Sama da wata bakwai kenan bayan ’yan Nijeriya sun zabi sabon Shugaban Kasar na 16, amma har yanzu ana ci gaba da kalubalantar nasarar zaben.
Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu, sannan aka rantsar da shi daga baya domin fara aiki.
Babban abokin hamayyarsa, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, ya daukaka kara zuwa Kotun Koli domin ci gaba da kalubalantar nasarar ta Bola Tinubu bayan Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya ci zaben a watan jiya.
Alhaji Atiku Abubakar ya tattara hujjoji 35 da yake so ya gabatar a gaban kotun domin kalubalantar zaben, amma babban makaminsa shi ne zargin cewa Shugaban Kasar ya yi amfani da takardar digiri ta bogi daga Jami’ar Jihar Chicago, da ya ce ya kammala a shekarar 1979, wanda hakan ya haifar da muhawara mai zafi a fagen siyasar kasar.
Takardun karatu
Shugaba Tinubu ya gabatar da shaidar kammala digiri a cikin takardun da ya mika wa Hukumar INEC domin shiga takarar Shugaban Kasa.
Kafafen yada labarai na cikin Nijeriya sun bayyana cewa an ba Atiku takardun kammala karatun na Tinubu ne bayan ya kai korafi Kotun Yankin Arewa ta Illinois da ke Amurka yana bukatar kotun ta tilasta wa Jami’ar Jihar Chicago ta bayyana duk wasu bayanan karatun na Tinubu, wanda ita kuma kotun ta amince.
Masana harkokin siyasa da shari’a sun bayyana ra’ayoyi mabambanta a kan takardun da aka sako, inda wasu suke bayyana cewa an yi jinkirin tayar da maganar.
“Ana bata lokaci ne kawai wajen kokarin tono takardun karatun Shugaban Kasar,” kamar yadda Kunle Adegoke (SAN) ya bayyana wa TRT Afrika.
Korafi mara isasshen bayani
“Ya kamata ne a ce an gabatar da wadannan hujjojin kafin zabe, ko kuma akalla ma a ce kafin a je Kotun Sauraron Kararrakin Zabe. Dama sun gabatar da hujjojin ne kafin a yanke hukunci (na Kutun Sauraron Kararrakin Zabe),” in ji shi.
“Shugaban Kasar yana da damar bayyana cewa lallai ya yi karatu a jami’ar, kuma lallai takardun karatun nasa ne,” in ji Emeka Monye, wanda masanin harkokin siyasa ne a Nijeriya.
Ana ta yada wasu takardun kammala karatu a kafafen sadarwa da ake cewa na Tinubun ne, wanda hakan ya sa wani Minista a Nijeriya ya mayar da martani.
A cewar ministan, “Lallai wannan kayin da Atiku Abubakar ya sha ya fi masa zafi, sama zafin da ya ji idan aka hada dukkan faduwa zaben da ya yi a baya… Ya kamata ya karbi kaddara kawai ya tara gaba,” kamar yadda Festus Keyamo ya rubuta a shafinsa na X, wadda ake kira Twitter a baya.
Ba a gama wasan ba
Amma wasu na ganin cewa lallai akwai sauran rina a kaba a game da lamarin.
“Idan har da gaske ne takardun karatun nan suna nan da gaske, me ya sa lauyoyin Shugaban Kasar suka yi ta kokarin ganin ba a sako su ba?” in ji wani masanin harkokin siyasa, David Okenwa.
“Za a ga kamar an gama wasan ne, amma Atiku tsohon dan siyasa ne, kuma ba zai rasa wani shirin ba. Sakaci ne a yi tunanin an cinye shi a wasan tun yanzu,” in ji Monye.
Shugaban Kasa Tinubu bai ce komai ba a game da lamarin - kwanan nan ya gama da wata matsalar inda ya samu nasarar hana Kungiyar Kwadago tafiya yajin aikin da suka yi shirin farawa a ranar 3 ga Oktoba.
Shi ma Atiku bai fito fili ya ce komai ba a game da lamarin, inda masana suke cewa akwai yiwuwar yana nan yana tattaunawa da lauyoyinsa ne a kan matakin da za su dauka na gaba.