Yadda mummunar mu’amalar Turai ga Afirka ta janyo rikicin ‘yan gudun hijira

Yadda mummunar mu’amalar Turai ga Afirka ta janyo rikicin ‘yan gudun hijira

Wasu kasashen Turai suna fuskantar sakamako na ko-oho da duniya ta dade tana yi game da batun gudun hijira.
'Yan gudun hijira na rasa rayukansu a teku yayin kokarin tsallakawa Turai./ Hoto: AA

Daga Yahya Habil

A shekaru goman da suka gabata, rikicin 'yan gudun hijira a tekun Bahar Rum ya zama batu mai muhimmanci da ke sanya damuwa ga kasashe da dama da ke gabar Bahar Rum da Turai.

Kasashe irin su Italiya da Girka sun fuskanci kwararar 'yan gudun hijirar Afirka da suke fitowa daga kasashen Libiya da Tunisiya.

Abin ya yi muni a 2014 inda Italiya ta shaida zuwan 'yan gudun hijira 170,000, wanda wannan ne adadi mafi yawa da aka taba gani a tarihin Turai.

Ya zuwa 2023, bayanan leken asiri na Italiya sun nuna ana ci gaba da samun kwararar 'yan gudun hijirar, inda ake tsammanin za a samu shigar 'yan hijira 700,000 Turai daga Italiya.

Wannan hasashe na nufin wannan rikicin na masu neman mafaka ya zama matsin lamba, wadda ke ci gaba da sanya damuwa.

Gudun hijirar wadannan mutane zuwa kasashen Turai ta haifar da rashin tsaron al'ummar yankunan da suke zuwa. Gudun hijira na kawo damarmaki da matsaloli a lokaci guda ga kasashen.

A gefe guda, akwai matsalolin tsaron kan iyaka da na rashin tabbatar da doka. Kazalika, ana fuskantar matsaloli na samar da kayan kula da lafiya da kayan more rayuwa sakamakon shigar 'yan gudun hijira.

Ci da gumin wasu

Amma kuma, ya kamata a fahimci cewa 'yan gudun hijira suna bayar da gudunmawa wajen cike gurbin ayyuka a kasashen, sai dai fadin yawan wannan gudunmawa abu ne mai wahala.

Kudaden da gudun hijira suke samar wa kasashen da suka je suna da matukar yawa kuma ya zama batun da ake tattauna wa ko yaushe, sannan akwai alkaluma mabambanta daga kasashe daban-daban na irin wadannan kudade.

Abu mai rikitarwa ya haura batun tattalin arziki, wand ya kai ga zamantakewa, siyasa da tallafa wa bil adama.

Magance alamun matsalar kawai ba zai warware ta ba, sai an shawo kanta daga tushe - ma'ana a koma ga tarihin kasashen Yamma da suka dinga ci da gumin Afirka ta hanyar bautar da bayi, kasuwanci da sace musu albarkatun kasa da kayayyakin al'adu masu daraja, da ma jagoranci.

Wannan abu da aka yi ya bar Afirka a cikin rikici, wanda yake sanya wasu 'yan nahiyar gudun hijira da kayan jikinsu kawai. Wasu za su iya cewa kasashen Yamma suna biyan bashin da suka ci a baya ne daga Afirka, amma kuma ba ta hanyar da ta dace ba.

Tambayar ta yaya Yammacin duniya ya dinga ci da gumin Afirka batu ne na tarihi da ke da rikitarwa, wanda ya shafi karni da dama da aka dauka ana mulkin mallaka, mamaya da sace arziki - ana bukatar tsinkaye don duba wannan batu tare da fahimtar halin da ake ciki a yau da yadda za a magance shi.

A yanzu Italiya na fuskantar sakamakon abin da ta aikata a baya na rura wutar rikici a Afirka tsaron karni da yawa.

Rikita-Rikita

Wannan hali na daukar hankalin duniya zuwa ga tushensa, amma shi ma ba ta hanya mai kyau ba, amma ana sa ran wannan abu ya amfani Afirka a nan gaba.

Wasu manyan 'yan siyasar Italiya, da suka hada da Firaminista Giorgia Meloni sun dora laifin wadannan abubuwa a kan faransa, kuma ana ta muhawara kan wannan tun kafin zaman ta Firaminista.

Wani bidiyon Girogia Meloni da aka yi ta yada wa ya bayar da haske kan gungun mugaye na Afirka da Turai da yadda suka samu kansu a makale a cikin su, wanda wannan bidiyo ya kamata a kalle shi don fahimtar halin da ake ciki.

Da suke nuna yadda Faransa ke ci da gumin Afirka, kafar yada labarai ta Pambazuka News ta rawaito cewa tun 1961, Faransa ke rike da lalitar kasashe 14 da ta yi wa mulkin mallaka.

Dadin dadawa, an yi hasashen Faransa na rike da dala biliyan 500 na kasashen Afirka a lalitarta, inda ta hana wadannan kasashe karbar kudadensu.

Kasashen za su iya samun kaso 15 na kudadensu duk shekara, inda ake tirsasa musu karbar bashin kaso 85, hakan na nufin an tare kudadensu da hana su amfana da su.

Killatattun 'yan gudun hijira

Domin katange wannan batu, Faransa ta saka iyakar adadin kudin da wadannan kasashe za su iya ranta daga lalitar, wanda hakan ke kara sanya wa suna dogaro da ita kan tattalin arziki.

Duk da shaidar da ake da ita ta alakar Yammacin duniya da tatsar Afirka da rikicin 'yan gudun hijira, kasashen Yamma na yawan korafi game da kwararar 'yan gudun hijirar tare da dora laifi kan kasashe irin su Libiya da Tunisiya.

Abun takaici, da yawa daga cikin wadannan 'yan gudun hijira na yin kokarin isa Turai inda suke fuskantar nun wariya daga al'ummunsu.

Rashin samar da wani takamaiman tsarin warware matsalolin daga kasashen Turai. Ana ta yin kira daga shugabannin Tarayyar Turai musamman ma Firaministar Italiya Giorgia Meloni kan a maganc wannan matsala.

A yayin da kalaman Meloni suke smaun goyon baya, hakan bai sanya Italiya sauke nata nauyin ba, kasar na da laifin ta'azzarar matsalolin da 'yan gudun hijira ke fuskanta musamman na nuna wariya da rashin tausayin bil'adama.

Misali, akwai rahotanni na masu neman mafaka da ake tsare da su bayan sun isa Italiya, inda ake shirin mayar da su kasashen da suka fito.

Dama mafi kyau

Wadannan ayyuka na kara ta'azzara wahalhalun 'yan gudun hijira ne, inda ake kira da a dauki matakan magance dalilan da suke janyo wannan balahira.

Domin kawo karshen wannan matsala, ana bukatar Tarayyar Turai da ta samar da mafita mai kyau da za kakkabe wannan matsala daga tushenta na Afirka. Wani mataki shi ne saukaka manufofin hana gudanar da wasu ayyukan cigaban tattalin arziki da Faransa da Ingila suka sanya wa wasu kasashen Afirka.

Sannan kuma, samar da tsarin tattalin arziki mai dore wa a kasashen Afirka, wanda hakan zai rage yawan 'yan gudun hijirar, daukar irin wadannan matakai ne mafita maimakon bayar da kayan taimako irin wanda aka yi wa Tunisia.

Eh taimakon da aka baiwa Tunisiya zai taimaka wata wajen bukata kudade da take da su, amma mayar da hankali ga warware rikicin Afirka na da matukar muhimmanci.

Idan aka bayar da kudade da kayan aiki don tallafa wa wadannan kasashe, akwai yiwuwar a samu a warware rikicin 'yan gudun hijirar tare da samar da cigaba mai dore wa a yankin.

Marubicin, Yahya Habil, dan jarida mai zaman kansa ne da ke Libiya wanda yake mayar da hankali kan harkokin Afirka. A yanzu haka yana aiki tare da wata kungiya a Gabas ta Tsakiya.

Togaciya: Ra'ayin wannan marubuci ba lallai ne ya zama shi ne irin ra'ayin TRT Afirka ba.

TRT World