Wasu masana sun bayyana cewa ba shakka waka da kuma rerata da ake yi wani abu ne mai karfi da jan hankali. /Photo AA

Daga Halima Umar Saleh

Wakokin Afirka kamar irin su Coupe Bimbamba ta Awilo Longomba da Premier Gaou wadda mawakan nan na Ivory Coast suka yi ko kuma wakar Burna Boy ta Last Bruna, sun wuce batun kalaman da ake yi a wakokin.

A wurin bukukuwa, wadannan nan ne wakokin da ake yawan sakawa a duk lokacin da aka kira ango da amarya su hau kan dandamali domin taka rawa – akasarin mutane sun san wakokin, wasu na rera su, ba da jimawa ba sai a ga ‘yan kallo su ma sun soma kada kafafuwa.

Mene ne a cikin wakokin Afirka da ke sa ‘yan nahiyar ke son na kasashe daban-daban, kuma mene ne sirrin da ya sa wakokin ke hada kan 'yan nahiyar?

Daga wakokin baka zuwa na Gambara da na Hiphop, waka wata aba ce da ke hada kan ‘yan Afirka. Amma ta ya hakan ke faruwa a yankin da ke da akwai harsuna daban-daban da al’adu da addinai da kabilu daban?

Wasu masana sun bayyana cewa ba shakka waka da kuma rerata da ake yi wani abu ne mai karfi da jan hankali.

“Akwai wani abu game da waka da haka yake duk duniya. Duk da cewa an raba waka gida-gida kamar su Reggae da wakokin Gambara da na Hiphop, duk wata waka za ta iya dukan zuciyar masu saurare da ke da al’adu da kabilu daban-daban,” kamar yadda Ibrahim Sheme wanda marubuci ne a Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika.

Soyayyar wakoki daban-daban

Mawakan Afirka irin Oumou Sangare ta Mali sun yi tashe sosai a arewacin Nijeriya /Photo Oumou Sangare Facebook

Tsawon shekaru, yadda ‘yan Afirka ke ta son wakoki daban-daban na yankuna na karuwa ne ba raguwa ba, duba da yadda ake sakin sabbin wakoki masu daukar hankali da kuma yadda intanet ya zagaye nahiyar.

Salon waka na Amapiano a misali, ya samo asali ne daga Afirka ta Kudu kafin cutar korona kuma ya ratsa nahiyar Afirka sosai, kamar dai yadda wakokin ‘yan Kongo da Swahili suka yi.

A Nijeriya, al'ummar kasar sun fi sauraren wakokin Nijar da Mali da Habasha da Afirka Ta Kudu da Congo da Ghana da na Gabashin Afirka da Ivory Coast da kuma na Sudan.

‘Yan Nijar na son wakoki daga Nijeriya da Mali da Ivory Coast kamar yadda suke son nasu

“Yadda mutanen Jamhuriyyar Nijar ke matukar son wakokin Hausa abin burgewa ne. Su ne wakokin da suka fi farin jini ko a tsakanin sauran kabilun kasarmu da ba sa jin Hausa,” in ji Djamilou Ibrahim Oumarou, wani dan kasuwa a Nijar.

“Duk inda ka je, kasuwanni ko wuraren shan shayi ko tashar mota – za ka ji ana jin wakokin Hausa. Baya ga wadannan wakokin, jama’a kuma na sauraren wakokin Mali da Ivory Coast," in ji Djamilou.

A kasashen yankin Tsakiyar Afirka, mutane na son wakokin Nijeriya da Afirka ta Kudu da Gabashin Afirka da wakokin Kongo fiye da ko wadanne wakoki.

Mawakin Hausa Umar M Shareef a arewacin Nijeriya ya ce hadaka da wasu kasashen zai habaka yaduwar harshe/Umar Shareef Facebook

A Gabashin Afirka, an fi son wakokin Nijeriya da Afrika ta Kudu da wakokin Mali kamar Selif Keita da Habib Koite da kuma wakokin Lingala na Congo wadanda suka samu karbuwa a fadin nahiyar.

Hadin gwiwar mawaka a nahiyar Afirka

Mawakin gambara kuma dan gwagwarmaya Webiro “Wakazo” Wassira wanda kuma tsohon dan kwamitin wakokin Tanzaniya ne, na ganin hadin gwiwa tsakanin mawakan Afirka na taimakawa wurin saka kishin nahiyar da kuma hada kan masoyan mawakan.

“Abubawan da ake fada a cikin wakoki ba a kowane lokaci yake tafiya ko zuwa daya ba, amma ana jin dadin kidan da abin da ake cewa,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Koffi Olomide daga Congo ya yi hadin gwiwa da mawakan Gabashin Afirka da dama.

Ita ma mawakiya Angelina Kidjo wadda ta sha lashe kyaututtuka ta yi hadin gwiwa sosai da mawaka kamar su Sauti Sol na Kenya da harshen Swahili, da kuma Yemi Alade ta Nijeriya da harshen Yarabanci.

Awilo Longomba na kasar Kongo shi ma ya yi wakokin hadaka da wasu mawakan Nijeriya cikin harsunan kasarsa da nasu.

Mawakin Tanzania Diamon Platnumz shi ma ya yi hadin gwiwa da mawaka daga Nijeriya da Afirka ta Kudu da Congo inda suka samar da wakokin da harshen Swahili.

Shi ma fitaccen mawakin Nijeriya Burna Boy, wanda yake waka da harsuna da dama ya yi hadin gwiwa da mawaka daban-daban a fadin nahiyar, hadin gwiwarsa da ta fi shahara ita ce da mawakin Senegal Youssou Nd’our, wanda shi ne tsohon ministan yawon bude ido na kasarsa.

An yi amanna cewar ba mawakin Afirkan da ya kai Diamond Platnumz na Tanzaniya yin wakokin hadaka/Photo Platinum Facebook

Sho Madjozi ta Afirka ta Kudu ta yi waka da mawaka daban-daban daga Gabashin Afirka da harsunan Zulu da Swahili.

Ta yi suna da wakokin da ta yi irin su John Cena, wadda gaba daya da harshen Swahili ta yi ta, kafin ta soma hadin gwiwa da sauran mawakan Tanzaniya.

Ana ganin Diamond Platnumz ba shakka shi ne mafi shahara a mawakan Gabashin Afirka inda yake yin wakoki akalla 25 a duk shekara tun daga 2018, inda sama da rabinsu na hadin gwiwa ne a fadin nahiyar.

Shi ma mawakin Hausa na Nijeriya Umar Sherrif ya yi tarayya da mawakan Ghana kamar su D-Flex da Wakili domin samar da wakokin da aka yi da Hausa da Turanci don su isa ga masoyan waka da dama musamman a Yammacin Afirka.

Sherrif na ganin irin wannan hadin gwiwar “zai yi tasiri matuka wurin tallata kananan harsunan Afirka.”

Marubuci kuma mai sharhi Ibrahim Sheme na ganin wannan hadin gwiwar na taimakawa wajen tallata su kansu mawakan wadanda suke zagaye nahiyar domin samun sabbin masoya.

Dalilai masu kamanceceniya

Wasu masana tarihi na ganin dalilin da ya sa wakokin Afirka ke kawo hadin kai wani abu ne na tarihi wanda ya soma shekaru da dama.

Sho Madjozi ta Afirka ta Kudu ta yi waka da mawaka daban-daban daga Gabashin Afirka da harsunan Zulu da Swahili/Sho Madjozi Facebook

Wasu na ganin abin da ya taimaka wa hakan ya fara ne da hijira da mutane ke yi daga wannan yanki zuwa wancan domin kasuwanci ko kuma ilimi. Daga haka ne jama’a suka soma koyo wakoki suna kaiwa yankunansu.

Malam Ibrahim Sheme na ganin kamanceceniya da ke da akwai ta al’ada da adinni da zamantakewa tsakanin al'ummomin Afirka na daga cikin abubuwan da ke hada kan nahiyar.

“Wani dalili kuma shi ne abin da nake ganin mutane suna ganin kansu daya. Mutane na kallon al’adunsu na kama da na wasu. Salon waka da al’adun wasu wakokin na sa wasu son wakokin wasu kabilun,” kamar yadda ya bayyana.

Mawaka a halin yanzu suna son mabiya da dama har wadanda ba sa jin harshensu.

Umar Sherrif ya shaida wa TRT Afirka cewa yana kallon wadanda ba sa jin harshen Hausa a matsayin mabiyansa.

Tasirin wakoki

Wakokin Afirka sun taka muhimmiyar rawa wurin bayani da kuma ilmantarwa kan yadda nahiyar take.

Haka kuma wakokin suna fito da al’adu da kuma akida.

A yanzu 'yan Sudan da dama kan kwaikwayi shigar Hausawa saboda yawan kallon wakokinsu/Photo AA

Ga wanda ya girma a arewacin Nijeriya daga karshen shekarun 1980 zuwa 1990, mutum zai iya sanin mawaka daga Nijar da Mali da Kamaru da Tanzaniya da Habasha da Ghana da Afirka ta Kudu da Sudan.

Duk da cewa abu ne mai wahala mutum ya fahimci me ake cewa wakokin, suna samar da wani hadin kai tsakanin Afirka da ‘yan nahiyar.

Wani dan jarida a Sudan Salman Farisi ya bayyana cewa mutane da dama a kasarsa sun san wakokin Afirka ta hanyar kallonsu a YouTube.

“Kafin wannan lokacin, yadda ‘yan Sudan ke saka kaya ga maza shi ne su saka doguwar jallabiya da makawuya, mata kuma sun fi saka laffaya.

"Amma a yanzu akwai ‘yan Sudan da dama wadanda ba su taba fita daga kasar ba da suke kwaikwayon saka kayan Hausawa sakamakon irin soyayyar da suke yi wa wakokinsu," in ji Salman.

Ya ci gaba da cewa "Maza na saka dogayen kaya jamfa da wando na yadi ko shadda, mata kan sa zani ko siket da riga na leshi ko atamfa kamar yadda matan Hausawa suke yi”.

Shahararren dan fim din Hausa Marigayi Rabilu Musa Ibro ya taba yin wani fitaccen fim din Hausa, Ibro Awilo inda ya kwaikwayi mawakin nan na Kongo Awilo Longomba.

Wakokin Amapiano na Afirka Ta Kudu sun yi tasiri kan mawakiya Niniola Apata wadda ta kwafi irin salon da Yarabanci, lamarin da har ya sa wasu ‘yan kasar Afirka ta Kudu da dama suke gani kamar asalinta 'yar kasarsu ce.

Mutane kuma suna kallon kamanceceniyar su daga wasu al’ummomi ta hanyar waka.

Farisi ya bayyana cewa “Nasarar da wakar Turar So ta yi a kasar nan {Sudan} na daga irin kayan kidan da aka yi amfani da su a wakar wadanda 'yan kasar suka lura irin na Sudan ne.

Shahararren furodusan wakokin nan na kudancin Nijeriya, Sarz ya yi wakoki da dama inda yake kwaikwayon salon wakokin na Afirka Ta Kudu.

Koyon harshe ta hanyar waka

Wakokin mawakin kasar Congo Awilo Longomba sun karade nahiyar Afirka/Awilo Facebook

Masana kamar Ibrahim Sheme na ganin daya daga cikin hanyoyi masu sauki na koyon harshe shi ne ta hanyar waka, inda mutane kan gano kalmomi kuma su fade su daidai.

Hafsatou mai shekara 30 wadda ‘yar kasar Kamaru ce da ke magana da harshen Faransanci da kuma harshenta na gado Fulatanci, ta shaida wa TRT Afrika cewa “Na soma koyon Hausa da Yarabanci da Wassoulou ta hanyar sauraren wakokin Nijeriya da Mali...

"Ina so na yi tafiya zuwa wadannan kasashe na ga abin da nake gani a bidiyon wakokin. Ina yawan jin dadin wasu wakokin musamman idan na gane cewa wasunsu na magana ne kan soyayya da kulawa; suna motsa masu rai," a cewar Hafsatou.

Haka lamarin yake a gabashi da tsakiya da kudancin Afirka, inda waka ta zama wata hanya ta fahimtar wani harsuna.

Yada wakoki a shafukan Tiktok na kuma taimakawa wurin tallata harsuna da kuma al’adun Afirka.

Mawakan Nijeriya irin su Olamide Gbenga Adedeji wanda ke waka da Yarabanci na daga cikin mawakan da wakokinsu ke sharafi a Tiktok.

Haka ma Ditto Chibuzor Nelson Azubuike wanda aka fi sani da Phyno da yake wakar gambara da harshen Igbo. Sai kuma Chinedu Okoli wanda aka fi sani da Flavour shi ma yana yi da harshen Igbo.

Duka wadannan wakokin sun shahara ne a tsakanin mawakan Afirka matasa.

TRT Afrika