Gamayyar kungiyoyin hamayya da masu zaman kansu da ba sa dauke da makamai a Chadi ranar Laraba ta yi kira ga shugaban kasar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya gaji mulki bayan mutuwar mahaifinsa a 2021, ya janye daga tsayawa takara a zaben wannan shekarar.
Gammayar mai suna Wakit Tamma ta zargi kasashen duniya, musamman Faransa, da goyon bayan “mulkin gado” a Chadi da kuma mara wa Janar Mahamat Deby baya a “shirinsa na kwace mulki, ciki har da amfani da karfin soja”.
An nada Mahamat mai shekara 37 a matsayin shugaban kasa shekaru biyu da suka wuce bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno a wani gumurzu da suka yi da ‘yan tawaye a fagen yaki. Ya kwashe fiye da shekara talatin yana mulki.
Kasashen duniya sun yi kira ga dansa ya gudanar da zabe cikin watanni 18 kamar yadda ya yi alkawari.
Sai dai ya kara shekaru biyu a kan alkawarin da ya yi na mika mulki ga farar-hula.
Babbar jam’iyyar adawa ta kasar wadda kuma ita ce kungiya mafi girma da ke rike da makamai ta kaurace wa wani shirin tattauawa na kasa da aka gudanar.
Wakit Tamma ta fitar da sanarwa ranar Laraba da ke kira ga Janar Deby da kada ya tsaya takara a zaben da ke tafe domin ya zama "mai kishin kasa".
Ta zargi Faransa da "yin katsalandan a harkokin kasar nan... a yunkurin na kara karfi a yankin Sahel".