Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta dakatar da ba da biza ga jami'an gwamnati da ke neman damar zuwa birnin New York na Amurka don halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya UNGA na bana.
A sanarwar da kakakin shugaban kasar Ajuri Ngelale ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya ce an dauki matakin ne don rage kudaden da gwamnati take kashewa a kan tafiye-tafiyen jami'anta.
Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunan duk wani jami'i da zai je taron ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.
Labari mai alaka: Shugaba Tinubu zai gana da Joe Biden a Amurka
"Don takaita duk wani tsaiko da ka iya biyo bayan wannan umarni, Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya da ke aikin ba da biza tare da babban ofishin da ke birnin New York, za su yi aiki tare wajen tabbatar da an bi matakan da suka dace wajen tantance wadanda za su je taron a hukumance," in ji sanarwar.
Bisa ga wannan umarni na shugaban, an bukaci duk wata ma’aikata ta tarayya da hukumomi su tabbatar da cewa sun takaita yawan jami’ansu da suka saka a cikin tawagar da za ta halarci taron na UNGA.
Kazalika Shugaba Tinubu ya bayyana cewa daga yanzu dole jami'an gwamnati su dinga taka-tsantsan wajen tafiyar da kudaden al’umma da ake kashewa.