A ranar Alhamis din nan ne wasu gwamnonin Arewacin Nijeriya suke kammala wani taro a Amurka kan zaman lafiya da matsalar tsaro a jihohin da kuma yadda za a shawo kansu.
Gwamnoni sun hada da gaba daya jihohin arewa maso yamma, wato Kano da Kaduna da Sokoto da Katsina da Jigawa da Zamfara da kuma Kebbi.
Sai gwamnoni uku na jihohin arewa ta tsakiya da suka hada da Neja da Nasarawa da Filato.
Sashen Afrika na Cibiyar da ke Bincike Kan Zaman Lafiya ta Amurka, wato African Centre of the United States Institute of Peace da ke birnin Washington ne ya shirya taron.
Cibiyar ta ce, taron na gwamnoni 10 ci gaba da tattaunawa ce da aka yi a Amurka da wasu gwamnonin jihohi Nijeriya kan batun tsaro da zaman lafiya wanda aka fara tun shekarar 2014 da kuma 2016.
Ta ce a taron na wannan makon an mayar da hankali kan abin da ‘yan kasa da shugabanni za su yi don rage tashin hankali da kuma yadda za a samar da ci gaba a jihohin.
Jihohin arewacin Nijeriya dai su ne suka fi fama da matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga da masu sace mutane domin neman kudin fansa, suka addabi yankin, tare da kashe dubban mutane.
Daya daga cikin gwamnonin da suke halartar taron, gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya bayyana wa TRT Afirka Hausa cewa duka gwamnoni goman da suke halartar taron sun yi bayani kan abubuwan da suke faruwa a johohinsu.
Ya ce baya ga gwamnonin akwai kuma masana da suka gabatar da bayanai inda suka duba matsalolin da ake fuskanta.
“Sannan a matsayinsu na masana sun ba mu shawararwari na yadda za a kai domin a ga cikin yardar Ubangiji an kawo karshen wannan matsala ta tsaro a wadannan jihohi namu,” in ji Gwamna Namadi.
Ya kara da cewa daga bayanan da masanan suka yi musu gwamnonin sun ƙaru sosai kan irin matakan da ya kamata su ƙara dauka don samar da tsaro a jihohin nasu.
Gwamnan ya ƙara da cewa “Ba wai don ba mu sani ba ne. Ka san dai da yake suna harka da duniya baki daya, suna da masaniya akan abin da ya faru a wata kasa – duk da cewa ba zai zama daya da abin da yake faruwa a kasarmu ba – amma dai wannan masaniya da suke da ita idan aka gano abin da aka yi a can da abin da aka yi a can, aka hada da abin da muke da shi, sai ka ga an samu mafita.”
“Wadannan abubuwan da ake tattaunawa gaskiya suna da amfani, kuma muna ganin cikin yaradar Ubangiji za su taimaka wajen kawo karshen wannan matsala da ake fama da ita.”
Jihar Katsina na daga jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro inda a yanzu haka ‘yan bindiga suka mamaye garuruwa da dama, sannan wasu garuruwan kuma suka zama fanko saboda yawan harin da ake kai musu.
Kwamishinan tsaro na jihar ta Katsina Alhaji Nasir Ma’azu na cikin wadanda suka je taron tare da gwamnan jiharsa, ya ce sun ƙaru sosai da irin misalai da dabaru da aka fada musu, wadanda wasu kasashe suka yi amfani da su, kamar Pakistan da Rwanda.
Gwamnonin na arewacin Nijeriya da suka halarci taron na Amurka su ne Dikko Umar Radda na jihar Katsina, da Dauda Lawal na jihar Zamfara da Uba Sani na jihar Kaduna da Mohammed Umar Bago na jihar Neja, da kuma Nasir Idris na jihar Kebbi.
Sauran su ne Malam Umar Namadi na Jigawa, da Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, da Caleb Mutfwang na jihar Filato, sai Hyacinth Iormem Aliana jihar Benue da kuma Mohammed Idris Gobir, mataimakin gwamnan jihar Sokoto.