Wajibi ne ƴan Liberia su zaɓi wanda a cikin ƴan takarar zai iya ba su irin Shugabancin da ya cancance su. Hoto/Getty Images

Daga Charles Mgbolu

Laberiya na tunkarar zagaye na biyu, na zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ranar 14 ga watan Nuwamba, tsakanin shugaban ƙasa mai ci, George Weah, da kuma mutum ɗaya tilo daga ƴan adawa da har yanzu yake cikin takarar, Joseph Nyumah Boakai, bayan sakamako daga zagayen farko ya nuna sun yi kankankan.

Weah, Wanda tsohon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya ne da ke tsayawa takara a karo na biyu, ya samu kashi 43.79% na ƙuri'u, yayin da abokin hamayyarsa mafi kusa a zaɓen, Boakai ɗan shekaru 78- da haihuwa, ya samu kashi 43.49 na ƙuri'un, a cewar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa.

Babu ɗaya daga cikin sauran ƴan takara 18, da ya samu sama da kashi 3%, a zagayen farko na zaɓen, a ƙasar ta Afrika ta Yamman, ranar 10 ga watan Oktoba.

Daɗaɗɗen mai tsayawa takara

Boakai, wanda sau biyu yana tsayawa takara shugaban ƙasa kuma jagora a jam'iyar Unity Party mai adawa, an san ya riƙe muƙamai na siyasa daban daban tare da nuna himma da jajircewa yayin da aka fuskanci ƙalubale.

Joseph Boakai ya sha kaye a hannun George Weah a zaɓen da ya gabata a 2017. Hoto/ Reuters

An haifi Joseph Boakai a ƙauyen Worsonga mai nisa, a gundumar Lofa ta arewacin Liberia. Shekarunsa 78 da haihuwa.

Dandalinsa na yanar Gizo ya bayyana yadda ya yi nasara a gwagwarmaya da ya yi da talauci domin ya samu ilimi.

Boakai ya kammala jami'ar Liberia a 1972 tare da takardar digiri a fannin nazarin gudanar da kasuwanci, kafin ya halarci jami'ar jihar Kansas a Amurka.

Ya tsunduma harkar siyasa ne yayin da yake riƙe da muƙamin ministan aikin gona, ƙarƙashin shugaban ƙasa Samuel Doe, daga 1983 zuwa 1985.

A ɗan wannan lokacin, Boakai ya jagoranci Ƙungiyar Bunƙasa Noman Shinkafa ta Ƙasashen Afrika ta Yamma-15.

Muƙami mafi ƙarfin faɗa a ji da ya riƙe kawo yanzu, ya samu ne a 2006, yayin da aka naɗa shi mataimakin shugaban ƙasar Liberia na 29th, ƙarƙashin shugabar ƙasa Ellen Johnson Sirleaf. Ya riƙe wannan muƙamin har zuwa 2018.

A matsayinsa na mataimakin shugabar ƙasa, ya jagoranci Majalisar Dokoki ta Liberia, sannan ya taka rawa a matsayin mai saka-ido a cibiyoyi da hukumomi dayawa, da suka haɗa da Hukumar Caca ta ƙasa ta Liberia, da Hukumar Kasuwanci ta Liberia, da Hukumar Samar Wa Al'umma Ayyukan Yi ta Liberia, da kuma Hukumar Kwance Ɗammara, da Sake Tsugunar da Jama'a ta ƙasa.

Yayin da wa'adin mulkin Sirleaf ke kawo wa ƙasashe, Boakai ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa. Ya sha kaye a hannun Weah a zaɓen 10 ga watan Oktoba, 2017.

Shugaba mai ci

Idan aka kwatanta da mai ƙalubalantarsa, hanyar da Weah ya bi ta kaiwa ga fadar shugaban ƙasa, ba ta samu gatan samun gogewa sakamakon riƙe muƙaman siyasa masu gwaɓi ba.

An haifi Weah a shekarar 1966 a Monrovia, babban birnin Laberiya, kuma ya tashi ne a Clara Town, wata unguwar marasa galihu a birnin.

Kafin tsundumarsa siyasa daga baya, ya yi wa Liberia hidima ne a matsayin shahararren tauraron ƙwallon ƙafa na duniya.

George Weah ya kasance shugaban kasar Laberiya tun 22 ga watan Janairu 2018. Hoto/AP

Weah, ɗan shekaru 57 da haihuwa, ɗan wasan gaba ne a shekaru 18 da ya kwashe a rayuwarsa ta ƙwararren ɗan ƙwallo maciyin ƙwalllaye, wacce ta kawo ƙarshe a 2003.

Ya wakilci Laberiya a matakin ƙasa da ƙasa na tsawon lokaci, ya zura mata ƙwallaye 18, sannan ya taimaka wa ƙasarsa ta yi galaba a wasanni 75.

A shekarar 1995, an sanar da shi a matsayin Gwarzon Ƙwallon ƙafa na Duniya, kuma aka ba shi kyautar yaba bajinta ta Ballon d'Or, abin da ya sa ya zama mutum na farko, kuma shi ɗaya tilo daga Laberiya, da ya taɓa lashe waɗannan kyaututtukan.

A shekarun 1989, da 1994 da kuma 1995 an sanar da sunansa a matsayin Gwarzon Ƙwallon ƙafa na Afrika, a shekarar 1996 kuma, aka naɗa shi Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na Shekaru Ɗari.

Biyo bayan hamɓarar da shugaban ƙasa Charles Taylor a 2003, Weah ya dawo Laberiya a matsayin jakadan fatan alheri na Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2005, ya tsaya takarar shugaban ƙasa a matsayin ɗan jam'iyar Congress For Democratic Change.

Bayan ya tsallake zagaye na ɗaya, Sirleaf ta jam'iyar Unity Party ta kayar da shi a zaɓen zagaye na biyu na watan Nuwambar shekara 2005.

Weah ya ƙara fuskantar Sirleaf a zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba shekarar 2011, amma wannan karo a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da ɗan takarar shugaban ƙasa Winston Tubman.

Tubman daga bisani, ya janye daga takarar ana daf da gudanar da zaɓen zagaye na biyun, yana zargin an tafka maguɗin zaɓe.

A watan Disamba 2014, Weah ya tsaya takarar kujerar ɗan majalisar dokokin na gundumar Montserrado, wadda ya lashe.

Shekaru biyu tsakani, Weah ya haɗe jam'iyarsa tare da wasu jam'iyyu suka kafa jam'iyyar Coalition for Democratic Change domin ƙarfafa ƴan adawa gabannin zaɓen.

Zagaye na biyu

Zagayen farko na zaɓen wannan shekarar bai samar da wanda ke kan gaba ƙarara ba, abin da ke nuna kowa na iya lashewa, da yiwuwar a yi ƙeƙe da ƙeƙe a ƙarshen zaɓen zagaye na biyun.

Rashin samun wanda ya yi nasara kai tsaye na nuni da damuwa da masu kaɗa ƙuri'a ke ciki game da halin da tattalin arziƙi ke ciki, abin da Weah ya tabbatar, ta hanyar roƙon da yake ta nanatawa a yaƙin neman zaɓe, na cewa, a ba gwamnatinsa ƙarin lokaci domin ta cika alƙawarin da ta yi wa mutane.

Ƴan Laberiya suna fama da ɗimbin matsalolin tattalin arziƙi. Hoto/Reuters

"Bari na tabbatar muku cewa, yanayin da ƙasa ke ciki yana da kyau. Yanayin da ƙasarmu ke ciki na daidaito ne.

Yanayin da ƙasarmu ke ciki na kwanciyar hankali da tsaro ne. Mun ƙuduri aniyar dawwamar da ita a irin wannan halin," ya ce.

Boakai, a ɗaya ɓangaren, yana cewa, shekarunsa da gogewarsa a harkar gudanar da gwamnati, sune tagomashinsa.

Ya gaya wa masu kaɗa ƙuri'a cewa, waɗannan siffofin su za su zama masa linzami wajen yanke shawara, yayin da ya tunkari matsalolin da yanzu suka addabi ƙasar.

"Abin da na sani sosai shi ne cewa, duk baiwa da tunani da muke buƙata wajen sake gina ƙasarmu ba za a same su a cikin jam'iya, ko ƙabila, ko gunduma, ko yanki, ko addini ɗaya ba.

Shi ya sa na ƙuduri aniyar kafa gwamnatin tafiya tare da kowa," ya ce. Ranar yanke hukunci na ƙarato wa ƴan Laberiya yayin da suke shirya wa aiki mai ƙalubalen yanke hukuncin waye a cikin mutane biyun zai iya ba su Shugabancin da ya cancance su.

TRT Afrika