Darakta Wray ya ce ya kai ziyara Nijeriya ne domin ƙarfafa "dangantakar" da ke tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka./Hoto:Fadar Shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) Christopher Asher Wray a Abuja ranar Juma'a don haɗa gwiwa kan yaƙi da ta'addanci da laifukan da ake aikatawa a intanet.

Wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Tinubu ya fitar jim kaɗan bayan ganawar ta ambato shugaban na Nijeriya yana cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali kan samar da ilimi ga 'yan ƙasar a matsayin wata hanya ta magance talauci wanda aka yi amannar cewa shi ne babban abin da ke haddasa laifuka.

''Muna aiki tuƙuru domin kawar da ta'addanci da laifukan da ake aikatawa a intanet da masu ƙulla soyayyar bogi ta intanet, sannan ina farin-cikin ganin hukumomi da dama sun taimaka wajen rage aikata waɗannan laifuka, kuma akwai wakilansu a wannan taron,'' in ji shi.

Shugaba Tinubu ya yi kira a ƙarfafa dangantaka tsakanin hukumomin tsaron Nijeriya da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) wajen yaƙi da laifukan intanet da ta'addanci da sauran laifuka masu alaƙa da su.

''Abin alfahari ne a gare ni da na karɓi baƙuncin Darakta Christopher Wray, shugaban hukumar da ta nuna ƙwarewar aiki a shekaru da dama. Ziyarar da ka kawo ta nuna muhimmancin Nijeriya da kuma haɗin-gwiwar Nijeriya da hukumomin tsaron Amurka. A gare mu, hakan wata yarda ce gamae da matakin da muke da kuma matsayin ƙasashenmu na musayar bayanai kan kawar da laifuka a gida da ƙasashen duniya," a cewar shugaban Nijeriya.

Ya ƙara da cewa,"Ba za mu iya samun wannan nasara ta kawar da laifuka ba ba tare da wannan haɗin-gwiwa ba. Abin arashi shi ne, a matsayinta ta shugabar ECOWAS, Nijeriya tana haɗa kai da sauran ƙasashen Yammacin Afirka domin yaƙi da laifukan tattalin arziki da sauran laifuka."

A nasa jawabin, Mr Wray ya ce ya kai ziyara Nijeriya ne domin ƙarfafa "dangantakar" da ke tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka.

Ya yaba wa Shugaba Tinubu game da goyon bayan da yake bayarwa wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron ƙasar da kuma hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) wajen kare 'yan ƙasashen biyu.

TRT Afrika