Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Hadi Sirika ya musanta zargin aikata laifin almundahana da ya shafi kusan Naira biliyan 2.7 da Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙara a kansa.
An gurfanar da Sirika ne a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis tare da ‘yarsa Fatima, da sirikinsa, Jalal Sule Hamma, da wani kamfani mai suna Al Buraq Global Investment Limited.
A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce za ta gurfanar da Sirika da wasu mutane uku a gaban kuliya.
Takardar tuhumar ta yi zargin cewa Sirika ya yi amfani da mukaminsa na minista wajen bayar da kwangila ga ‘yarsa da surukinsa, da kuma abokan huldarsa.
Ita ma ‘yar tasa da surukin nasa da suka halarci kotun tare sun musanta zargin da ake musu na tuhuma shida da aka karanta musu, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito. Bayan musanta tuhumar da ake yi musu ta zamba, lauyoyinsu sun gabatar da bukatar neman belinsu wanda alkali ya bayar.
Dokokin belin
Mai Shari’a Oriji ya bayar da belin nasu ne a kan naira miliyan 100 kowannesu da kuma gabatar da mutum bibbiyu da za su tsaya musu.
Dole ne wadanda za su tsaya masa su kasance ’yan kasa masu cikakken adireshi na gida yayin da daya daga cikinsu ya mallaki kadarori da takardar shaidar zama wacce Ministan FCT ya sanya wa hannu.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin ka da wadanda ake ƙara su fita kasar ba tare da izinin kotu ba.
Kotun ta sanya ranar 10 ga watan Yuni domin fara shari’ar.
Tuhumar Hadi Sirika
Sirika ya yi aiki a matsayin Ministan Sufurin Jiragen Sama a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A cikin watan Fabrairu ne hukumar EFCC ta kama ɗan’uwan Sirika Abubakar Sirika bisa zargin badakalar kwangila a ma’aikatar sufurin jiragen sama.
A lokacin da yake riƙe da mukamin minista, Sirika ya fuskanci zarge-zarge da suka hada da karkatar da kudaden jama’a da ƙara kuɗin kwangila da cin hanci da rashawa, da karkatar da kudaden da suka kai N8,069,176,864.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa kudaden da ake taƙaddama a kai sun shafi kwangilolin sufurin jiragen sama guda hudu da tsohon ministan ya bai wa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakin ƙaninsa.