Kotun Kolin Nijeriya ta ce ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, za ta yanke hukunci kan karar da 'yan takarar shugabancin kasar na Jam'iyyar PDP da Labour Party suka shigar a gabanta suna kalubalantar zaben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu.
Daraktan Watsa Labarai na Kotun Kolin Festus Akande ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba.
Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP suna neman Kotun Kolin ta soke zaben Bola Tinubu wanda kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da nasararsa a matsayin shugaban kasa a zaben 2023.
Mutanen biyu suna so Kotun Koli ta soke zaben Tinubu ne bisa zargin cewa an tafka magudi.
Labari mai alaka: Matakai hudu da suka rage wa Atiku da Obi bayan hukuncin kotu kan zaben Tinubu
Kazalika sun dage cewa Shugaba Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba, kuma bai samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaben da aka gudanar a Nijeriya ba.
Atiku Abubakar ya gaya wa Kotun Kolin cewa takardun kammala Jami'ar Chicago State University da Shugaba Tinubu ya mika wa hukumar zaben Nijeriya, INEC, don tsayawa takara na jabu ne.
A watan Fabrairu aka gudanar da zaben shugaban kasar kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara inda samu kuri'a 8,794,726 -- wato kashi 37 na kuri'un da aka kada.
INEC ta ce Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne yake biye masa da kuri'a 6,984,520 -- kashi 29, yayin da dan takarar Jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu kuri'a 6,101,533 -- kashi 25.