Daga Firmain Eric Mbadinga
A wata fitowa mai muhimmanci a fim din Edward Scissorhands na Hollywood, mace mai sana'ar kayan kwalliya Peg Boggs ta gano babban jarumi da aka bari a wani gida, kuma ta kaɗu da ganin kala da ƙuraje ko tabo-tabon da ke jikinsa.
Ta yi kokarin rufe abin da ta gani ta hanyar kwalliya a yayin da Edward ke sauya kama, amma bai wani damu ba. Peg ta ƙarƙare da ɓata abin, amma kuma saƙon da ake son isarwa ga masu kallo bai ɓata ba.
A rayuwa, Tatiana Mengui 'yar kasar Kamaru na son a ko yaushe ta zama cikin kwalliya, kuma kowa ya zama yana kallonta.
Hakan ya sa a duk lokacin da mai aikin bayar da kudaden da ke da shekaru kimanin 30 za ta fita daga gida, sai ta yi kwalliya a fuska ta hanyar shafa hoda da sauran su.
Rebecca Maria, mai sana'ar yin kwalliya da ke birnin Accra na Ghana, da Valentine da ke zaune a Libreville sun yi amanna cewa amfani da kayan kwalliya don a yi kyau wajibi ne musamman ma ga mata.
"Kowacce mace na jin tana da kyau idan ta yi kwalliya. Kwalliya ta shafi jin mace na da kyau a fata, kuma dole mace a ko yaushe ta yi kokarin yin kyau sosai," in ji Valentine yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Akawun mai shekara 34, ta yi gaggawar ƙarawa da cewa ta samu labarin illar wasu kayan kwalliya, wanda hakan ya sanya dole ne mata su kula sosai wajen zaɓin kayan kwalliya.
A yayin da Valentine ta nace kan "ba ta zama mai tsananin son yin kwalliya ba", Tatiana kuma ta amince cewa muni za ta yi idan ba ta yi kwalliya ba.
Tatiana ta fara ne shekaru goma da suka gabata, wadda ta ji tana bukatar daukar mataki bayan da aka tsokane ta game da yadda take a yankinta na Mbam da ke Kamaru.
Ta bayyana cewa "Idan fuskokinmu ba su dace da ka'idojin da al'umma suka saka ba na kyau, sai kawai a ce munana ne mu. A yayin da na gano kwalliya a 2015, na yi tunanin 'ga hanyar rufe bakunan 'yan sa ido',"
"Na zama mai tsakanin kaunar yin kwalliya saboda ina tsoron kar a yi watsi da ni a cikin jama'a. Tare da yin kwalliya, na sake samun tabbacin kaina, kuma ma na daga samun kima a kaina."
Ra'ayin mutane game da kwalliya
Bincike baya-bayan nan da Cibiyar 'Renfrew Centre Foundation' a Canada ta yi ya bayyana cewa kaso 44 na mata na jin ba sa jan ra'ayin maza idan ba su kwalliya ba.
A 2013, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ja hankalin jama'a kan hatsarin lafiya da ke tattare da wasu kayan kwalliya.
Ta yi nuni da cewa sinadaran d aake hada wa a samar da kayan kwalliyar sun hada da masu kutse kan kwayar halitta da ka iya janyo rashin haihuwa ko ciwon daji na fata.
Kwararriya kan kayan kwalliya Rebecca na yawan haduwa da mutane da suke son kwalliya sama da wasu. Domin kawata masu zuwa wajen ta, tana amfani da kayan kwalliya daban-daban.
Ta lissafa kayan da take amfani da su wajen yi wa mutane kwalliya da suka hada da: hoda nau'i daban-daban, burushi kala-kala da jan baki da ja gira da kwalli da sauran su.
Mai sana'ar yin kwalliya da ta ke koyawa wasu, ta bayyana cewa tana da nau'in kwastomomi biyu: masu son a yi amfani da kayan kwalliya da yawa sosai, da masu son a dan saka musu kadan kawai. Saboda tana da masu zuwa sosai, Rebecca na amfani da kayan kwalliya marasa cutarwa.
Baya ga tambaya game da ingancin kayan kwalliyar da ake sayarwa ta ci barkatai a shaguna, likitan fata na kasar Togo Waguena Gnassingbe ya yi gargadi kan hatsarin da ke tattare da wasu sinadarai da ake saka wa a cikin kayan kwalliyar fuska da dama.
Jerin kayan ya hada da hoda da kwallicda rini da ƙona fata da kaolin.
Duk wadannan abubuwa na iya janyo matsalar lafiya. Hoda kan iya janyo daɓɓara-daɓɓara a fuska, rina fata ma na janyo ta dinga zafi tana ciwo.
Dr Gnassingbe ya kuma ce "Kwalliya ta zama guba idan ta fara busar da fata, ko idan ta dinga janyo zafin fuska, ko janyo dabbara-dabbara da ma kuraje," yayin da Tatiana kuma ta ce tana sane da irin wadannan hadurra kamar yadda Dr Knassingbe ya zayyana.
Ta shaida wa TRT Afirka cewa "Na taba samun matsala a fata da ta numfashi saboda rashin ƙwari da fatata ke da shi. Amma ba zan iya daina yin kwalliya ba; abun ya fi karfina."
A zaɓa a darje
Ga mutane irin su Tatiana da ba za su iya hakura da yin kwalliya ba kullum, Dr Gnassingbe ya ba su shawara da su ilmantar da kansu game da me ya kamata su yi amfani da shi.
Ta bayar da misali bai kamata kayan kwalliya da ke dauke da sinadaran 'benzophenones 1 da 3' su zama ana sayar da su ba.
Su 'benzophenones 1 da 3' sinadarai ne da ya kamata a same su a cikin kayan da ake yakar ciwon 'ultraviolet rays'. An gano suna janyo matsalar haihuwa ga mata.
Ga mutanen da fatarsu ba ta da kwari, ko masu yawan samun kuraje, radadin fata da kodewar ta, Dr Gnassingbe ya ce fatarsu z ata iya komawa yadda take.
A yayin da kasuwar kayan kwalliya ke ci gaba da shahara a duniya, kwalliya ta zama abin da wasu da yawa ba za su iya hakura da yin ta ba.