Gawarwaki sun watsu a titunan Yammacin Darfur a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF ya tilasta wa fiye da mutum miliyan biyu da rabi arcewa daga gidajensu.
Wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana uku da za ta kare ranar Larabar nan ta sa an samu saukin bata-kashi tsakanin bangarorin biyu a Khartoum, babban birnin kasar.
Yakin ya barke ne tsakaninn janar-janar biyu - Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojojin kasar da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, shugaban dakarun RSF ranar 15 ga watan Afrilu.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 2,000, a cewar kungiyar the Armed Conflict Location and Event Data Project da ke tattara bayanai game da yakin.
Adadin mutanen da yakin ya raba da muhallansu ya zarta miliyan biyu da rabi, ciki har da mutum 550,000 da suka tsere zuwa kasashen waje, a cewar Hukumar Kula da Masu Kaura ta Duniya, IOM, a takaice.
Filippo Grandi, shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, ya roki makwabtan Sudan da su bar kofofinsu a bude duk da damuwa game da tsaro da hakan ka iya haifarwa.
"Ina kira ga dukkan makwabtan kasashe cewa na fahimci damuwarku game da tsaro, amma don Allah bu bar iyakokinku a bude domin kuwa wadannan mutane suna gudu ne domin tsira da rayuwarsu," in ji shi a wata hira da aka yi da shi.
Ma'aikatar wajen Amurka ta ce a El Geneina, babban birnin Yammacin Darfur kadai an kashe kusan mutum 1,100.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an aikata "laifukan yaki da na keta mutuncin dan adam" a Darfur, inda rikicin "ya dauki salon kabilanci", a wata sanarwa da ta fitar tare da kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kungiyar kasashen Gabashin Afirka IGAD.
Ana ci gaba da ganin gawarwaki a yashe a titunan El Geneina, inda rikicin da aka kwashe watanni ana yi ya ya aka rufe shaguna sakamakon masu kwasar "ganima".
An hango wata gawa yashe an rufe ta da kasa a kusa da motar yaki. Kazalika an ga gawar wani mutum a kofar gidansa a nannade. Sannan an gano wasu karin gawarwakin sun yi ruf-da-ciki a tituna da dama.