Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen da ake gabatarwa karkashin Hukumar Kula da Shirin Tallafa wa Marasa Galihu ta Kasa (NSIPA), in ji Gwamnatin Tarayyar kasar.
Da yake sanar da dakatar da shirye-shiryen a ranar Juma'ar nan, Daraktan Watsa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya ce matakin na shugaban "na daga ayyukan bincike kan zargin almundahana wajen kula da hukumar."
Sanarwar ta ce "An dakatar da dukkan shirye-shirye hudu da Hukumar ke gabatarwa na N-Power, Shirin Aika Kudade Kai-Tsaye, Shirin Karfafawa Mutane da Koya Sana'o'i na Gwamnati da Ciyar da Daliban Makarantu na tsawon makonni shida a karon farko."
"Shugaba Tinubu ya kuma bayyana matukar damuwa game da ayyukan rashin dacewa da cuwa-cuwa a biyan kudade a karkashin shirye-shiryen."
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Shugaba Tinubu ya kuma kafa kwamitin ministoci da zai yi zuzzurfan nazari kan ayyukan hukumar, tare da bayar da shawarwarin kawo gyara a NSIPA.
A tsawon lokacin dakatar da shirin, duk wasu ayyuka da suka shafi Hukumar NSIPA sun tsaya cak, in ban da raba kayayyaki, gudanar da shirye-shirye, hadin gwiwa da yin rajista.
Tinubu ya kuma tabbatarwa da 'yan Nijeriya cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen tabbatar da aiki da tsari na adalci, kuma daga yanzu za a tabbatar da an aiwatar da shirin tallafa wa jama'a ta yadda ya kamata, za a taimaka wa 'yan Nijeriya mabukata.
Dakatar da shugabar NSIPA
Bayan damuwa kan yadda ake mu'amala da kudade a hukumar, Shugaba Tinubu a ranar 2 ga Janairu ya dakatar da shugabar Hukumar Kula da Shirin Tallafa wa Marasa Galihu ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu.
Kafin nada Halima a wannan matsayi, ta yi aiki a matsayin Jagorar Shirin Tura Kudade Kai-Tsaye, kuma a baya ma ta yi aiki da Ma'aikatar Harkokin Jinkai, Yaki da Annoba da Ci-gaban Zamantakewa ta Tarayya.
Bayan dakatar da Halima, an nada Babban Jami'in Shirin N-Power Dr Akindele Egbuwalo a matsayin shugaban riko har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Dakatarwar tata ta zo watanni uku bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da ita a matsayin shugabar Hukumar NSIPA.