Ko a bara sai da aka kashe Deborah Samuel kan zargin batanci ga Annabi a Sokoto. Hoto/AP

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Sokoto ta ce ta kaddamar da bincike kan kashe wani mahauci wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda yara da manya suka rinka yi wa mahaucin ruwan duwatsu har ya galabaita.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Sokoto ASP Ahmad Rufa’i ya tabbatar wa TRT Afrika cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a mahautar birnin na Sokoto.

“A ranar 25 ga watan Yuni da misalin 09:55 na safe, an samu kiran gaggawa kan cewa wani Usman Buda daga Karamar Hukumar Gwandu wanda mahauci ne a mahautar Sokoto ana zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

“Sakamakon haka fusatattun matasa Musulmai suka far masa tare da ji masa rauni mai tsanani,” in ji ASP Rufa’i.

A cewarsa, bayan samun wannan bayani sai jami’ansu suka yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ke faruwa.

“Ko da suka isa, fusatattun matasan sun tsere sa’annan wanda aka ji wa raunin bai san inda kansa yake ba inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Usmanu Danfodio Sokoto domin duba lafiyarsa,” in ji ASP Rufa’i.

Ya bayyana cewa ko da aka isa da shi asibitin daga baya sai aka tabbatar da cewa ya rasu.

“Kwamishinan ‘yan sandan Sokoto CP Ali Hayatu Kaigama na kira ga jama’a da su ci gaba da hidimominsu bisa doka ba tare da fargaba ba sakamakon an shawo kan lamarin. A halin yanzu ana ci gaba da bincike domin kamawa da kuma daukar mataki kan masu hannu a lamarin,” in ji ASP Rufa’i.

Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan lamari ba a Sokoto. Ko a bara sai da fusatattun matasa suka kashe wata daliba a Sokoto Deborah Samuel tare da kona gawarta kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

TRT Afrika