“Iyaye da dama suna ganin koya wa ‘ya’yansu harshen uwa ci gaba ne,” kamar yadda wani uba ya shaida wa TRT Afrika. Hoto - Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Garba Nahantchi, wanda jami’i ne a ma’aikatar ilimi ta Nijar ya shiga rudani kan tunanin da wasu iyaye suke yi kan cewa ‘ya’yansu ba za su samu tushen ilimi mai kyau ba a rayuwa idan suka soma karatu da harshen uwa.

“Iyaye da dama suna ganin koya wa ‘ya’yansu harshen uwa ci gaba ne,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Garba ya bayyana cewa ba haka lamarin yake ba. “Duk wani yaro wanda ba a koya wa karatu a harshensa na uwa, akalla a shekarunsa na farko, ana tilasta masa koyon wata al’ada da ba tasa ba ce.

Don haka daya daga cikin tasirin wannan sabon tsarin shi ne kara riko da al’adunmu,” in ji shi. A kasar da ake da karancin masu ilimi a duniya, wannan wani batu ne mai sarkakiya.

Kamar yadda bayanai suka nuna daga cibiyar kididdiga ta hukumar ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO, adadin masu ilimi a kasar zuwa karshen 2022 na kan maki 37 cikin 100.

Tsarin da gwamnatin kasar ta fito da shi a 2012 ya tilasta amfani da harshen uwa domin koyar da dalibai a matakin farko na ilimi. Picha: Nyingine

Duk da cewa an cimma matsaya kan Jamhuriyyar Nijar na bukatar ta yi gaggawa da kuma kara bayar da himma wurin inganta ilimi, da alama hanyar da za a bi domin aiwatar da hakan ta raba kan kwararru da iyaye.

Wasu kwararru na da ra’ayin amfani da harshen da yara ba su saba da shi ba yana da matukar tasiri kan shekarun farko na ilimin yaro kuma akwai yiwuwar hakan zai iya mummunan tasiri kan ci gaban karatun yaro.

“Tsohuwar hanyar (a matsayin harshe daya na koyarwa) ta lalata al’adunmu; shi ya sa gwamnati ta yanke shawarar amfani da sabuwar hanya,” in ji Garba.

Sai dai aiwatar da tsarin koyarwa da harshen uwa a wani yanki na daban a shekarun ukun farko na firamare ba lamari bane mai sauki.

Garba ya tuna da wani lokaci da wani mahaifi ya tunkari wani malami, inda yake so ya san dalilin da ya sa ‘yarsa ke magana da harshen Zarma, wanda ‘yarsa ke magana da shi a gida.

“Mahaifin ya ce bai kai ‘yarsa makaranta domin ta koyi harshen da dama ta iya shi a gida ba.”

Makarantu 500 ne aka aiwatar musu da wannan tsarin a cikin kasar bayan an fitar da shi. Hoto: OTHERS

Jami’an da aka kira domin su shiga tsakani sun sha wahala kafin suka yi kokarin shawo kansa cewa rubutu da karatu a harshen Zarma wata fasaha ce da ta cancanci a koye ta.

Cire tarnakin Faransa

Tsarin da gwamnatin kasar ta fito da shi a 2012 ya tilasta amfani da harshen uwa domin koyar da dalibai a matakin farko na ilimi.

“Muna koyar da yaro daga aji daya zuwa uku da harshen uwa. Duk da cewa ana koya Faransanci, ba shi ba ne harshen da ake koyarwa da shi,” kamar yadda Garba ya bayyana.

“Idan yaro ya kai aji hudu, kashi 50 cikin 100 na koyarwar da ake yi ana yin ta ne da Faransanci inda sauran darussan ake yin su da harshen uwa.”

Makarantu 500 ne aka aiwatar musu da wannan tsarin a cikin kasar bayan an fitar da shi. Cikin harsuna 10 na kasar, takwas ne aka zaba domin koyarwar.

Daukar lokaci mai tsawo

Nijar ta dade tana tunanin amfani da harshen uwa a matsayin hanyar koyarwa a fannin ilimi inda ta soma wannan tunanin tun shekarun 1970.

“Tun daga 2012, an aiwatar da wannan tsarin a wasu zababbun makarantu,” in ji Mallam Kassoum Issa, wani malamain makaranta wanda ya yi ritaya a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Hukumomin ilimi a kasar wadda Faransanci ya kasance harshen kasar a hukumance na magana, na ganin wannan sabon tsarin na tafiya daidai duk da kalubalen da ake fuskanta.

Nazarin da aka yi wadanda aka kwatanta makarantun gargajiya (Faransa) da makarantun Faransa da Larabci da makarantun da ake amfani da harsuna biyu, (inda dalibai ke koyon harshensu na uwa da Faransaci) ya nuna cewa wannan sabon tsarin ya fi bayar da ingantaccen ilimi.

Makarantun da ake amfani da harshen Faransanci zalla su ne aka ba maki mafi kankanta wurin ingancin ilimi, kamar yadda kungiyar Global Partnership for Education ta bayyana.

Gina su tun suna yara

Dakta Nicholas Dominique, wanda dalibi ne wanda ya yi karatu a karkashin shirin gwaji domin amfani da harshen uwa wurin koyarwa a Nijar, na ganin hakan ya taimaka masa a rayuwarsa.

Wasu na ganin cimma muraadin batu ne mai sarkakiya a kasar da ake da karancin masu ilimi a duniya. Picha: AA

Dakta Nicholas wanda mai sharhi ne kan yankin Sahel, sai da ya bi ta wannan tsarin koyarwar a shekaru uku na makaranta wanda aka koyar da su a harshen Hausa a Maradi.

“A duk lokacin da za a yi jarrabawa, wadanda suka soma da karatunsu da Hausa sun fi kwazo fiye da wadanda suka soma karatunsu da Faransanci,” in ji shi.

Baya ga harshen Hausa da Faransanci da ya koya a Nijar, Dakta Nicholas na magana da harshen Ingilishi, wanda ya koya a lokacin da yake karatu a wata jami’a da ke makwaftaka da Nijeriya.

Kamar yadda masu ruwa da tsaki suka bayyana, tsarin karatun Nijar ba ya wasa da koyon harsunan waje. Haka kuma yana bayar da muhimmanci wurin harshen uwa a maimakon sauran harsuna wurin koyon ilimi.

TRT Afrika