'Yan sandan Nijeriya ta ce an gano makamai da dama da katunan cirar kudi a hannun mutanen./Hoto: Rundunar 'yan sandan Nijeriya

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta kama mutum uku da ke cikin wani gungun masu dauke da bindigogi da ya kai hare-hare a jihar Filato a jajibirin Kirsimeti wadanda suka yi sanadin mutuwar akalla mutum 200.

A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata da maraice, ya ce mutanen na cikin mutum 67 da suka kama bisa zargin aikata laifuka daban-daban a fadin kasar.

“Mutanen da ake zargin su ne Ahmed Sulaimon da Balikisu Aliyu da Aboki Samuel. Bayan an kama su, an gano makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda daya da kirar AK-49 guda daya da harsasai 1000 da kwanson harsasai biyar,” in ji Adejobi.

Ya kara da cewa “a halin da ake ciki mutanen suna tsare a hannun ‘yan sanda kuma suna taimakawa wurin bincike.

Wasu ‘yan bindiga ne suka kaddamar da jerin hare-hare a kauyuka kusan ashirin a jihar ta Filato a jajibirin Kirsimeti.

Tun da fari, hukumomi sun ce mutum 163 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos.

Sai dai yayin da mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya kai ziyara a jihar ta Filato, shugaban karamar hukumar Bokkos Monday Kassah ya ce mutum 148 aka kashe a yankinsa.

Kazalika an kashe mutum akalla 50 a kauyuka daban-daban na karamar hukumar Barkin Ladi, a cewar Dickson Chollom, wani dan majalisar dokokin jihar daga yankin.

"Muna rokonku da ku guji raba kawuna da kiyayya ga junanku, a yayin da muke kokarin ganin an yi adalci domin samar da zaman lafiya," in ji Kashim Shettima a yayin da ya gana da jami’an gwamnati da sarakuna da kuma mazauna yankunan.

‘Sauran masu aikata laifuka’

Olumuyiwa Adejobi ya kara da cewa “a yunkurin” rundunar ‘yan sanda na “kakkabe aikata laifuka a fadin kasar nan, sashen leken asiri da dabaru” ya yi nasarar kama mutum “67 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da sayar da makamai, da fashi da makami.”

“Kazalika ‘yan sanda sun kwace harsasai 5,454 da kwanson harsasai 300 da kananan bindigogi 68 da katin cirar kudi na ATM 33 da sauransu,” in ji kakakin ‘yan sanda.

TRT Afrika