Aƙalla mata 35 masu satar mutane suka tafi da su a lokacin da suke komawa gida daga wajen biki, a arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda jami'ai suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Litinin.
Wannan satar mutane da ta faru a Jihar Katsina ita ce mafi girma da aka yi a baya-bayan nan a ƙasar, wacce ita ce mafi yawan al'umma a Afirka.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Abubakar Aliyu, ya ce "wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi kwanton ɓauna tare da sace kusa mata 35" da ke komawa gida bayan kammala taron biki a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da daddare, amma sai yanzu ne bayanai suke fitowa.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Nasiru Muaz ya ce mutanen da aka sace sun fi haka, inda ya ce fiye da mutum 50 ƴan bindigar suka sace, waɗanda ke komawa ƙauyen Damari bayan kai amarya gidan mijinta.
"Jami'ai sun ziyarci ƙauyen kuma an gaya musu cewa mutum 53 aka sace," in ji shi.
"Akwai haɗari sosai a ce motocin ƴan ɗaukar amarya sun bi hanyar da ta yi ƙaurin suna wajen satar mutane kuma da daddare.
"Ƴan bindigar sun yi amfani da wannan damar suka sace mutanen," ya fada.
Kwamishinan ya nemi mazauna yankin da su guji yin tafiya cikin dare yana mai cewa jami'an tsaro na ƙoƙarin gano da kuma ceto waɗanda aka sace ɗin.
Satar mutane don neman kudin fansa babbar matsala ce a Nijeriya, inda gungun masu aikata laifuka ke kai wa manyan tituna hari, da gidajen mutane, har ma da sace yara a makarantu.
Ƴan bindigar kan ɓuya a dazuzzuka da ke jihohin yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ne don aiwatar da ayyukansu.
A farkon shekarar nan, ƴan bindiga sun sace wasu ƴan mata biyar ƴan'uwan juna a Bwari da ke birnin tarayyar Nijeriya, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu saboda gaza biyan kuɗin fansa a lokacin da suka sanya, lamarin da ya tayar da hankula a ƙasar.
A makon da ya wuce ma mahara sun kai hari kan wata motar makaranta tare da sace yara biyar da wasu malamansu a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Nijeriya.
Kazalika an sace wasu sarakunan gargajiya a wani harin daban a Ekitin ranar Litinin ɗin makon jiya, sannan kuma ƴa n bindiga sun kuma harbe wani sarkin da sace matarsa a Jihar Kwara a ranar Alhamis.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro bayan da ya karbi mulki a bara.
Kasar na fama da matsalar tsaro da 'yan bindiga da kuma rikicin ƙabilanci a wasu sassan.