Majalisar Dinkin Duniya na karbar baƙuncin Babban Taronta na shekara-shekara a hedikwatarta da ke birnin New York na Amurka.
Taron wanda shi ne karo na 78 na Babban Taron MDD, an saka ranar fara shi daga 18 zuwa 22 ga watan Satumba, inda ake sa ran shugabannin ƙasashe da na gwamnatoci daga aƙalla ƙasa 145 za su halarta.
Taken taron na bana shi ne "Sake saka yarda da ƙarfafa miƙa wuya daga ƙasashen duniya: Daukar mataki da sauri kan muradun ci gaba wajen samar da zaman lafiya da ci gaba ga kowa."
Ana sa ran shugabannin Afirka za su yi magana a kan batutuwan ƙasa da ƙasa da kuma halin da ake ciki a ƙasashensu.
Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka AU, wanda kuma shi ne shugaban ƙasar Comoros Azali Assoumani na daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka biyar da ake sa ran za su gabatar da jawabai.
Ana sa ran jawabinsa, tare da na sauran shugabannin Afirka za su mayar da hankali ne a kan abin da nahiyar ke buƙata daga ƙasashen duniya.
Sauyin Yanayi
Ana sa ran shugabannin Afirka za su sake tunasar da ƙasashen Yammacin Duniya cewa nahiyar na ci gaba da fuskantar bala'in sauyin yanayi duk da rage amfani da iska mai gurbata muhalli da suka yi, idan aka kwatanta su da wasu ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki.
Mai yiwuwa shugabannin su buga misali da abubuwan da suka faru kwanan nan a Libiya, inda mahaukaciyar guguwa mai suna Daniel ta afka wa yankin tare da jawo ambaliyar ruwan da ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 11,000.
Ana sa ran shugabannin ƙasashen Afirka za su yi kira ga ƙasashen duniya da su yi duba kan jajircewarsu ta baya su samar da dala biliyan 100 duk shekara a hidimar sauyin yanayi, da kawar da gurɓataccen fetur da kuma samar da wata cibiya da za ta dinga aikin gyara ɓarnar.
Waɗannan ƙudurori su ne kuma za a kambama su a wajen Babban Taron Sauyin Yanayi da za a gudanar ranar 20 ga watan Satumba a jerin tarukan da za a yi a Babban Taron MDD.
Samar da yanayi na adalci
Wani batun da mai yiwuwa za a sake yin duba a kansa shi ne na buƙatar samar da wani yanayi na adalci a gaban ƙasashen duniya, musamman kan batun cibiyoyin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da ita kanta MDD.
Afirka ta shafe shekaru tana neman samun kujera a Kwamitin Tsaro na MDD inda a baya-bayan nan kiran ke ƙara yawa. Wataƙila shugabannin Afirka su ƙara jaddada kiran a jawabansu.
Sannan wataƙila a tattauna batun tsarin hada-hadar kuɗi na duniya ma, saboda yadda ƙasashen Afirka ke yawan cewa ba a yi musu adalci shi yasa ma suke samun kansu a "tarkon dabaibayin bashi."
Samar da abinci
Ga alama kuma za a sake bijiro da batun yaƙin Rasha da Ukraine, inda shugabanni za su jaddada tasirin da yake yi a kan samar da abinci a nahiyar tasu.
Ana sa ran shugabannin za su yi kira kan samar da mafita ta zaman lafiya tare da roƙon Rasha ta sake shiga yarjejeniyar fitar da hatsi ta Bahar Aswad, wacce Turkiyya ta samar a watan Yulin 2022 tare da goyon bayan MDD.
Yarjejeniyar ta taimaka wajen fitar da fiye da tan miliyan 32 na kayan amfanin gonar Ukraine ta Bahar Aswad, inda aka kai kusan tan miliyan 19 zuwa ƙasashe masu tasowa a Afirka.
Jerin juyin mulki
Ana sa ran a jawabinsa, Shugaban Nijeriya kuma Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Bola Tinubu, zai taɓo batun juyin mulkin da ake samu a yankin da kuma ƙoƙarin kare dimokuraɗiyya.
Zuwa yanzu an samu juyin mulki a ƙasashe biyar a yankin da suka haɗa da: Burkina Faso (Janairu 2022) Guinea (Satumba 2021) Chadi (Afrilu 2021) Mali (Agusta 2020) da kuma Sudan (Oktoba 2021).
A lamarin Nijar kuwa, da fari ECOWAS ta yi barazanar amfani da ƙarfin soji don mayar da Shugaba Mohamed Bazoum, amma daga baya ta zaɓi tattaunawa don warware lamarin.
Tashin hankali ya ƙaru a yayin da Mali da Nijar da Burkina Faso, ƙasashe uku na yankin Sahel a Yammacin Afirka da sojoji ne mulkinsu suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsaro bisa alkawarin taimakon juna idan har aka tura musu sojoji ko aka yi musu "kutse."
Yadda tsarin taron yake
Kowane shugaban ƙasa zai yi jawabi na minti 5 zuwa 15, inda za su bijiro da matsalolin da ke damunsu, ciki har da batun kawo ƙarshen yunwa da talauci, da inganta samar da kuɗaɗen shiga da ilimi a faɗin duniya, tare da samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli.
A yayin taron, kowane shugaban ƙasa ko wakilansu, za su gabatar da jawabi. Za su yi amfani da ɗaya daga cikin yarukan Majalisar Dinkin Duniyar shida: Larabci ko Chanisanci ko Turanci ko Faransanci ko Rashanci ko kuma Sifaniyanci.
A kan cewa masu magana su yi ƙoƙarin taƙaita bayanansu a ƙasa da minti 15, duk da cewa dai a kan yi biris da hakan.
Shugaban ƙasar Cuba Fidel Castro shi ne wanda ya taɓa yin jawabi mafi tsaro ga Babban Taron MDD a tarihi, inda a shekarar 1960 ya shafe awa hudu da rabi yana magana.
Sauran muhimman masu jawabi a taron
Ana sa ran shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai halarta, kuma zai yi jawabi ga Kwamitin Tsaro na MDD a kan yaƙin da ake yi a ƙasarsa.
Sai dai, Shugaban Rasha Vladimir Putin da na China Xi Jinping da kuma na Faransa Emmanuel Macron sun nuna alamar ba za su halarta ba.
An fi cimma sakamako mafi muhimmanci a taron UNGA ne daga ƙananan tarukan da akan yi tsakanin shugabannin ƙasashe.