Kwamandan Rundunar RSF ta Sudan Mohamed Hamdan Daglo ya ce bangarensa ya amince ya tsagaita wuta na tsawon sa’a 24 a yakin da ake fafatawa tsakaninsa da gwamnatin mulkin sojan kasar.
Janar Daglo ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, yana cewa matakin na zuwa ne bayan da "Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya tuntube shi."
“Biyo bayan tattaunawa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da sauran kasashe kawayenmu da suka nemi a tsagaita wuta na wucin gadi, RSF ta tabbatar da cewa za ta tsagaita wuta har tsawon sa’a 24 don a tabbatar da an bar fararen hula sun fice salin alin da kuma kwashe wadanda suka jikkata,” in ji janar din.
Sai dai gwamnatin mulkin sojin Sudan din ta yi watsi da ikirarin RSF na cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, inda ta kira hakan da “farfaganda.”
“Ba mu da labarin kowace irin yarjejeniya da masu shiga tsakani na kasashen waje, ‘yan tawayen sun ayyana yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’a 24 ne don kauce wa jin kunyar nasarar da suka ga za a samu a kansu cikin ‘yan sa’o’i masu zuwa,” kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Sudan ya wallafa a shafinsu na Twitter.
“Mun shiga wani mataki mafi muhimmanci kuma mun mayar da hankali kan kokarinmu na kai wa gaci,” in ji sanarwar.
Rundunar RSF ta “bayyana rashin jin dadinta” kan kin amincewa da tsagaita wutar da Rundunar Sojin Sudan din ta yi.
“Suna ci gaba da kai harin bam kan yankunan da ke da cunkoson jama tare da jawo asarar rayuka, Wannan aikin keta dokokin kasa da kasa ne da kuma dokar jin kai,” in RSF.
Janar Daglo ya kara da cewa a yanzu bangarensa zai jira tattaunawar da za su sake yi da Mr Blinken kan yadda za a warware batun keta dokokin da ake yi.