Ƙarfafa dangantaka da Turkiyya da inganta ayyukan tsaro na haɗin gwiwa zai kasance mai muhimmanci yayin da Turai ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro a faɗin duniya. / Hoto: AA Archive

Turkiyya ta kasance a wuri na musamman kuma mai muhimmanci dangane da tsaron Turai. Sojojin Turkiyya ne na biyu mafi girma a ƙungiyar NATO, haka kuma ƙasar na taka muhimmiyar rawa wurin daƙile barazanar ta'addanci a yankin, da kuma taimakawa wurin samar da zaman lafiya.

A daidai lokacin da Turai ke fama da rashin tabbas musamman na ta'addanci da kuma kutsen internet, da hijirar jama'a wadda yaƙi ke haifarwa da sauyin yanayi da talauci, Turkiyya na taka muhimmiyar rawa wurin taimakawa domin magance waɗannan matsalolin.

Duka hanyoyi na bin ta Turkiyya

A yayin da ta raba ƙafa a tsakanin nahiyar Turai da Asia, inda Turkiyya take ko kuma mazauninta ya ba ta wata irin muhimmiyar dama, ganin cewa ita ce ke da iko kan shige da ficen Bahar Aswad da kuma mashigin teku na Istanbul, waɗanda wurare ne na musamman domin wucewar kayayyakin soji a faɗin duniya da makamashi da abinci.

Akwai bututai na makamashi da dama waɗanda suke da matuƙar amfani ta fannin tattalin arziƙi da tsaro waɗanda suka ratsa ta cikin Turkiyya zuwa Turai: misali bututun Baku-Tbilisi-Ceyhan (BTC), da bututun Trans-Anatolian Natural Gas (TANAP) da Turkish Stream (Türk Akımı) da kuma bututun Nabucco.

Kula da iyakoki masu hatsari

Haka kuma Turkiyya tana da iyaka da wasu daga cikin wurare marasa aminci a Gabas ta Tsakiya, wato yankin Caucasus da Balkan. Turkiyya tana taka muhimmiyar rawa idan aka yi la'akari da wurin da take ta hanyar tabbatar da zaman lafiya a yankin. Ta hanyar samar da zaman lafiya a tsakanin makwabtanta da ke yankin, Turkiyya kai tsaye tana taimakawa wurin samar da tsaro da kwanciyar hankali a Turai.

Sakamakon Turkiyya ta zama mamba a ƙungiyar NATO tun daga 1952, hakan ya ƙara ƙarfafa ƙungiyar a kudu maso gabashi. A cikin shekarun da suka gabata, Turkiyya ta inganta matakan tsaro na NATO ta hanyar ba da gudummawa ga albarkatun soji da kadarorinta. Waɗannan sun haɗa da bayar da sansanonin soji da fasahar zamani ta soji da kuma halartar ayyuka da dama na NATO, waɗanda duka suke ƙara bunƙasa tsaron ƙawancen.

Sakamakon yadda take samar da sansanoni ga sojojin NATO, Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa wurin ƙara inganta muradun ƙawancen. Gudunmawar sojanta na da muhimmanci ga gamayyar tsarin tsaro na Turai, wanda ke zama katanga don fuskantar barazanar da ka iya tasowa daga kudanci da gabas.

"Turkiyya na taka muhimmiyar rawa ba wai ga tsaron Turai kawai ba, amma ga tsaron baki ɗaya ƙawayen Yamma, sakamakon tana daga cikin muhimmiyar mamba ta NATO tsawon shekara 72. Kamar yadda aka gani a yaƙin Ukraine, Turkiyya ta kasance muhimmiyar ƙasa domin samar da tsaron soji ga Turai. Haka kuma, matsayar Turkiyya dangane da muhimman hanyoyin da ake bi na hijira zuwa Turai da kuma rawar da take takawa kan samar da makamashi suka sa take da muhimmanci ga tsaron Turai," in ji Enes Bayrakli, Mataimakin Farfesa a Jami'ar Turkish German a tattaunawarsa da TRT World.

Ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katz, ba da jimawa ba ya caccaki Turkiyya dangane da dangantakarta da ƙawancenta da NATO da kuma irin caccakar da Shugaban Turkiyya Recep Erdogan yake yi game da Isra'ila.

Amma duk da haka kiran da Isra'ila ta yi kan Turkiyya ba zai zama komai ba, domin Turkiyya mamba ce muhimmiya kuma ta jima a matsayinta ta mamba a ƙawancen, inda ita kuma Isra'ilar ƙaramar mamba ce.

Ƙawancen ba zai yi sakacin rasa ƙasa ta biyu da ke da dakaru mafi girma a ciki ba, wanda hakan zai jawo cikas ga tsaron na Turai musamman a kudu maso gabashi

Ƙoƙarin daƙile ta'addanci

Turkiyya ta himmatu wajen yaki da ta'addanci. A matsayinta na kasa wadda ke sahun gaba, ba za a iya misalta rawar da take takawa wajen yaki da ta'addanci ba. Kasar dai na taka rawar gani wajen yakar kungiyoyin ta'addanci irinsu PKK, Daesh, da FETO.

Wadannan kungiyoyi ba kawai suna haifar da babbar barazana ga Turkiyya ba, har ma suna da damar yin tasiri ga kasashen Turai. Matsayin da Turkiyya ta dauka na yaki da wadannan kungiyoyin ta'addanci na taimakawa wajen daƙile barazanar 'yan ta'adda da ke kan iyakoki, wanda hakan kai tsaye zai kara inganta tsaron cikin gida na Turai, da kuma ba da gudummawa wajen samar da yanayi mai aminci ga 'yan kasashen Turai.

Ribar tattalin arziki da amfana da juna

Zaman Turkiyya a matsayin muhimmiyar ƙasa da ake wucewa da makamash shi ma wani lamari ne mai muhimmanci game da ita. Tsaron makamashi na Turai ya dogara ne kacokan kan hanyoyin da makamashi ke wucewa ta cikin Turkiyya, wanda hakan ke taimakawa wajen samun kwanciyar hankali a samar da makamashi.

Ayyukan da Turkiyya ke yi musamman na makamashi, waɗanda suka haɗa da samar da bututu da kayayyakin ci gaba, na da muhimmanci matuƙa ga dogaro da kai ta ɓangaren makamashi ga Turai.

Bugu da ƙari, dangantakar tattalin arziƙin Turkiyya da Turai ta ƙara yauƙaƙa yadda suke amfana da juna. Dangantaka mai ƙarfi ta tattalin arziƙi na taimakawa sosai wurin samar kwanciyar hankali da kuma haɓakar tattalin arziƙi waɗanda duka suna da muhimmanci ga tsaro baki ɗaya.

Yarjejeniyar fitar da hatsi ta Bahar Aswad wanda ofishin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya da Turkiyya suka jagoranta a Yulin 2022, ta taimaka wurin dawo da yadda ake samar da hatsi daga Ukraine, wadda tana daga cikin ƙasashe mafi girma da ke fitar da hatsi, inda Turkiyyar ta bayar da dama aka rinƙa wucewa da miliyoyin tan na hatsi ta Bahar Aswad.

Diflomasiya da kwanciyar hankalin yanki

Aikin da Turkiyya ta yi wajen inganta zaman lafiya da tsaro a Gabas ta Tsakiya, Balkans, da Caucasus na da muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin yankin da ya shafi tsaron Turai.

Ta hanyar manufofin diflomasiyya da na soja, Turkiyya ta yi aiki domin magance rikice-rikice da kuma samar da kwanciyar hankali a waɗannan muhimman fannoni. Ƙoƙarinta na diflomasiyya da samar da kwanciyar hankali a yanki sun yi daidai da muradun Turai kuma suna ba da gudummawa matuƙa wurin samar da yanayi mai aminci.

Idan aka yi la’akari da rawar da take takawa da gudummawar da take bayarwa, ba za a iya musun muhimmancin Turkiyya ga tsaron Turai ba. Wurin da ƙasar take da kuma matsayinta na mamba a NATO da ƙoƙarin da take yi na yaƙi da ta'addanci da kula da yanayin gudun hijira da irin yadda take bayar da tsaro ɓangaren makamashi duk suna yin nuni da irin muhimmancin da ƙasar ke da shi .

Ƙarfafa dangantaka da Turkiyya da inganta ayyukan tsaro na haɗin gwiwa zai kasance lamari mai muhimmanci yayin da Turai ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro a faɗin duniya.

Tabbatar da zaman lafiya da hadin gwiwar Turkiyya na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da ci gaban nahiyar Turai, kuma amincewa da muhimmiyar rawar da take takawa na da muhimmanci ga samar da makomar nahiyar.