Kazalika rundunar 'yan sandan ta Nijeriya ta ce dakarunta na sirri sun dakile wani yunkuri na yin garkuwa da mutane./Hoto:Rundunar 'yan sandan Nijeriya

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kama wasu masu aikata laifuka a Abuja, ciki har da gawurtattun masu garkuwa da mutane.

Rundunar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Asabar da maraice.

Kakakin rundunar ta 'yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya gabatar wa manema labarai mutum 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ya ce sun kama makamai da dama ciki har da mashingan.

"A cikin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da aka gabatar da su a yau akwai mutum uku da ke zaune a yankin Bwari - Idris Ishaku da Bala Umar da Dahiru Salisu, kowanensu dan shekara 27. Su ne suka yi jerin fashi da makami da satar jama'a a Karamar Hukumar Bwari da sauran sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja," in ji Adejobi.

Ya kara da cewar dakarun nasu sun kuma kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin na Nijeriya.

Labarai masu alaka:

Kazalika rundunar 'yan sandan ta Nijeriya ta ce dakarunta na sirri sun dakile wani yunkuri na yin garkuwa da mutane lamarin ne me ya kai ga kama gawurtattun masu satar mutanen a Bwari da makamansu.

Ta ce ma'aikatanta sun kama wani mutum mai suna Everest Magaji, wanda yake sayar da makamai da yin garkuwa da mutane yayin da yake kokarin karbar kudin fansa, tana mai cewa wasu abokansa da ke da hannu a lamarin sun tsere. Sai dai ta ce an kwace makamai daga wurinsu.

TRT Afrika