Daga Hamisi Salim
Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo tana gudanar da zaɓuɓɓukanta na shugaban ƙasa da na ƴan majalisa ranar Laraba.
An saka ido sosai a kan zaɓuɓɓukan a naniyar, yayin da ƙasar ke neman ƙarfafa mulkinta na Dimokuraɗiyya.
Za su kasance zaɓuɓɓuka na farko tun lokacin da aka miƙa mulki cikin lumana daga shugaban ƙasa Joseph Kabila zuwa shugaban ƙasa mai ci Felix Tshisekedi a 2018.
Ƙasar Afirka mafi girma idan aka yi la'akari da faɗin ƙasa tana fama da ƙazamin rikici a yankin gabashi da kuma matsalar tattalin arziƙi duk da ɗimbin arziƙin ma'adananta.
Fiye da mutane miliyan Shida ne rikicin ya raba da muhallansu a yankin gabashin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Waɗanda suke zaune a sansanonin ƴan gudun hijira ba za su yi zaɓe ba, saboda ba a yi musu rigista a matsayin masu zaɓe a inda suke ba.
Shugaban ƙasa Tshisekedi na ɗaya daga cikin ƴan takara fiye da 20 da suke neman shugabancin ƙasar a zaɓen.
Shin 'yan adawa za su iya ba da mamaki?
Tshisekedi da jam'iyarsa ta UDPS na fuskantar hamayya mai zafi daga abokan adawa waɗanda suka gudanar da yaƙin neman zaɓensu a kan taken canji.
Tsohon firaminista Martin Fayulu, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata a 2018, yana daga cikin manyan abokan hamayyar Tshisekedi.
Ɗan kasuwa Moise Katumbi, wanda ya mallaki ƙungiyar ƙwallon ƙafar da ta fi kowacce samun nasara a ƙasar, yana tunƙaho da gogewarsa a harkar shugabanci a matsayinsa na tsohon gwamnan lardin Katanga da ya samu cigaba wajen samar da kayayyakin more rayuwa a yankin.
Denis Mukwege, likitan mata mai aikin fiɗa kuma wanda ya taɓa lashe kyautar zaman lafiya, shi ma yana ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasar. Ya gaya wa magoya bayansa cewa lokaci na ƙurewa da za a ceto Dimokuraɗiyyar Kongo.
Amma gazawar ƴan adawa su fitar da ɗan takara ɗaya tal da zai fuskanci Tshisekedi ya sa zaɓen ya zama na sai mai rabo. Wani shirin da za a ƙulla ƙawancen ƴan adawa ya watse tun da farko a wannan shekarar, bayan tattaunawar ta kasa cim ma matsaya.
Mata, matasa da kuma zaɓen
Mace ɗaya tilo a takarar shugabancin ƙasar, Marie Josee Ifoku, ƴar Shekaru 58 da haihuwa, tana neman shugabancin ƙasar a karo na biyu kenan.
Ifoku, wacce aka kuma sani da mata mai tsintsiya, ta bayyana ƙarara cewa ilmin da ta samu a zaɓen da ya gabata ya sa ta shirya wa aikin da ke gaba.
Matasa na cewa duk da suna sane da ɗimbin dukiyar ƙasarsu, amma matakin da rashin aikin yi da talauci suka kai yana firgita su.
"Idan muka zaɓi mutanen kirki, rayuwarmu za ta inganta. A ɗaya ɓangaren kuma, idan muka zaɓi lalatattu, sauye sauyen da za a samu marasa kyau ne," ɗan fafutikar kare haƙƙin bil adama, Natalie Maliva ya gaya wa TRT Afrika.
Farfaɗowar ƙungiyoyin ƴan tawaye
Sake dawowar aikace-aikacen ƴan tawaye a gabashin ƙasar ya haifar da kashe kashe dayawa da kuma raba ɗaruruwan dabbanin mutane da muhallansu.
A matsayin wani martani kan tayar da ƙayar bayan, Ƙungiyar Ƙasashen Gabashin Afrika, da ta ƙunshi ƙasashe Bakwai ta tura tawagar sojoji a watan Nuwamba 2022 da hadafin maido da zaman lafiya a yankin.
Amma an janye tawagar sojojin yayin da wa'adita ya ƙare ranar 8 ga watan Disamba, sakamakon rashin gamsuwa da tasirinta.
Majalisar Dinkin Duniya ita ma ta fara janye dakarun kiyaye zaman lafiyarta da aka tura yankin a 1999.
Hakan ya biyo bayan jerin munanan zanga-zanga da aka gudanar a kan dakarun, waɗanda mutanen yankin suka zarga da gaza daƙile tashin hankalin da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai masu yawa suke haddasawa.
Kayan aiki
Yan adawa sun buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta (CENI) ta gudanar da zaɓuɓɓuka cikin walwala da adalci kuma karɓaɓɓu. Kuma sun yi nuni da zargin yin ba daidai ba wajen gudanar da aikin rigistar masu zaɓe da kuma rashin ingancin katin zaɓe, inda wasu ke koɗewa kafin ranar zaɓen ma.
Zunzurutun faɗin da ƙasar ke da shi na nufin babban ƙalubalen kayan aiki wajen gudanar da zaɓuɓɓukan. Hukumar zaɓen CENI ta ce an rarraba kayayyakin zaɓe zuwa rumfunan zaɓe a faɗin lardunan ƙasar 26.
Hukumar ta yi gargaɗi game da taruwar jama'a waje ɗaya, da hayaniya da kuma kamfei ranar zaɓen, sannan ta buƙaci masu kaɗa ƙuri'a su koma gida bayan sun kaɗa ƙuri'unsu.
Duk da ƙalubalen tsaro masu yawa, masu zaɓe dadama, sun bayyana aniyarsu ta yin zaɓe tare da fatan a shi cikin kwanciyar hankali kuma karɓaɓɓe da kuma makoma mai kyau ga ƙasar.