Sabon Karamin Ministan Tsaro na Nijeriya Mohammed Bello Matawalle ya mayar da martani ga masu cewa ba shi da kwarewar da zai iya rike babbar ma'aikata irin wannan har ya kawo ci-gaban da ake so a wajen.
Tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya fitar da ma'aikatun da ministocinsa za su yi aiki inda tsohon gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar ya zama babban Ministan Tsaro, shi kuma takwaransa na Jihar Zamfara, Matawalle ya fito a karamin minista, 'yan kasar suka dinga bayyana shakku kan ingancinsu a kan wannan babban aiki, a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da tarin matsalolin tsaro.
Sai dai a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta an ga Bello Matawalle, wanda ya yi gwamnan Zamfara - jihar da take fama da matsalolin tsaro, tsawon shekara hudu, yana yin raddi ga masu cewa ba za su iya rike ma'aikatar ba.
"Na yi ta jin bayanai ana cewa da ni da dan uwana Badaru, ba mu da capacity na zama ministoci na tsaro...wadanda ke fada ba su san ma mene ne tsaro din ba. Domin za ka iya haifar da amma sai ya fi ka kwazo da nazari da ilimi," Matawalle ya fada a cikin bidiyon.
"Ba a nan gizo ke saka ba, abu ne na idan ka yi, ka san za ka iya kuma kana da wannan karfin gwiwar da za ka yi, kuma kana da damar da za ka yi."
Jihar Zamfara da karamin Ministan Tsaron Matawalle ya fito ta yi kaurin suna wajen fama da matsalar tsaro da hare-haren inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, duk da cewa dai za a iya cewa shi ma gadar hakan ya yi.
Amma a jawabin nasa ministan ya kara da ce "Sanda ina gwamna, babu hanyar da ba mu bi ba domin dakile tsaro a Jihar Zamfara. Sai da aka yi kwana 100 ba a taba kowa ba, muka zo aka kara yin wata tara ba a taba kowa ba a Jihar Zamfara," ya ce.
"Duk matakan da nake dauka na dakile matsalar tsaro a Jihar Zamfara, sai na yi sannan wasu gwamnoni su dauka. Saboda me? Saboda ina da ilimin abin," Matawalle ya nanata.
Sai dai tun bayan nadin ministocin tsaron biyu masu sharhi ma suna tababar cewa da wuya idan an ajiye kwarya a gurbinta ne nadin mutanen biyu a matsayin masu kula da tsaron kasar.
Amma karamin ministan tsaron ya tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa ba zai ba su kunya ba a wannan tafiyar cikin yardar Ubangiji.
“Abin da zan ba ku albishir al’ummar jihar Zamfara ba zan ba ku kunya ba idan Allah ya yarda. Wannan abu da ake fadi cewa ni da dan uwana Badaru ba za mu iya ba, to masu fadin haka za su sha kunya, za su san cewa Allah ke yi ba su ba,” in ji Matawalle.
"Lokacin ta'addanci ya zo karshe"
Ya kuma umarci mahalarta taron da yake yi wa bayanin a cikin bidiyon cewa idan suka koma, to su isar da sako cewa "Lokaci na ta'addanci idan Allah Ya yarda an kai karshensa."
Fadar wannan kalami ke da wuya aka jiyo taron cikin bidiyon sun rude da sowar murna.
Matawalle ya ci gaba da cewa "Da sai dai mu nema a yi, to yanzu gare mu za a zo a nema mu je mu yi."
Ya kara nanata cewa yadda ake ganin ba za su iya ba to idan Allah Ya yarda, Allah da suke nema a wajensa zai ba su ilimin da za su iya. "Kuma shi ke iya ba da ilimin da fasahar da za ka iya.
"Ka da ka bugi gaba ka ce sai wane, shi ya sa muke shiga cikin matsaloli," ya ce.
Ya tabbatar wa al'ummar Jihar Zamfara cewa a matsayinsa na wakilinsu to ba zai ba su kunya ba, zai zama jakadansu kuma za su yi alfahari da jakadancinsa a tawagar minsitocin tarayya
A karshe ya gode wa al'ummar Jihar Zamfara da 'yan Nijeriya masu yi musu fatan alheri.