Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta yaye tubabbun 'yan daba 50 wadanda suka samu mukamin kwansitabul na ‘yan sanda.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda reshen Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Litinin, ya ce mutanen na cikin ‘yan daba 222 da suka yi saranda ga ‘yan sanda tare da daukar alkawarin ba za su sake aikata laifi ba.
“Yau rana ce ta farin ciki ga jama’ar Kano da ‘yan sandan Kano saboda mun yaye matasa 50 daga cikin 222 wadanda suka tuba daga daba wadanda tuni suka yi alkawarin ba za su sake yin daba ko wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a jihar ba,” in ji Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Mohammed Usaini Gumel a lokacin yaye daliban.
Labari mai alaka: Rundunar 'yan sandan Kano ta fitar da sunayen manyan 'yan "daba" da take nema
An dauki mutum goma daga kananan hukumomin Dala da Fagge da Ungogo da Municipal da kuma Gwale har suka zama mutum 50.
Hukumomin sun bayyana cewa sabbin ma’aikatan sun samu horo na watanni biyu kafin suka samun mukamin kwansitabul din.
Ana yawan taimaka wa tubabbun masu aikata laifuka a Nijeriya inda sau da dama gwamnati ke koya musu sana’o’i domin dogaro da kai ko kuma daukarsu ayyuka.