Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ta amince da sake fasalin rabon harajin kayayyaki na VAT, wanda ke janyo ce-ce ku-ce a ƙudirin sabuwar dokar harajin ƙasar da ke gaban majalisun dokokin ƙasar a yanzu haka.
Matsayar gwamnonin dai ta biyo bayan wani taro ne da ƙungiyar ta yi da kwamitin shugaban ƙasa kan sauya fasalin dokokin harajin ƙasar, wanda aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, babban birnin ƙasar.
Wata takardar bayan taro da shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya sanya wa hannu ta ce, ƙungiyar ta fahimci muhummancin zamanantar da tsarin yadda ake tattara haraji a ƙasar domin samar da ci gaba a harkar samun ƙudade.
A sanarwar da ƙungiyar gwanonin ta fitar ta bayar da shawarar yadda rabon harajin na kayayyaki wato VAT zai kasance tsakanin jihohi, wanda za a iya cewa ya saɓa da abin da ke cikin ƙudirin dokar.
Ta ce ya kamata a riƙa raba 50% tsakanin duka jihohin ƙasar daidai wa daida, sai 30% shi kuma a raba shi gwargwadon abin da kowace jiha ta kawo, sai kuma a raba 20% bisa lura da yawan jama’ar jiha.
A ƙudirin sabuwar dokar harajin da take gaban majalisa dai a yanzu haka, gwamnati na son sauya tsarin da ake amfani da shi a yanzu zuwa raba 60% gwargwardon abin da kowace jiha ta samar, sai 20% lura da yawan jama’a da kuma wani 20% ɗin da za a yi raba daidai tsakanin jihohin ƙasar 36 da babban birnin tarayya Abuja.
Haka kuma gwmanonin sun ba da shawarar cewa majalisun ƙasar su ci gaba da aiki kan ƙudirin dokar da majalisun suka jingine sakamakon taƙaddamar da ta biyo bayan tura ƙudirin majalisu, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Satumbar 2024.
Ƙungiyar ta gwamnonin Nijeriya ta kuma ba da shawarar cire sashin da ya yi magana kan wa’adin sauya fasalin yadda ake bai wa hukumomi irin su TETFUND da NITDA da NASENI kuɗaɗe daga cikin ƙudirin dokar.
Haka kuma gwamnonin na Nijeriya sun yi kira da a ci gaba da cire muhimman kayayyakin buƙatu da kayan aikin gona daga cikin kayayyakin da ake biya wa harajin VAT, don walwalar 'yan ƙasa da bunƙasa samar da kayan amfanin gona.
A ƙarshen shekarar 2024 dai gwmanoni da sarakunan arewacin ƙasar sun yi watsi da sauya fasalin rabon harajin VAT da ke cikin dokar, abin da suka ce zai mayar da su baya, sannan ya fifia wasu jihohi tsiraru.
Majalisar Datattawan ƙasar da ofishin babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a sun kafa wani kwamiti don duba ɓangarorin da ke jawo ce-ce ku-ce a cikin ƙudirin sabuwar dokar ta haraji