Amurka da kawayenta su ne ke da alhakin barin Isra'ila tana aikata laifukan yaki

Amurka da kawayenta su ne ke da alhakin barin Isra'ila tana aikata laifukan yaki

Isra'ila ta kai hari a asibiti cike da mutane, saboda ta san kasashen duniya ba za su fadi laifinta ba, a cewar masana.
Hamas ta kira harin da aka kai asibiti a matsayin “kisan rashin imani”. / Hoto: AFP

Daga Murat Sofuoglu

Duniya ta yi zugum yayin da sojin Isra'ila suka yi kisan kiyashi kan mutane akalla 500, yawancinsu mata da yara, lokacin da ta kai hari a asibiti a Gaza, a makon nan.

Mummunan harin, wanda masana suke kira da laifukan yaki, ya faru ne 'yan awanni bayan da Amurka da kawayenta na kasashen Yamma suka yi watsi da kudurin da Rasha ta gabatar a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don tsagaita wuta a Gaza.

Isra'ila ta san abin da ta taka sanin cewa tana da cikakken goyon bayan kawayenta na Yamma, sannan sojinta suna da tabbacin za su tsira daga laifukansu na kai hari a asibitin Kiristocin na jinkai, wato Al Ahli Arab Hospital a Gaza.

“A wannan hari a asibiti, mun ga karairayin Isra'ila tun farkon fari,” in ji Riham Abuaita, wani Kiristan Bafalasdine mazaunin Ramallah, wanda ya jagoranci kafar binciken-sahihanci ta Kashif, domin tantance ikirarin harin.

Falasdinawa suna duba illar da da aka yi wa wani coci da mutane suka nemai mafaka, a asibitin al-Ahli, a birnin Gaza, Oktoba 18, 2023. / Hoto: Others

Karyar Isra'ila ta farko ita ce kan wa ya kai harin asibitin, in ji Abuaita.

Dan lokaci bayan fitowar rahotanni game da harin, jami'an Isra'ila tun daga Firaminista Benjamin Netanyahu, zuwa kan shugaban 'yan adawa Yair Lapir suka fara yada labari bisa wani bidiyo da ba a tabbatar ba, wanda ya nuna cewa kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad ce ta kai harin bam din a asibiti.

Ely Cohen, wani dan jaridar Isra'ila, ya zargi Hamas bisa dogaro da bidiyon bogi, in ji Abuaita.

Amma bayan awanni, sai Netanyahu da abokansa suka goge bidiyon daga shafukansu na sada zumunta ta inda a baya suka yada. Abuaita ya gaya wa TRT World cewa, “Ba na gaskiya ba ne. Tsohon bidiyo ne”.

“Karya ta biyu ta zo ne daga wani bidiyon bogi na wani shafin Twitter mai suna Farida Khan, wanda ya yi ikirarin cewa ita 'yar jaridar Al Jazeera ce, kuma wai ta gani da idonta inda makami mai linzami na "Ayyash 250" ya sauka kan asibitin.

Wannan ma ba gaskiya ba ne, saboda Al Jazeera ta fitar da sanarwa mai cewa shafin Twitter ba shi da alaka da tashar” in ji Abuaita. Ayyash 250 wani nau'in makami ne mai linzami na Hamas.

Isra'ila tana ruwan bam kan Falasdinawa yayin da kuma take watsa farfaganda don yin rufa-rufa kan laifukan yaki da take aikatawa, kamar dai yadda suka aikata lokacin aka kashe Shireen Abu Akleh, 'yar jaridar Al Jazeera, in ji Abuaita.

Wani zane da ke nuna 'yar jarida Ba'amurkiyar Falasdinu, Shireen Abu Akleh kan wani bangare na ginin iyakar Isra'ila a birnin Bethlehem na Gabar Yamma. / Hoto: Others

Da farko Isra'ila ta karyata cewa alhakinta ne kisan 'yar rahoton, har ta zargi mayakan Falasdinawa irin yadda a yanzu take kauracewa alhakin harin asibitin Gaza.

Amma bayan an fito da hujjojin da ke nuna karya Isra'ila take, tare da matsin lambar kasashen duniya, a karshe Isra'ila ta amsa laifinta da cewa wani sojanta ne ya kashe Shireen Abu Akleh.

ABuaita ya ce, “Bayan kashe ta, sun yada karairayi game da abin da ya afku,” kamar yadda Isra'ila take ta yi tun bayan harin asibitin nan.

Duk abin nan da ake yi, Isra'ila ta dogara ne da kasashen Yamma, musamman Amurka don su taimake ta ta kauce wa hukunci, duk da irin hujjojin cewa sojinta sun aikata laifukan yaki.

Ba dadewa Amurka ta aika da jirgin ruwanta na yaki mai daukar jiragen saman yaki zuwa Tekun Bahar Rum don karfafa goyon bayanta ga kasar Yahudawan.

Nadia Ahmad, farfesan fannin shari'a ce a Cibiyar Tsaro ta Orlando, wato Race and Rights ta ce, “Saboda muhimmancin alakar siyasar yankin duniya, da kungiyoyin kamun kafa masu karfi, da kacaniyar diflomasiyyar duniya, Isra'ila tana cimma matsayin cin karenta ba babbaka, irin yadda ko ta ina ka kalla laifukan yaki ne".

Amma ta yi gargadin cewa ayyukan sojin Amurka a Falasdinu shi ne saka-ido, amma Amurka tana bukatar daidaita ayyukanta da doka da mutunta hakkokin dan'adam.

Ta fada wa TRT World cewa, “Yana da muhimmanci ba mu taimakawa duk wani nau'in rikici kan rayukan marasa laifi a Gaza. Al'ummar duniya dole ta ta hada kai ta yi allah-wadai da duk wani zalunci, kuma a saka gabadaya alhakin duk wani laifin yaki da Isra'ila ta aikata".

Shin duka Falasdinawa abin hari ne?

Makon baya, Herzog ya ba da wani rikitaccen bayani kan manufar goyon bayan Isra'ila don kashe tarin farar hular Falasdinawa inda yake cewa, “Gaba daya kasar ce take da alhaki” kan harin Hamas na 7 ga Oktoba kan Isra'ila.

Herzog ya ce 'ya Gaza ya kamata su a ce sun “yi bore”, kuma sun “yaki” ba Isra'ila ba, wadda ta mamaye Falasdinu, amma sun yi wa kungiyoyi kamar Hamas tawaye.

Wannan ya nuna cewa Isra'ila suna da matsala da duka Falasdinawa saboda wadanda ke rayuwa a yankin Gabar Yamma da aka mamaye, inda Hamas take da iko, suna shan matsai daga sojin Isra'ila a kullum, in ji Abuaita.

Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun cinna wuta kan gidajen da motocin Falasdinawa a Ramallah, Gabar Yamma ranar 21 ga Yuni, 2023. / Hoto: AA

Ta tambaya “Suna musanta cewa suna kashe fararen hula saboda Hamas tana amfani da su don neman kariya. Amma ina kuma Gabar Yamma?”

A zahiri, mamayar Isra'ila a Falasdinu, wadda ta faru tun kafin kafa Hamas a shekarun 1990s, ta janyo hallakar dubban Falasdinawa, sannan ta raba dubban daruruwa daga gidajensu, kuma yanzu abin yana cigaba da faruwa.

“Suna yin kisan ba wai don Hamas tana nan ba. Suna so su kashe tarin Falasdinawa yadda suka so, saboda su masu laifukan yaki ne.”

Shagabannin Isra'ila sun karfafa irin wannan fahimtar ta hanyar kalamansu na tunzurawa.

Abir Kopty, wani Bafalasdine marubuci kuma malamin makaranta ya ce, “Isra'ila ta bayyana karara tun a farkon wannan yakin cewa tana so ne ta batar da Gaza. Kodai ta kashe kowa da kowa, ko ta tursas su su fice. Isra'ila tana fada wa duniya cewa tana yaki da “dabbobin mutane”, kuma Netanyahu ya kamanta yaran Gaza da ‘yaran bakar duniya’.”

Ya fada TRT World cewa “Wannan yare ne na masu kisan kare-dangi, duk abin da Isra'ila take yi za a kalle shi ta wannan mahanga”.

A salon yakin farfaganda, wasu 'yan Isra'ila su ma suna kokarin kamanta Hamas da Daesh, don saka tunani cewa 'yan Isra'ila suna yakin abin da suka kira masu fafutukar addini, wadanda suka fito don kashe mutane marasa laifi.

Amma ita Abuaita, wanda Kirista ce Bafalasdine, ta musanta irin wannan ikirari. Ta ce, ba yakin Yahudawa da Musulmi ko Kiristoci ne ba.

Ta ambata cewa, “Wannan ba yakin addini ba na. 'Yan Isra'ila suna kokarin saka tunanin yakin addini. Amma ba yakin ba batun Musulmi suna yakar Yahudawa ba ne”.

“Yaki ne na Isra'ila ke yakar Falasdinawa. Batu ne na Isra'ila ta mamaye Falasdinu. Ba rikicin addini ba ne kwata-kwata.”

TRT Afrika