Tsohon kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Ghali Umar Na'Abba, ya rasu.
Ya rasu ne ranar Laraba da asuba a wani asibitin birnin Abuja bayan ya yi jinya, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Sun kara da cewa nan gaba kadan za a tafi da shi birnin Kano domin yin jana'izarsa.
An haifi marigayin a birnin Kano da ke Nijeriya a shekarar 1958.
Ghali Na'Abba ya rike mukamin kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2003.
A lokacin da ya jagoranci Majalisar, Ghali ya yi fafutuka wajen ganin ta samu 'yanci daga bangaren zartarwa tare da tabbatar da mutunta raba iko tsakanin bangarorin biyu.
Hakan ya sa an yi ta samun takun-saka tsakaninsa da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo.
Ghali ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya samu shaidar karatun Digiri a fannin Kimiyyar Siyasa a shekarar 1979.