Matasan na son ba da gudunmowarsu wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano. Hoto: Kano Poilce

Wasu fitatun masu amfani da Tiktok a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriy sun kai wa rundunar ‘yan sandan jihar ziyara inda suka ce a shirye suke su hada kai da jami'an tsaron don kawo gyara da zaman lafiya a jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matasan sun kai ziyarar ne a ranar Laraba ga kwamishina don bai wa rundunar ‘yan sanda gudunmowarsu da yunkurinsu na ganin cewa ta basirar da suke da ita sun taimaka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.

Cikin wadanda suka kai ziyarar neman yin aiki tare da rundunar ‘yansanda har da matashin nan Mubarak Isa Muhammad wanda wata kotun majistare ta taba tsare shi da abokin burminsa Nazifi Muhammad Bala bayan samun su da laifin bata sunan tsohon gwamna jihar Abdullahi Umar Ganduje.

A bidiyon da rundunar ‘yan sandan ta wallafa, an ga matasa shida zaune a kujeru tare da SP Kiyawa, inda aka bai wa kowanne damar yin bayani kan dalilan da suke so su hada kai da ‘yan sanda don kawo gyara.

Mubarak Isa Muhammad

Mubarak Isa wanda shi ne ya fara Magana, ya ce yana jan hankalin matasa da sauran mutane da su guji zagin manyan mutane ko bata musu suna a soshiyal midiya, “kamar yadda ni ma na taba yi a baya, a yanzu ina da na sani kuma b azan kara ba in-shaa-Allahu.”

Ali Nuruddin Badoo

Shi ma Ali Nuruddin da aka fi sani da Badoo ya ce yana jan hankalin al’umma musamman matasa da ‘yan mata da su daina yaudara. “Ku guji yaudara, ni ma na daina yaudara don haka ku ma ku daina,” ya fada inda ya kammala da tafa hannayensa.

Idris Mai Wushirya

A nasa sakon, Idris Mai Wushirya ya gargadi matasa ne da su guji yin kalaman batsa ko yada wasu abubuwa na batsa, “kamar dai yadda ya faru da ni.

A bidiyon da rundunar ‘yan sandan ta wallafa, an ga matasa shida zaune a kujeru tare da SP Kiyawa. Hoto: Kano Poilce

“Don haka ina shawartar al’umma da ku daina yada kalaman batsa ko yin shigar batsa, musamman ma mata har da mazan ma. To ku kiyaye domin samun zaman lafiya a gare ku da al’umma baki daya,” ya ce.

Sharfaddin Bature

Sharfaddin Bature ya ce “kamar yadda kuka sani aikinmu dama shi ne ganin yadda matasanmu na arewa za su ci gaba da kuma yadda za a samu zaman lafiya a wannan yanki namu.

Shawarata ga matasa ‘yan mata da ma iyaye shi ne a saka ido sosai wajen amfani da soshiyal midiya da kuma yadda za a ci amfanin kafar ba tare da asarar data da asarar lokaci ba da za a dawo ana da na sani.

Muhammad Ibrahim Khalil

Muhammad Ibrahim Khalil da aka fi sani da Magajin Malam ya ce yana kira ga ‘yan uwansa matasa musamman masu dora hotunan wani ko wata soshiyal midiya, a zage su a ci mutuncinsu, ko a musu kazafi saboda wani sabani da aka samu.

“Sai daga baya idan ka tsinci kanka a wajen hukuma ka fito kana ba da hakuri, to don haka nake son jan hankali, maganin kar a yi kar a fara.

“Mu gane cewa abu ne mai illa a idon addini da al’umma,” ya karkare da cewa.

SP Kiyawa ya rufe taron da jan hankalin jama’a cewa sha’anin tsaro ba a kan hukumomi kawai ya ta’allaka ba, kowane dan kasa zai iya taka rawa wajen samar da tsaro a yankinsa.

TRT Afrika