Janar Abdourahamane Tchiani ya gargadi kasashen duniya kada su sanya baki a sha'anin Nijar./HotoRTN

Daga Abdulwasiu Hassan

A wannan mako ne sojoji suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, abin ya fara ne bayan dakarun da ke tsaron fadar Shugaba Mohamed Bazoum sun tsare shi – abin da ya sa fargaba a zukatan jama'a kan yadda juyin mulki ke neman dawo a nahiyar Afirka.

Ko da yake kifar da gwamnati yana neman zama tarihi, sai dai abubuwa da yawa sun faru a nahiyar a shekaru uku da suka wuce da ke nuni da dawowar hakan.

Tsakanin shekarar 2020 zuwa yanzu, an samu juyin mulki ko yunkurin juyin mulki akalla 10.

Kasashen da abin ya shafa sun hada da Sudan da Chadi da Burkina Faso da Mali da Guinea da Guinea-Bissau da kuma yanzu a Nijar.

Shugaban dakarun fadar shugaban kasar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana a talabijin a ranar Juma'a a matsayin sabon shugaban kasar bayan juyin mulkin ranar Laraba.

Me ya sa sojoji ke yin juyin mulkin?

Dalilin da ya sa sojoji ke karbe iko yawancin ba ya wuce batun cewa gwamnati ta kasa sauke nauyin da ke wuyanta. Sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda "ci gaba da tabarbarewar tsaro da zamantakewa da kuma tattalin arziki."

Wannan dalilin ya yi kama da dalilin da sojoji suka bayar na yin juyin mulkin watan Agustan shekarar 2020 wanda ya kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Ibrahim Boubacar Keita a Mali.

Su ma wadanda suka hambarar da gwamnatin tsohon Shugaba Alpha Conde na Guinea a 2021 sun bayar da irin wannan dalili ne.

Tsakanin shekarar 2020 zuwa yanzu, an samu juyin mulki ko yunkurin juyin mulki akalla 10 ciki har da Mali makwabciyar Nijar.

"Idan ka dubi halin da hanyoyinmu suke ciki da asibitocinmu, to za ka ga lokaci ya yi da ya kamata mu farka," in ji Kanal Mamady Doumbouya wanda ya kifar da gwamnatin Conde.

Tsarin dimokradiyya, kamar yadda masana kimiyyar siyasa da kuma masu fafutika, ya yi Allah-wadai da wadanda suke da hannu a hambarar da gwamnati.

"A baya a shekarun 1960 zuwa 1980, babban dalilin da masu kitsa juyin mulki shi ne rashin daidaito a siyasance da kuma magudin zabe," in ji Dokta Aminu Hayatu na sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero ta Kano a Nijeriya.

"A kwanakin nan ba sa magana kan magudin zabe. Sai dai suna magana ne kan tsadar rayuwa da matsalolin da mutane ke fama da su."

Dokta Hayatu ya ce hatta wadanda suke da hannu a juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ba su danganta aikinsu da matsalar magudin zabe ko kuma wata matsala ta siyasa mai kama da haka.

Manyan matsalolin da za su biyo baya

Masana suna ganin dawowar juyin mulki a Afirka a matsayin wani koma baya da zai mayar da nahiyar baya sosai.

"A matsayinmu na wani yanki dawowar juyin mulki ya mayar da mu baya daga inda muke a 'yan shekarun da suka wuce," in ji Idayat Hassan, wacce babbar jami'a ce a cibiyar tsare-tsare da nazari kan harkokin kasashen duniya wato Centre for Strategic and International Studies.

Masana sun yi amannar cewa juyin mulki ba hanya ce ta warware matsalolinsu tattalin arziki ba. "Matsin rayuwar da mutane suke tserewa zai dawo saboda wadanda suka kitsa juyin mulkin ba su da kwarewa gyara matsalolin ci gaba rayuwa," in ji Dokta Hayatu.

"Idan wannan abin ya ci gaba da faruwa a kasashen Afirka, za a ci gaba da samun wanzuwar matsalolin take hakkin dan Adam," kamar yadda ya yi gargadi.

Kamar yadda Dokta Hayatu ya ce dimokradiyya tana tafiya kafada da kafada da ra'ayin jama'a da wakilcin jama'a da kuma yi wa jama'a aiki.

"Kuma aka bar mulki a hannun wasu 'yan tsirarun sojoji, ka san tun da ba zabensu aka yi ba, za su yi abin da suka ga dama ne kawai," in ji shi.

Yadda za a magance matsalar

Bayan kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da dakatar da yiwuwar samun juyin mulki a yankin, masana suna ganin Afirka tana bukatar ta tabbatar da dorewar tsarin dimokradiyya don samun nasara.

"Ana samun lokacin da 'yan kasa daina kare dimokradiyya, suka daina karfafa ta, to gaba daya tana cikin hadari," kamar yadda Idayat Hassan ta shaida wa TRT Afrika.

Janar Tchiani wanda shi ne kwamandan rundunar sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa a yanzu ya ayyana kansa a matsayin shugaban Nijar. Hoto: Reuters

"Ya kamata mu wayar da kan 'yan kasa su fahimci muhimmancin dimokradiyya kansu. Ya dace dimokradiyya ta koma hannun 'yan kasa – wadanda za su iya kare dimokradiyyarmu," in ji ta.

Wasu sun bukaci manyan 'yan siyasa da su rika yin bincike don gano ainihin dalilin da ya sa aka yi kowane juyin mulki. Hakan yana nufin daukar matakin dakile wata matsala da sojoji za su iya fakewa da ita wajen yin juyin mulki.

Dokta Idayat ta bukaci 'yan siyasa da su dauki darasi kan yadda juyin mulki ya dawo a nahiyar Afirka.

"Wasu abubuwa da suka haifar da dalilin juyin mulkin, kamar yadda sojojin suka yi korafi, akwai kamshin gaskiya a cikinsu," in ji Dokta Hayatu.

"Ya kamata 'yan siyasa sun fahimci damuwar mutane. Idan mutane ba su da wadannan korafe-korafe, yana da wuya juyin mulkin ya yi nasara."

TRT Afrika