Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa sababbin ministocin da ya nada ma'aikataun da kowannensu zai yi aiki a can.
Mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar shugaban kasa a ranar Laraba.
An bai wa tsohon gwamnan Jigawa Badaru Abubakar Ma'aikatar Tsaro, sai tsohon gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro.
Sannan tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike shi aka bai wa Ma'aikatar Birnin Tarayya, Abuja.
Ga jerin kamar haka:
- Babban Ministan Tsaro – Muhammad Badaru
- Karamin Ministan Tsaro – Bello Matawalle
- Karamin Ministan Gidaje da Bunkasar Birane – Abdullahi Gwarzo
- Ministan Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki– Atiku Bagudu
- Ministan Birnin Tarayya – Nyesom Wike
- Karamar Ministar Birnin Tarayya – Mairiga Mahmud
- Ministar Al’adu da Bunkasa Tattalin Arziki – Hannatu Musawa
- Karamin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli – Bello Goronyo
- Ministan Gona da Samar da Abinci – Abubakar Kyari
- Ministan Ilimi – Tahir Mamman
- Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’idu Alkali
- Ministan Harkokin Waje – Yusuf Tuggar
- Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a –Ali Pate
- Ministan Harkokin 'Yan Sanda – Ibrahim Gaidam
- Karamin Minsitan Tama da Karafa – U Maigari Ahmadu
- Ministan Sadarwa da Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Intanet - Bosun Tijani Ministan Muhalli - Ishak Salako
- Ministan Kudi - Wale Edun
- Ministan Harkokin Teku - Bunmi Tunji
- Ministan Lantarki - Adedayo Adelabu Karamin
- Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a - Tunji Alausa
- Ministan Ma’adanai - Dele Alake
- Ministan Harkokin Yawon Bude Ido - Lola Ade-John
- Ministan Sufuri - Adegboyega Oyetola
- Ministan Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari - Doris Anite
- Ministan Kimiyya da Fasaha - Uche Nnaji
- Karamin Ministan Kwadago da Ayyuka - Nkiruka Onyejeocha
- Ministan Harkokin Mata - Uju Kennedy
- Ministan Ayyuka - David Umahi
- Ministan Matasa - Abubakar Momoh
- Ministan Ayyukan Jin kai da Rage Talauci - Betta Edu
- Karamin Ministan Iskar Gas - Ekperikpe Ekpo
- Ministan Man Fetur - Heineken Lokpobiri
- Ministan Wasanni - John Enoh
- Karamin Ministan Ilimi - Yusuf T. Sunumu
TRT Afrika