diyya ba."
Ministan Ma'adanai da Man Fetur, Gwede Mantashe ya ce ya kamata barazanar Shugaba Trump ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu kudade ta fuskanci mayar da martani daga kasashen Afirka.
"Mu karfafawa Afirka, mu dakatar da kai albarkatun kasa Amurka. Idan ba za su ba mu kudi ba, kar mu ba su albarkatun kasa," ya fada wa babban taron zuba jari a ranar Litinin.
"Muna da albarkatun kasa a nahiyar, sbaoda haka muna da wani abu," in ji shi, yana mai karawa da cewa "Mu ba mabarata ba ne."

Ana wasan siyasar duniya?
Afirka ta Kudu ce babbar kawar Amurka a nahiyar Afirka. A 2022, kayan da aka samar a Amurka da aka shigar da su Afirka ta Kudu sun kai na dala biliyan 9.3, inda ita kuma ta sayi na dala biliyan 16.2, kamar yadda Oishin Kula da Kasuwanci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.
Alkaluman Amurka sun bayyana cewa kasar ta taimaka wa Afirka ta Kudu da dala miliyan 440 a shekarar 2023.
Amma Afirka ta kudu ba ta taba jin nauyin bayyana wasu bangarori da ta ke da sabanin ra'ayi da Amurka ba.
Pretoria ta shigar da karar kisan kiyashi da Isra'ila ta aikata a gaban Kotun Kasa da Kasa a watan Disamban 2023, duk da sabawa Amurka da ya yi, da kuma kasancewar ta babbar mai shigar da makamai isra'ila.
A watan Mayun wannan shekarar, jakadan Amurka a Afirka ta Kudu ya zargi kasar da samarwa rasha makamai a yakin da take yi a Ukraine. Wani bincike mai zaman kansa bai iya samo hujjar tabbatar da ikirarin jakadan ba.
Afirka ta Kudu na daga kasashen da suka kafa kungiyar BRICS da ke tattauna wa kan daina amfani da dalar Amurka a 'yan shekarun nan. A watan da ya gabata Shugaba Trump ya ce babu damar da kasashen za su maye gurbin dalar Amurka da wani kudi.
"Duk wata kasa da ta yi kokarin hakan to za ta marabci karin haraji, kuma ta yi bankwana da Amurka."
"A bayyane yake karara cewa Donald Trump na amfani da diflomasiyyar tirsasawa wanda Amurka ke amfani da ita tsawon shekaru a kan gwamnatocin da suka ki ba ta kai bori ya hau," in ji Mtimka.
"A yanzu ba mu san cewa Afirka ta Kudu na da zabin manufofin kasashen waje d aba sa dadadawa Amurka a 'yan shekarun nan. Tun daga yakin Rasha da Ukraine, kai Isra'ia kara Kotun Kasa da Kasa, da kuma ayyukanta a BRICS," in ji malamin jami'ar.
"Gwamnatin Trump na kallon wadannan abubuwa a matsayin halayyar kawancen da ba za a amince da su ba," in ji shi.