Ofishin DMO da ke kula basussukan Nijeriya ya ce gwamantin Shugaba Bola Tinubu ta gaji basussukan da suka kai naira tiriliyan 87.38 a lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban ƙasa.
Ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023 ne dai Shugaba Tinubu ya kama aiki.
Ofishin na DMO ya bayyana haka ne domin ƙarin haske game da wasu rahotanni da ke iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya gaji bashin naira tiriliyan 21 kuma basussukan sun kai na naira tiriliyan 142 a yanzu.
A wata sanarwar da ya fitar ranar Litinin, ofishin ya ce jimullar basussukan da ake bin Nijeriya zuwa ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2023 bayan shugaba Tinubu ya karɓi ragamar mulki naira tiriliyan 87.38 ne.
Ofishin ya ce, basussukan sun haɗa da na cikin gida da na ƙetare tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi 36 da kuma Birnin Tarayya Abuja.
“A gaskiya iya basussukan da ake bin Nijeriya a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2023, wadda ita ce ranar ta farko da aka wallafa iya basussukan da ake bin ƙasar bayan Tinubu ya hau karagar mulki (ranar 29 ga watan Mayu, ta shekarar 2023); naira tiriliyan N87.38 ne, ba naira tiriliyan 21 da kafafen watsa labarai suka ruwaito ba. Kuma ya kama a gane cewa jimullar basussukan da ake bin ƙasar da DMO ta wallafa sun haɗa da basussukan cikin gida da na ƙetare na gwamnatin Tarayya da na jihohi 36 da kuma Birnin Taryya Abuja,” in ji sanarwar.
Ofishin ya jaddada muhimmancin dogaro da tabbatattun alƙalumma daga bayanai na hukumomin gwamnati domin kauce wa watsa labaran ƙarya, musamman game da muhimman batutuwa kamar basussukan gwamnati.
“Ofishin kula da basussuka na DMO na son sanar da mutane cewa labarin da ke yawo mai taken, ‘yadda basussukan Nijeriya suka ƙaru daga naira tiriliyan 21 zuwa tiriliyan 142 a ƙarƙashin Tinubu’ ba gaskiya ba ne”, in ji sanarwar.