Daga Charles Mgbolu
Idan kwallon kafa rayuwa ce ta mintuna 90, to shirya halartar gasa ne ruhin wasan.
A yayin da magoya baya suke ta shewa da murna game da gasar cin Kofin Afirka ta (AFCON) da abin da za ta iya kawowa, gasar da za a gudanar a tsakanin 13 ga Janairu da 11 ga Fabrairu 2024, - na janyo cece-ku-ce tsakanin nahiyoyi.
Tarayyar kwallon kafa ta Afirka ta yi karo da kungiyoyin kwallon kafa na Turai, tun bayan da Tarayyar Kwallon Kafar Afirka (CAF) ta sanar da lokacin gudanar da gasar AFCON da kasashe 24 za su fafata a garuruwa biyar na kasar Côte d'Ivoire.
Mafi yawan kungiyoyin kwallon kafar Ingila za su rasa manyan 'yan wasansu 'yan Afirka idan har aka gudanar da AFCON a tsakiyar kakar wasanninsu, kuma da yawan su sun nuna ba sa son sakin 'yan wasan kafin gasar.
Dr Patrice Mostepe, shugaban CAF, ya dage kan lallai a dage lokacin gudanar da gasar daga watanni Yuni da Yuli, wanda ya yi daidai da lokacin tafiya hutu na gasar ta kasa da kasa zuwa wannan watan na Janairu saboda yanayi a Côte d'Ivoire.
A yayin da yake fitar da jadawalin, Mostepe ya shaida wa taron 'yan jaridu a Moroko cewa "Ba zai yi kyau ga kwallon kafar Afirka ba idan aka yi gasar a wannan lokaci."
Niran Adesanya, mai nazari kan harkokin kwallon kafa a Nijeriya kuma mai gabatar da shirye-shirye ya ce ba abun mamaki ba ne yadda kungiyoyin Turai suka nuna matsala game da hakan.
"Janairu da Fabrairu na da matukar muhimmanci a jadawalin kwallon kafa. Kungiyoyin kasashen Yamma na dawowa daga hutun gasar kasa da kasa, kuma lokacin ne mafi kyau na murmurewa da samun maki." in ji Adesanya yayin zantawa da TRT Afirka.
Gaskiyar zance
A watan Nuwamban 2021, an takurawa mai horar da 'yan wasan Liverpool Jurgen Klopp ya fitar da bayanan karin bayani bayan ya yi a wajen taron 'yan jaridu na bayan wasanni saboda kalaman da ya ya yi na kiran gasar AFCON da "'yar karamar gasar Afirka".
Ya kara da cewa "Na ji cewa a lokuta daban-daban cewa babu tsagaitawa a yayin gasar har zuwa watan Maris, akwai karamar gasa a Afirka."
Zargin da aka yi wa Klopp na kaskantar da AFCON ya janyo nuna bacin rai a shafukan sada zumunta, inda wani dan jaridar Afirka ya nemi lallai da manajan 'yan wasan ya fito ya bayar da hakuri a yayin wani taron.
Dan kasar Jamus din ya ce martanin nasa ba ya fita daga shafin da ake batu a kai, ind aya kara haske da cewa kawai yana bayyana damuwarsa ne saboda zai rasa 'yan wasa irin su Sadio Mane (Sanagal), Mohamed Salah (Masar) da Naby Keita (Guinea) a yayin gasar.
A watan Disamban 2021, makonni kadan kafin gasar Janairun 2022 ta gasar Turai, Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Kafar Turai Nasser al-Khelaifi ya yi korafi game da kungiyoy kan yadda aka samu cin karo na lokacin gudanar da gasar guda biyu.
Amma a yayin da CAF ta karkata ga ci baya a shekarun da suka shude, sauya lokacin gudanar da gasar zuwa wasu watanni a nan gaba kuma lokacin da yanayi ba shi d akyau ga kwallon kafa, to zai zama kungiyar ta bayar da fifiko ga bukatar nahiyar.
Darussan da aka koya a baya
A yayin gasar AFCON 2019, da Masar ta karbi bakunci a tsakanin watannin Yuni da Yuli, lokacin zafi ne wanda ya sanya dan kasar Uganda Denis Onyango gajewa ana tsaka da buga wasa.
CAF ta nace kan cewa Janairu ne lokacin da ya fi dacewa a shekara a gudanar da gasar. Sun ki su janye duk da korafin da kungiyoyin Turai suka gabatar.
"A nan ake yada 'yan wasa, musamman wadanda har yanzu suke kokarin kaiwa kololuwa a sana'arsu ta kwallo," in ji John Ofori, mai nazari kan harkokin wasanni a Ghana.
"Abun takaici dole su zabi bangare daya, buga wasanni a wadannan kungiyoyi ne suke samun kudaden kula da rayuwarsu kuma a nan ne suke gina rayuwarsu ta aiki. 'Yan wasa na yawan tsintar kan su a cikin yanayi mai wahala."
Mai gabatar da shirin wasanni a talabijin a Nijeriya Blessing Nwosu ba ta iya yarda sosai ba. "Wannan babban batu ne, saboda kamar yadda yake ga kungiyoyin Turai da suke korafi kan suna bukatar 'yan wasansu su yi kokari a gasar, kungiyoyin Afirka ma na bukatar gwarazan 'yan wasan a gasar AFCON."
CAF ta kulla yarjejeniya da kungiyoyin Turai don gasar AFCON 2022 kan su saki 'yan wasan su dawo gida a watan janairu, in ji Ofori, tana mai cewa wannan yarjejeniya na da amfanarwa sosai.
Ofori ta shaida wa TRT Afirka cewa "Idan ya zama saura mako guda a fara gasa, mai masu horar da 'yan wasa za su iya yi a gajeren lokaci?
"Ta yaya 'yan wasan za su kafar juna? Kwanaki nawa suke bukata don su san juna su kulla dabarun cin wasa? Ina nufin wannan babu adalci. Ya kamata kungiyoyin Yamma su girmama wannan gasa."
Kungiyoyin Turai na muhawarar cewa abun da ya sanya suka ki sakin 'yan wasan shi ne saboda tsoron kar 'yan wasan su samu rauni a gasar ta AFCON, wanda zai hana su buga wasanni idan sun dawo gasar ta Turai."
Wadannan kungiyoyi sun kuma yi nuni da cewa 'yan wasna da ake saki suna ci gaba da karbar albashinsu, a yayin da suke bugawa kasarsu wasa. Duba da haka, ya zama lallai kungiyoyin su dauki kwararan matakai.
Dokokin kare manufofin kungiyoyi
Dokokin FIFA na taimakawa kasashen Afirka ta fuskar kwallon kafa. Sashe na farko na dokokin ya ce "Dole kungiyoyi su saki 'yan wasa zuwa kasashensu, matukar kasashen sun kira 'yan wasna kan su je su buga musu wasanni."
Amma ba wajibi ne ga kungiya ta saki 'yan wasa a lokacin da ba na gasar kasa da kasa ba - a watan Janairu babi irin wannan gasa.
Ofori ta ce "Kamar kokarin hawa tsauni da dutse ne, sai ya fado ya make ka. Kamata ya yi dokokin su tilasta wa kungiyoyin Turai su saki 'yan wasa, kuma a kan lokaci. Tilastawa na nufin daukar matakan da suka dace."
To me 'yan wasan Afirka da wannan dambarwa ta rutsa da su za su yi?
"Ya rage na 'yan wasan su san meye abin yi," in ji Adesanya. "'Yan wasan Afirka da dama sun nuna me suke so. Dider Drogba Michael Essien da Samuel Eto'o, da wasun su Sun fada wa kungiyoyinsu cewa 'A'a, za n buga a gasar AFCON'."
Batun kudade
A watan Agustan 2022, shugaban Napoli, Aurelio De Laurentiis ya bayyana cewa kungiyarsaba z ata sanya hannu da 'yan wasna Afirka ba sai sun yarda ba za su buga wasa a AFCON ba.
Tsohon dan wasan Napoli dan kasar Sanagal Kalidou Koulibaly ya yi saurin sukar De Laurenttis saboda wannan barazana, yana cewa hakan kamar dakile 'yan wasan Afirka matasa da ke son gina rayuwarsu ta kwallon kafa ne."
"A wajena, abu mafi muhimmanci shi ne a girmama kowa. Ba za ka iya magana ga kungiyoyin Afirka haka ba. Dole ne ka girmama su, kamar yadda kake girmama kungiyoyin Yamma."
Gwarzon dan aksar Kamaru Eto'o ma ya yi magana sosai kan wannan batu, inda ya nace kan lallai duniya ta gyara jadawalinta saboda gasar Afirka, kuma 'yan wasan Afirka su yi tsayin daka su kare AFCON.
Rashin dan wasan gaba na Nijeriya da ke taka leda a Napoli, Victor Osimhen a wasannin farko na neman cancantar halartar gasar Kwallon Kafa ta Duniya 2026 abu ne da ya girgizar kungiyarsu, yanzu idan bai halarci gasra AFCON ba, Super Eagles na cikin hatsari.
Nwosu ta ce "Ya kamata Napoli ta kula sosai kan batun sakin Osimhen saboda ba sa son ya je ya ji ciwon da zai hana shi buga wasa a kakar wasannin bayan gama AFCON. Amma kuma, ka yi tunani a ce kungiyar Nijeriya ta fita gasar AFCON babu Osimhen."
A yayin da ake ci gaba da muhawara, magoya baya na fatan za a warware wannan takaddama.
Ofori ya ce "Abun da muke so a matsayin mu na nahiya shi ne yin kwallo mai kyau. MUn fuskanci kalubale sosai na fili da na boye. A matsayinmu na mutane, ina tunanin mun cancanci jin dadin wannan gasa."