Sojojin Nijeriya sun dade suna fatattakar 'yan bindiga daga yanki amma lamarin na ci gaba da faruwa./hoto: Reuters

Akalla mutum shida ne suka mutu sannan aka yi garkuwa da mutum 40 a harin da wasu 'yan bindiga suka kai a Karamar Hukumar Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna a Nijeriya.

Ganau sun ce mutanen manoma ne kuma cikinsu har da Mataimakin Shugaban Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunnah na Karamar Hukumar Birnin-Gwari, Malam Yakubu Muhammad Bugai.

Shugaban wata kungiya a yankin mai suna Birnin-Gwari Emirate Progressives Union (BEPU), Ishaq Usman Kasai, a wata sanarwa da ya fitar ya ce hare-haren sun faru ne tsakanin ranar Laraba da Alhamis da suka gabata amma har yanzu babu duriyar wadanda aka sace.

Ya kuma ce akwai wasu manoma 40 da aka yi garkuwa da su a wani hari na daban.

A cewarsa an harbi jagoran kungiyar Izalan ne a ciki yayin da yake gona a kusa da garin Rema kuma daga bisani aka garzaya da shi asibiti inda rai ya yi halinsa.

Shugaban kungiyar BEPU ya ce maharan sun sace wasu mutane a kewayen dajin Kuyambana wanda ya kasance maboyar 'yan bindigar.

Mun tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna DSP Mohammed Jalige kan al'amarin, sai dai ya bukaci mu ba shi lokaci ya yi bincike sannan ya kira mu.

Ko da yake har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai tuntube mu ba.

Kazalika kakakin gwamnan jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu ya shaida wa TRT Afrika cewa ba zai iya "gaskata ko musanta faruwar al'amarin ba saboda ban samu karin bayani a hukumance ba."

Haka kuma maharan sun kai hari kauyen Unguwar Danfulani, inda suka kashe wani mutum daya suka kuma sace mutum bakwai 'yan gida daya.

Daga nan 'yan bindigar sun sace mutum shida a yankin yammacin Birnin-Gwari.

TRT Afrika da abokan hulda