Wani wuri tsakanin wannan tuƙi da kuma neman ciyayi maras ƙarewa na ɗan adam shine gaskiyar Afirka. . Photo: Getty Images

Daga Mazhun Idris

Kamar sauran labaran da ake samu daga Afirka wadanda ake yin su bisa kabilanci wadanda ba gaskiya a cikinsu, labarai kan hijira daga nahiyar akasari suna zuwa ne ba tare da cikakkiyar gaskiya ba.

Yadda lamarin yake na kwararar bakin-haure daga Afirka da ke gudun hijira daga kasashensu – wadanda suka rasa dama iri daban-daban, a tafiyar da suke yi mai tsananin hatsari, wadda aka yi musu alkawarin samun arziki mai yawa a kasashen da suka ci gaba.

Wani wuri tsakanin wannan tuƙi da kuma neman ciyayi maras ƙarewa na ɗan adam shi ne gaskiyar Afirka.

A dan tsakanin wannan lamari da kuma bukatar bil adama ta samun alherai na da alaka da yadda Afirka take.

Ko a cikin kasa mai dumbin arziki, a kowane lokaci na shekara, ana samun ayarin wasu ma’aikata da ke tsallaka iyakar kasar inda suke neman mafaka a wuraren da za su samu karin kudi da kuma damarmaki masu dorewa don su shana.

Matsalar tattalin arziki ce babba da ke sa mutane yin kaura a Afirka. Hoto. AP

“Yanayin yadda ci-ranin Afirka yake akasari daga kauyene zuwa birni, inda talakawa da ke kauyuka ke guduwa zuwa kasashe ko birane masu maiko,” in ji Dakta Muhammad Baba Bello, wani masanin noma da tattalin arziki daga Jami’ar Bayero ta Kano a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Haka kuma, bayanai da suka fito daga Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa ya nuna cewa masu tafiya ci-rani daga Afirka saboda aikatau “a cikin kasa yankin kashi 80 cikin 100 ne”.

Yada zango a Tunisia

Adnen Ben Hadj Yahia yana da cibiyar koyar da sana’a wadda ake kira El Space a Tunis, babban birnin Tunisia inda yake zama tsani ga mutane da dama da ke tafiya ci rani daga Arewacin Afirka.

A matsayinsa na wanda yake kallon kansa da kungiyarsa a matsayin masu ra’ayin kawo sauyi, daya daga cikin abin mamaki a rayuwarsa shi ne yadda yake ganin ‘yan ci-rani wadanda suke sauka a Tunis a karshe suke ci gaba a nan.

Dubban 'yan cirani daga kasashen Afirka sun rasa na yi a Tunusiya. Photo: Reuters

“’Yan ci-rani daga Afirka na zuwa Tunis da Sfax da Gabes inda suke tafiya Turai. Sai dai wasu musamman mata, sai suka gane za su iya aiki domin tara kudi a nan, sai su tsaya su tara jari kafin su koma gida,” in ji shi.

“A cibiya, muna horas da ‘yan ci-rani kan yin sana’o’in da za su dogara da kansu ko da ba su yanke shawarar yin tafiya mai hatsari zuwa Turai ba. Muna taimaka musu samun kananan ayyuka da albashi mai tsoka.”

“’Yan ci-rani daga Afirka na zuwa Tunis da Sfax da Gabes inda suke tafiya Turai. Hoto: AP

Akwai dumbin matasa daga Tunisia wadanda suke zuwa manyan birane inda suke zuwa jami’o’i inda kuma daga baya suke tafiya kasashen waje. Wasu daga cikinsu suna karewa wurin neman ayyukan yi masu kyau a wadannan biranen da kuma zama a can.

Zirga-zirgar ma’aikata

Yanayin yadda ake zirga-zirga domin aiki tsakanin kasuwannin Afirka na kara hada kan yankuna. Irin wadannan hanyoyin wadanda ake zirga-zirga a kansu sun shafi yankunan kasashen da ke da tattalin arziki.

“Duk a cikin kasar, hijira da ake yi daga kauyuka zuwa birni na taimaka wa wurin dorewar samun ma’aikata ga kamfanoni da wuraren sana’o’i da ke a garuruwa da birane,” in ji Dakta Muhammad.

Kamar yadda Kungiyar Kwadago ta Duniya ta bayyana, kasashen Afirka kadan ne ba su samun irin wadannan ‘yan ci-ranin, ko dai a matsayin kasashen da ‘yan ci-ranin ke yada zango ko kuma suke tarewa a can.

“Neman ma’aikata a bangarorin da suka hada da aikin gona da kamun kifi da hakar ma’adinai da kuma wasu ayyukan da suka hada da ayyukan gida da kiwon lafiya da aikin shara da aikin gidan abinci da otel-otel da sayar da kayayyaki na da muhimmanci a nahiyar,” kamar yadda rahoton na Kungiyar Kwadagon ta bayyana.

Tun daga Afirka ta Kudu zuwa Nijeriya da Kenya da Masar, manyan birane da manyan garuruwa suna neman ma’aikata da za su yi aiki a kudi kadan daga kauyuka masu nisa.

Idan aka cire batun hijira domin neman aiki, akwai wadanda suke rabuwa da muhallansu saboda yaki da yunwa da ambaliyar ruwa. Photo: Reuters

A duk shekara, manyan kasashe masu karfin tattalin arziki kamar Nijeriya jawo hankalin ma’aikata masu son albashi daga kasashe matalauta da ke makwaftaka da ita kamar su Nijar da Benin da Chadi da Kamaru da Togo.

Batun sauyin yanayi

Kamar sauran abubuwa da suka shafi sauyi, akwai abubuwan da ke jawo ‘yan ci rani da kuma abubuwan da ke ja ‘yan ci-rani tafiya. A bangaren Afirka, abubuwan da ke saka wa ana tafiyar suna a kauyuka.

Sauyin yanayi da kuma rikici a kasashen Afirka da dama na yin tasiri a hijirar da ake yi a cikin nahiyar. Idan aka cire batun hijira domin neman aiki, akwai wadanda suke rabuwa da muhallansu saboda yaki da yunwa da ambaliyar ruwa.

Kaurar matasa zuwa birane na jawo koma baya a harkokin noma a kauyuka. Hoto: AFP

Ba kamar a shekarun 1990 ba, a lokacin da Afirka ke tsananin fama da ‘yan gudun hijira wadanda a halin yanzu suke zaune a kasashen da ke makwaftaka da nasu wadanda suka hada da Sudan da Habasha da Nijar da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka.

Matsalolin cirani

A ajiye batun masana tattalin arziki a gefe, kan batun kaura, masana tattalin arziki su ne masana ilimin kasa da ke fayyace tasirin kaurar jama'a masu yawa da matsalolin tattalin arziki da hakan ke jawowa a kan muhalli da yawan al'umma da kuma amfana daga arzikin kasa.

Dr Murtala Uba Mohamed, wanda ke koyar da ilimin labarin kasa da tsarin tattalin arziki a Jami'ar Bayero ta Kano, ya bayyana yadda ci-rani ke shafar karuwar yawan jama'a da haihuwa da mace-mace a cikin al'ummomi.

Yawanci wasu 'yan ciranin da ke kaura a tsakanin kasashen nahiyar Afirka ba sana'a mai karfi suke yi ba. Photo: Reuters

"A hanyoyi da dama, yin ci-rani a tsakanin kasashen Afirka yana yin tasiri a zamantakewa da tattalin arziki - ba ta wajen inganta tattalin arziki da bambance-bambancen kabilu ba, har ma da wajen rikice-rikice da aikata laifuka."

Ganiyar shekarun aiki

Bayanai daga wata cibiya ta STATAFRIC Migration ya nuna cewa a 2019, kashi 77 cikin 100 na kaura daga Afirka mutane da ke kan ganiyar shekarun yin aiki ne suka yi ta.

A yankunan karkara, tafiyar matasa majiya karfi cirani na matukar shafar harkar noma, inda a biranen kuma ba a samun kasar yin nomar ko damar yin hakan.

Don haka tafiyar majiya karfi birane don cirani ta sa yankunan karkara na samun koma baya a fannin samar da abinci da karuwar talauci.

Duk da cewa mafi yawan 'yan ciranin kan aika kudadse gida daga cikin abin da suke samu, tsananin mayar da hankali wajen ayyukan samun kudade a birane da gabobin teku suna sake samar wa talauci gindin zama a kauyuka.

An yi wa kayayyakin more rayuwa rubdugu

Yawan kaurar da ake yi daga kauyuka zuwa birane ta sa albarkatun da ake da su a biranen na yi kadan, musamman ma abubuwan more rayuwa.

A cewar Dr Mohammed, biranen da ke fadada ma suna fuskantar matsalar karuwar farashin filaye, lamarin da a karshe yake shafar 'yan ciranin da suka je daga kauyuka har su gaza kama gidan haya mai dan kyau.

"Da wuya ka ga wani babban birni a Afirka da babu unguwannin marasa galihu. A Legas akwai makoki, a Nairobi akwai Kibera a Johannesburg akwai Soweto," yadda ya lissafa.

Tafiyar majiya karfi birane don cirani ta sa yankunan karkara na samun koma baya a fannin samar da abinci da karuwar talauci.: AFP

Sannan kuma tasirin masu kudi da irin gidajen alfarma da suke ginawa ya sa ake kara samun cunkoson yin unguwannin da ba a tsare suke ba, ta yadda har kwararru suka yi amannar cewa ba za a yi raba 'yan cirani da kaura zuwa birane ba.

Mafita

Wani dan Tunisiya Adnen Nino ya yi amannar cewa karuwar masana'antu a birane na yin illa ga harkar noma a kauyuka. "Wadannan masu harkar noman a kauyuka suke aiki a masana'antu a birani," ya ce.

Dr Mohamed ya gamsu cewa babbar mafita ga matsalar tafiya cirani a tsakanin nahiyar ita ce kasashen Afirka da biranenta su bi diddigin bayanan masu kurar, su kuma yi amfani da su yadda ya kamata ko don tsara tattalin arziki da yawan al'umma da kuma kula da filaye.

Ya nemi gwamnatoci da su dinga tsara yadda za a yi kasafin arzikin kasa da tsara birane da samar da gidaje masu rahusa da cigaban yanki da bayar da damarmaki iri daya, da kuma samar da hanyoyin rage wa iyalan da ke kauyuka radadin rayuwa.

Idan dai ba hakan aka yi ba, to batun cirani a kasashen nahiyar Afirka ko tafiya kasashen Turai - zai ci gaba da zama matsala ga kowace kasa da al'ummarta.

TRT Afrika