Samuel Perry (daga dama) na daga cikin masu barkwanci na Nijeriya da suka fi fice. Hoto/Samuel Perry/Instagram

Daga Charles Mgbolu

Wasan barkwanci da ake kallo a intanet ya kawo sauyi matuka daga wasan barkwanci na gargajiya da aka saba da shi na da shi na daɓe, wanda mai wasan barkwancin ke hawa kan dandamali a dakin taro ya yi ta bayar da dariya.

A baya, an samu sauye-sauye, inda ake samun wasannin barkwanci ta sauki sakamakon zuwan intanet. Idan mutum yana da waya ta zamani da kuma intanet, masu son barkwanci za su iya kallon barkwanci iri-iri, inda kalubalensu kawai shi ne su zabi wanda ya yi musu domin su kalla.

Wannan wata hujja ce idan aka yi la’akari da mutanen da ake gani suna kallon wasan barkwanci ta internet. Misali, fitaccen mai wasan barkwancin nan na Nijeriya Samuel Animashaun Perry yana da akalla mutum miliyan hudu da ke kallon duk bidiyo daya da ya yi.

Bayanai daga Cibiyar Kuri’ar Jin Ra’ayi ta Afrika (API), sun nuna cewa mutum biyar na farko daga Nijeriya na masu samar da irin wannan barkwancin na da jimlar mabiya miliyan 53 a kafafen sada zumunta daban-daban.

“A nan kasuwar take a halin yanzu,” kamar yadda Christian Iroka, wani mai wasan barkwanci a kafafen sada zumunta ya shaida wa TRT Afrika. “

Kamfanoni da ‘yan kasuwa sun fi son aiki da masu dumbin mabiya a shafukan sada zumunta.

Shi ya sa wannan sabon tsarin na barkwanci ke habaka.

Yaga, wanda wani mai samar da wasan barkwanci ne a shafukan sada zumunta daga kasar Kenya wanda ke da sama da mabiya miliyan 1.2 a Tiktok, ya ce a halin yanzu wasan barkwanci na daɓe ba shi da yawa.

Masu bidiyo ta intanet a halin yanzu suna aiki da masu daukar hoto da sauran 'yan kuru na fina-finai domin samar da ingantattun bidiyo. Hoto/Reuters

“A wasan barkwanci na daɓe, mutanen da ke cikin dakin nan ne kawai za su kalle ka, ko ma ya adadin su yake. Su kadai ne za su iya kallon abin da kake yi a daidai lokacin,” in ji shi.

“Amma da kafofin intanet, za ka iya samun jama’a ba iyaka; babu wata kayyadewa,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

A shekarun 1990 da 2000, wasan barkwanci na daɓe shi ake rububi domin nishadi, inda ake sayar da tikiti da tsada. A lokacin tsakiyar hutu, ana sayar da tikitin zuwa kallon wasannin barkwanci har naira miliyan daya.

Amma a yanzu, wasan barkwanci na daɓe ba su cika tasiri ko bayar da sha’awa ba.

“An kwana biyu ban ji an shirya irin wannan wasan ba,: in ji Christian Iroka “Wani babban sauyi ne inda a yanzu wasa daga cikin manyan masu wasan barkwanci ke komawa kafafen sada zumunta,” in ji shi.

Kudaden shiga masu yawa

Wasu daga cikin kafafen sada zumunta kamar YouTube, na biyan masu saka bidiyo zunzurutun kudi har dala 40,000 a duk wata.

Mai wasan barkwanci na daɓe daga Afirka ta Kudu Trevor Noah har yanzu na daga cikin masu samun mutane. Hoto/AP

Kamfanin Meta, bayan kaddamar da tsarin dogon bidiyo na Facebook da Instagram, ya ce yana biyan masu bidiyo har dala 35,000 a duk wata kan iya adadin mutanen da ke kallo.

‘Wasannin barkwanci na daɓe ba za su iya gasa da irin wadannan ba, Wane irin taro ne za a yi na wasan daɓe da zai iya biyan mai wasan barkwanci irin wadannan kudaden a duk wata?” kamar yadda Yaga ya yi tambaya.

Kamfanoni za su neme ka idan kana da mabiya da dama a kafafen sada zumunta, hakan na nufin saka abubuwan ku da yawa a kafafen sada zumunta na da amfani sosai,” in ji Eric Omondi, wanda shi ne dan wasan barkwancin Kenya da ya fi kowa mabiya a kafafen sada zumunta.

David Mensah, wanda mai wasan barkwanci ne na daɓe, na ganin wasan barkwanci na fuska da fuska har yanzu yana da muhimmanci.

“Za a ci gaba da samun mutane wadanda za su ci gaba da son barkwancin zahiri. Abin da masu wasan barkwanci na daɓe ke bukata a halin yanzu kawai shi ne fito da sabbin tsare-tsare,” in ji shi.

Akwai masu wasan barkwanci na daɓe da dama da suka san cewa suna da bukatar tafiya da lokaci inda kuma suke wallafa bidiyoyinsu a shafukan sada zumunta.

“Duk da haka akwai bambanci sosai sakamakon masu barkwanci na daɓe na iya saka bidiyonsu ne kawai bayan an yi wani taro, wanda ake daukar watanni ana shiryawa.

Ba zai zama daya da wanda ake fitarwa bagatatan a kafafen intanet ba wadanda suke wallafa bidiyo a kullum,” in ji Mensah.

Ba lamari bane mai sauki ga su kansu masu samar da wasan barkwanci a kafafen sada zumunta.

Babu abin da yake zuwa da sauki, in ji Yaga. “Ya zama dole ku yi aiki tukuru ku samar da adadin mutanen da ake bukata na kallon bidiyo.

Wasu da ke kusa da ni sun taba shaida mani cewa ba ni bayar da dariya kuma ina bata lokaci na, amma ban bari hakan ya sagar mani da gwiwa ba,” kamar yadda ya kara da cewa.

Sauyin da aka samu ta fannin wasan barkwanci a kafafen intanet yana da kyau, sai dai ba a iya musu, hakan na nufin idan suka bukaci wani sauyi na wasan barkwanci, masu yin na daɓe watakila su sake samun dama.

TRT Afrika