Suna aiki a wani asibitin al’umma a wani wuri da bai da nisa daga tsakiyar birnin Yola na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Damuwar da suke da ita kan tsawon lokaci da suke kwashewa a kan hanya ba ta kai irin damuwar da suke da ita game da hatsarin da za su iya shiga a hanyar ba.
A zantawa da TRT Afrika, ma’aikaciyar rigakafi, Dorothy Ezikiel, ta ce ‘’nakan tafi Mayo da Gombi, wadanda suke kimanin sa’a biyu daga wurin da nake zaune. Kafin na tafi, nakan yi addu’ar Allah Ya kare ni.’’
A cewar Dorothy mai shekaru 26, ‘’na san ina yin babbar kasada, domin za ka iya shiga hannun masu garkuwa da mutane ko ma ‘yan ta’adda idan kana tafiya a hanyar mota zuwa yankunan karkara.’’
A shekarun baya-bayan nan matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa ta karu musamman a arewacin kasar.
Alkaluma daga cibiyar kwararru kan hulda da kasashen waje da ake kira Council on Foreign Relations wadda ke da mazauni a Amurka, na nuna cewa an yi garkuwa da mutum fiye da 4,000 a Nijeriya a 2022 yayin da aka kashe sama da 4,500.
A 2018, Boko Haram ta yi garkuwa da ma’aikatan agaji mata su uku a jihar Borno mai makwabtaka da Adamawa.
A watan Yunin 2022, babban jami’in ayyukan jin kan bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya ya shaida wa kafofin labarai na cikin gida cewa yawan kai hare-hare a kan ma’aikatan agaji, musamman a jihar Adamawa da yankuna masu makwabtaka da ita a arewa maso gabashin kasar, na kawar da hankali daga ayyukan agaji.
Duk da hatsari ga rayuwarsu, ma’aikatan lafiya a wadannan yankuna na ci gaba da taimaka wa jama’a, suna shiga lunguna, wasunsu masu wuyan zuwa, domin ayyukan rigakafi da ake matukar bukata da kuma rarraba magunguna.
Lokaci mai ban tsoro
John Manabeta, Daraktan Zattaswa na wata kungiyar fafutikar kare hakkin mata, yana mamakin irin karfin hali da ma’aikatan lafiya ke ayyukan duk da hatsarin da suke fuskanta.
‘’Su kadai suke zuwa wadannan kauyukan. Ba su tafiya da rakiyar jami’an tsaro … babu komai. Sukan dai yi fatan komawa gida lafiya’’ a cewarsa.
Shiga yankuna masu hatsari ba shi ne kadai ke damun ma’aikatan lafiya ba. Suna kuma fuskantar kalubale daga masu adawa da rigakafi a arewacin Nijeriya, wadanda a wasu lokutan kan nuna tirjiya har ta hanyar tashin hankali ga ma’aikatan lafiyar.
“An yi garkuwa da mutum fiye da 4,000 a Nijeriya a 2022 yayin da aka kashe sama da 4,500.”
Sadiq Musa, wanda ya kwashe shekara 29 yana yawon aikin kiwon lafiya, ganau ne ba jiyau ba.
Ya ce ‘’nakan hadu da su, sukan kuma zarge ni da bai wa yaransu magungunan takaita haihuwa domin su kasa haihuwa da yawa.’’
Ma’aikaciyar rigakafi Dorothy na tuna wani lokaci mai ban tsoro, lokacin da ala tilas ita da wata abokiyar aikinta suka gudu.
‘’Sai kawai suka fara magana da wani karin harshe wanda ni da abokiyar aikina ba mu fahimta ba,’’ in ji ta.
Ta kara da cewa ‘’maza ne kimanin takwas, kuma kamar suna kokarin kewaye mu. Na fada wa abokiyar aikina cewa kamata ya yi mu bar wannan wuri nan take.’’
Daga nan Dorothy da abokiyar aikinta suka arce, amma sai suka ga su ma gungun mazan na bin su da sauri.
Dorothy ta ce ‘’zuciyata na bugawa da sauri. Sun tsaya, amma suka ci gaba da kallonmu yayin da muka yi nisa, kuma muka bar kauyen.’’
Laurete Anaza, wadda ke aiki da wata kungiya mai horar da ma’aikatan sa-kai na kiwon lafiya, ta shaida wa TRT Afrika cewa irin wadannan lamura za su iya kidimar da ma’aikatan lafiya da suka shafa.
‘’Kwarai, mukan fada masu cewa idan akwai hatsari, to su gudu don tsira da ransu, musamman idan akwai hatsarin cutarwa gare su ko ga abokin aikinsu. Mun samu lamuran cin zarafin ma’aikatan lafiya.’’
John Manabeta, wani jami’in, ya kara tabbatar da wannan batu.
Ya ce ‘’mukan fada wa ma’aikatan lafiya su yi kokarin shaida gidajen da suka fuskanci matsala, kuma wasu lokutan mukan koma da ‘yan-sanda idan sun nuna wa ma’aikatan hali na tashin hankali.’’
Ko da yake yawan faruwar irin wadannan lamura na tayar da hankali, amma ba bai sanyaya gwiwar Dorothy daga ci gaba da aikinta na kiwon lafiya a cikin al’uma ba.
A cewarta, ‘’ban iya komawa wancan kauyen da suka fafare mu, ni da abokiyar aikina, ba. Sauran wurare da na tafi kuwa, na tafi ne cikin shiri, sanye da takalman gudu da gajeren wando a cikin tufafina, sannan ina ankare.’’
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, yanzu a duk shekara, rigakafi na taimakawa wajen rage yawan mace-mace kamar muliyan biyar wadanda ake samu sanadin cututtuka kamar kyanda, da mura, da makarau da dai makamantansu.
Rigakafi na taimakawa wajen rage hatsarin kamuwa da cuta ta hanyar aiki tare da garkuwar jiki don bayar da kariya.
Saboda haka, rigakafi na da matukar muhimmanci duk da irin hatsari da ma’aikatan dake aikin ke fuskanta.
A watan Maris na bara, gwamnatin jihar Adamawa ta bayar da sanarwar cewa ta cimma kashi 101 bisa dari na adadin aikin rigakafi da ake yi na yau da kullum don yaki da cututtuka kamar shan inna, baya ga fara allurar rigakafin korona.
Wannan wata alama ce ta karfin hali da kuma himmar wadanda ke aikin, abin da ma’aikacin lafiya Sadiq ya danganta da addu’o’insa.
‘’Wannan shi ya sa nake alfahari da irin aikin da nake yi’’ a cewarsa. To amma da sauran jan aiki. Dorothy ta ce ‘’har yanzu akwai al’umomi da ke lunguna wadanda ba a kai gare su ba.
"Wata kila ba yau ko gobe ba, amma dai tabbas wata rana za mu kai sakonmu na kiwon lafiya a gare su.’’