'Yan bindiga sun kashe mutum 11 ranar Laraba a wani wurin haƙar ma'adinai a jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya.
'Yan bindigar da ke kan babura sun kai harin ne a yankin ƙaramar hukumar Anka, kamar yadda kafofin watsa labai da hukumomi suka tabbatar.
Kazalika gomman mutane sun jikkata.
Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-hare na ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya irin su Boko Haram da ISWAP da kuma masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa
Garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa na ci gaba da yin ƙamari duk kuwa hukuncin kisa da gwamnati ta ce za ta riƙa yi waɗanda aka samu da hannu a yinta.
'Yan bindiga na yawan kai hare-hare a ƙauyuka da makarantu da matafiya a Arewacin Nijeriya, inda suke neman a biya su kuɗin fansa.
Zamfara ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga da ke da alaƙa da ƙungiyoyin 'yan ta'adda.
A watan Fabrairu, 'yan bindiga sun kashe mutum huɗu da ke hannunsu, ciki har da 'yan sanda biyu, sannan suka yi garkuwa da mutum 40 a wani hari da suka kai a jihar ta Zamfara, a cewar 'yan sanda.
'Yan bindigar suna da sansanoni a dazukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, da Neja, inda suke kai mutanen da suka sace, ciki har da ɗalibai daga makarantu.