Uganda na fuskantar mamakon ruwan sama a 'yan kwanakin nan. / Hoto: Reuters

Akalla mutane 30 sun mutu bayan zaftarewar ƙasa a wani ƙauye a gabshin Uganda, a cewar wata jami'a a ranar Alhamis, tana gargaɗin cewa adadin zai iya ƙaruwa.

"Mun rasa kimanin mutane 30", kamar yadda kwamishiniyar gundumar Bulambuli Faheera Mpalanyi ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, bayan zaftarewar ƙasar a ƙauyen Masugu, inda ta ƙara da cewa, kawo yanzu an tono gawawwakin mutane shida ciki har da yaro.

"Ganin irin bala'in da girman wajen da abin ya shafa da kuma abin da iyalen da abin ya shafa suke faɗa mana, ba a ga mutane da dama ba, kuma wataƙila baraguzai sun binne su," a cewarta.

Zaftarewar ƙasar ta zo ne watanni uku bayan mutane da dama sun mutu a cikin irin wannan zaftarewar.

Ƙasar da ta zaftare ta binne gidaje 40 baki ɗaya, yayin da wasu kuma suka lalace, kamar yadda Gidan Rediyo da Talabijin na Uganda ya rawaito.

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya

Kawo yanzu, jami'an ceto na Ƙungiyar Agaji ta Red Cross Soceity sun tono gawawwaki 13, kamar yadda hukumomi da mazauna yankin da kafar watsa labaran suka bayyana.

Ofishin Firaministan Uganda ya ce ana fargabar cewa kimani gidaje 20 sun rushe baki ɗaya.

Ya kuma fitar da gargaɗi a shafin X cewa: "Mamakon ruwan sama a ranar Laraba ya haifar da bala'o'i a yankuna da dama."

Ƙasar ta Gabashin Afirka ta sha fama da mamakon ruwa sama a 'yan kwanakin nan, inda aka fuskanci ambaliya a arewa masu gabashi, bayan wani ɓangare na tekun maliya ya ɓalle, abin da ya sa jami'an agaji suka riƙa kai-kawo domin ceto mutanen da suka maƙale a cikin motoci.

TRT Afrika