'Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike kan wannan hari. Hoto/Nigeria Police Force

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa ‘yan fashi da makami sun kashe DPO da wasu ‘yan sanda uku a Jihar Benue.

‘Yan fashin sun kashe ‘yan sandan ne a yayin da bangarorin biyu ke musayar wuta a lokacin da ‘yan fashin suka kai hari wasu bankuna a jihar.

A sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Benue SP Catherine Anene ta fitar, ‘yan fashin sun kai harin ne bankunan Access da First da Zenith da UBA da Stanbic a Otukpo da ke Jihar Benue.

Catherine ta bayyana cewa ‘yan sandan na Otukpo sun yi kokarin dakile ‘yan fashin, sai dai ba su samu nasarar hakan ba.

“‘Yan fashin wadanda aka yi arangama da su kan hanyar Otukpo-Taraku, sun yi musayar wuta da ‘yan sanda, an kashe ‘yan fashin biyu. Sauran ‘yan fashin sun bar motocinsu suka gudu cikin daji, inda ‘yan sanda suka bin su.

“DPO din ‘yan sanda wanda ya samu rauni a cikinsa da sauran ‘yan sanda uku an tabbatar sun rasu a asibiti. Sauran mutanen da suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga a bankin an tafi da su asibiti,” in ji Catherine.

TRT Afrika